A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa, pay aduniya or pay alahira????????‍♀️ duk wacce ta watsamin book waje batare da izinina ba ban yafemiki ba har abada.

Yakai almost 30min yana kuka, ya tsani raini, ya tsani zagi, and abinda Aneesa tamai yau is a total raina, Banza kawai, you