A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Motar data kawo kayan ne tai reverse tafice daga dakin, fitowa Aliyu yayi daga flat dinshi sanye dawasu kayan exercise na kampanin ceegar, purple rigane armless hoodie sai wani gajeren wando daya tsayamai a guiwa, yasaka sport shoes na Nike yafito yanadan kakkabe hannu yana kallon inda Aneesan take datai kaman bashi take kallo ba tana sharanta abinta nanko idanunta nakanshi, kallonshi instructor yayi yace “are we ready Leo?” gyadamai kai yayi with full confidence shi adole soyake ya burge Aneesa yau, wani adjustable dumbbell instructor nashi yadauka kaman yadau tsinke abinka da wanda aikinshi kenan yace “are you ready Leo, squat, spread your legs and give me your hands” squatting Aliyu yayi ya bubbude kafa kaman yanda instructor yayi agabanshi yamikamai hannu, ahankali instructor yasakama Aliyu dumbbell din ta hanyar dauramai a hannu yace “let’s go, lift it up in the count of 3, one, two, three” wani irin ihu Aliyu yayi Instructor na zare hannunshi daga kan dumbell with yasakan mai nauyin duka, ko lifting dumbbell din up baiyiba yahau sakin ihu “auuchhh Daddddd, ahhhh hannuna, auuchhh” da sauri Aneesa tadago kai rike karfen barandan su tayi kaman zatai kuka tana kallon Aliyun dataga yay wani iri da hannu kaman hannunshi na shirin ballewa yana kiran Dady, the thing looks funny amma tausayi yabata dan tasan ita tasashi da yanzu yana zaman zaman shi, dariya instructor yayi yana gyara position din dumbbell din a hannunshi yace “oh common u can do it, is just 80kg dumbell fa, saika saba da wanan zan kaga 100kg dumbell, lets go, let go lift it up” kaman Aliyu zai sakin mai kuka ya girgiza kai a shagwabe yace “ni bazan yiba kacire mini kona kirama Abba na wlh” kyalkyacewa da dariya Aneesa tayi at this point the whole Aliyu thing looks funny wlh, bata taba ganin lazy namiji irin Aliyu ba ita yama akai takeson wanan mutum haka Allah na tuba ai koni zan iya dagawa sama, akwai shi a shagon madam ta backyard tafa taba dagawa fa kuma bawani nauyi koda yake dadai nauyi but ba sosai ba, kyalkyacewa da dariya tayi hartana buga kanta da brander abin yay kara da sauri Aliyu yajuyo ganin Aneesa ce ke dariya sosai tana kallonshi yasa ya kauda kai, kafin yakara waigowa da sauri hada ido sukayi ta daure fuska kaman ba ita ke dariya ba tamai alamu da hannu idan bakayi ba forget bazan aureka ba dinan, wani irin namijin ihu Aliyu yayi yay lifting karfen sama gabaki daya yana huci da baki kaman macen dake nakuda, yanda taga hannunshi na rawa kaman yana shirin sakinshi kasa jijiyoyin wuyan shi dana kanshi duk sun bullo tsabagen nauyin abinda yadaga kana ganinshi kasan yanacin wuya, tausayi taji yabata sosai daukan tsintsiyan tayi tabude dakinsu ahankali ta shiga dan bazata iya jure taganshi yana aikin wahala ba kuma ita tasashi.
Daddy ne kadai zaune afalo yana kallon news ganinta yasa yace “ki shirya, anjima idan Yayanki yagama tarkacen training dinchan zansa yakaiki saikiyi registration din jamb ko, mamanki tacemin baki riga kinyi ba” murmushi tayi tace “to Abba” tawuce kitchen ta ijiye tsintsiyan sanan ta wanke hannu tazo tana taya Ammi aiki sinasir Ammi keyi da safen nan daga taji Dady yace yanajin cin sinasir shine tafara yi bamata fadamai shizatayi ba, sai around 10 suka gama tsaf Aneesa ta dinga fito da warmers din tana jerasu a dinning, waya Dady yadauka yakira Aliyu. “leave that training kazo kai breakfast” katse wayan Dady yayi saida Aneesa tagama ajiye komi a dinning harda cucumber zobo juice din da Ammi tayi sanan tawuce sama danta watsa ruwa, dakinta ta shiga bayi direct tawuce wanka tayi sanan tafito wata hadadiyar pink atampan da Dady ya saimata ta dauko tasaka an mata dinkin Riga da skirt daya kamata ya bala’in mata kyau, mai kawai ta shafa ko hoda bata tsaya shafawaba sabida kwala mata kira dataji Ammi tayi tace “ganinan zuwa Ammi” wani karamin hijabinta na zaman gida tadauko baki daya tsayamata acinya tasaka, sanan tafito ta maida kofan tarufe, tundaga saman takejin kamshin turaren Aliyu alamun ya shigo kenan ahankali take tafiya kanta akasa harta fito falon baki Ammi tabude zatamata masifa dan tuntuni ita suke jira basu faracin abincin ba gashi Dady zai fita Dady yadaga mata hannu yace “kinga bance kima y’ata fadaba bakiga wanka tayiba, zauna abinki muci abinci” Dady yay maganan yana nuna mata kujeran dake gefen na Aliyu, ahankali taja kujeran ta zauna, Ammi tadau plate mai kyau ta zubama Dady sinasir da miyan, tadau wani bowl tazubamai farfesun kayan ciki sanan ta kalli Aliyu tace “mezakaci son?” ahankali yace “coffee Mum” dan hararanshi Ammi tayi tace “nasan zakasha coffee namaka shi daman, but zakaci abincin dazai kama maka ciki” mug ta dauka ta tsiyayamai coffee sanan tamika mai zuma tace “gashi kasa daidai” da sauri Aneesa ta fizge zuman kafin ya amsa tace “Ammi cikawa zaiyi wlh ya iyacin zaki” wani irin kallo Ammi tabita dashi surprisingly, Aliyun ma dago kai yayi ya kalleta for the first time tunda ta shigo dakin, Ammi zatai magana Dady yace “ya akayi kikasan Aliyu dason zaki daughter? Aiko hakane, samishi kadan kinji” dan murmushi Aneesa tayi akunyace sabida kallon da Ammi keta binta dashi tasan sai tace nata Yaya2 akayi tasan Aliyu nason zaki, adan kunyace tadago kanta hada ido sukayi da Aliyun dake kallonta dauke kai tayi tamika mai zuman tace “gashi kasa” da sauri Dady yace “samai daughter na kinji” ahankali tasaci kallon Ammi ganin takoma gefen Dady tai zamanta abinta kaman ma bata ganinta yasa tajawo coffee Aliyu dake binta da kallo ta zubamai zuman daidai sanan ta juyamai ta turamai gabanshi tadan saci kallonshi tareda sakinmai harara, murmushi yayi yadau mug din yakai baki, Ammi tace “samai sinasir kema kisaka” zubama Aliyun tayi dayawa ta ajiyemai agabanshi sanan itama tazuba nata tadawo ta zauna, ahankali takecin abinci duk wani motsi dazatayi akan idanun Aliyu hakan yasama takasa cin abincin da kyau gashi yay shegen dadi girkin.
Saida Dady yagama sanan ya kalli Aliyu yace “Son take Aneesa to inda zatai jamb registration okay, nizan fita saina dawo” dan dukowa yayi ko damuwa baiyi ba ya sumbaci goshin Mami rufe fuska da hijabi Aneesa tayi akunyace Aliyu yay murmushi aranshi yace “I will do more to you yarinya”.
Shafa kan Aliyu Dady yayi sanan ya shafa kan Aneesa yace “saina dawo yarana” ahankali Aliyu yace “bye Dad” “saika dawo Abba” Aneesah tafada ahankali tanacin abinci fita Dady yayi yarufo musu kofan duk suka gama cin abincin Aliyu ne yafara ture abincin kadan yarage dan girkin yamai dadi sosai Ammi ne tace “badai harka cinye ba” murmushi yayi yace “nakoshi Mum, bari naje nai wanka” ya kalli Aneesa yace “get ready” da sauri Ammi tace “wlh kaman kasani dan wanan wasanta yay yawa Aliyu” daure fuska Aneesa tayi tareda turo baki Aliyu yay murmushi yawuce yafita, saida Ammi taga yarufo kofa sanan ta kalli Aneesan tace “ya akayi kikasan yanason zuma harda fizgewa?” sosai gabanta yafadi kasa magana tayi, wani irin kallon da Ammi tamata yasa batasan lokacin datace ai uhn jiyane da ina assignment anan falo ya shigo yace namai coffee idanunshi sunyi ja sun kumbura shine namai naga yanata tula uban zuma ciki fa” wani irin kallo Ammi tamata saikuma bata karacewa komiba tace “tashi ki kwashe kayan nan kikai kitchen kibar wanke wanken kije ki sako proper hijabi kizo kutafi wajen jamb registration din” tashi tayi ta shiga hade plates din takai kitchen sanan tadawo takarasa kwashe sauran tawuce sama, wani baby pink hijabi tajawo har kasa tasaka sanan tazauna bakin gado tasa safa tadau Jakarta tasa wayanta da kudin datake dashi dubu ta jefa ajakan tadau jakan ta rataya she looks damn cute dudda babu kwalliya akan fuskanta banda mai kadai data shafa, fitowa tayi tawuce dakin Ammi a kwance taga Ammi da alamun kaman bacci takeso tayi ganin Aneesa yasa ta tashi zaune tace “harkin shirya?” “hijabi kawai nasa da safa” gyadamata kai Ammi tayi tajawo Jakarta yan dubu daidai tajawo tabata guda uku tace “gashinan kirike incase, ki kama kanki banda rawan kai, inkin dawo kitunamin yau zamu kira su Baffan ki kinji” murmushi tayi tace “to Ammi na, Ammi yaushe zanje hutu gidansu Ihsan din Momma” idanu Ammi ta ware tace “tooo su Anty Aneesa manya, yaushe kika fara islamiyyan da zaki fara fashi? Keda kije koda nan da chan ne sai kunyi hutun islamiyya da hadda, so nake ki natsu ki haddace Al Qur’ani kinji Aneesa kafin tsayayyen miji yafito” akunyace tarufe fuska murmushi Ammi tayi tace “kunyan gulma tashi kije Aliyu na jiranki awaje saikin dawo” gyadama Ammi kai tayi tatura kudin ajaka tawuce tafita.
Ahankali tabude kofar flat dinsu daidai lokacin Aliyu yabude kofar flat dinshi yana sanye dawani dark blue fitted jumper data mugun haska farin fatanshi, hannunshi rikeda wayanshi kiran iPhone 11 sai key motar shi, kallon juna sukayi na almost a minute kafin Aneesa tafara dauke kai, wani sabon loafers dinta dake kan shoe rag din bakin kofansu ne tadauka tazauna ahankali kan dakalin tasaka takalman dasuka ma dan karamin kafarta kyau, mikewa tayi tafara tafiya anatse tana saukowa Aliyu daya tsaya agaban motan yabude bangaren dazata shiga ya tsaya yana jiran takaraso, hardewa kafafun ta suka shiga yi tsabagen yanda yake kallonta, karasowa tayi har inda yake atsaye dagokai tayi ta kalleshi tareda turomai baki tace “nikadena kallona saikasa ka nafadi” tai maganan tana shiga motan ta zauna akan kujera, ahankali yasa hannunshi ya tattare hijabin nata yace “ke kadai idanuna suke gani, haka kuma kece abincin su, barka da zuwa gimbiyar zuciyata, the only woman that owns Ali Gadanga Gusar Yaki, I can’t wait to make this yummy yummy barkono girl mine” da sauri tadago kai ta kallai zatai magana kuma saita dauke kai sabida yanda yacika mata ido, dan murmushi yayi yazagayo yanadan yatsine fuska sabida yanda hannunshi kemai ciwo sosai, shiga motan yayi ya kunna duk yana murmushi, ahankali batare daya kalleta ba yace “kin tuna ranan dakika fara shiga motan nan kina kuka wiwi kaman ba Aneesa barkono ba” da sauri tadago kai ta kallai jan motan yayi yafita daga Gate din gidansu da aka bude, ahankali tace “waye barkono?” kyalkyacewa da dariya yayi ya kalli fuskanta gani yayi tadaure fuska, ahankali yace “you are my barkono, tunda kikama motana wankan kasa nace toooo fah” murmushi tayi ta dauke kai tana kallon hanya, bata kara cemai komiba harsuka kai wajen wani babban cafe ne acikin baze University, parking yayi yaciro wayanshi yakira wani number ba’a dadeba saiga wani mata shi yafito yazo har wajen motan Aliyu.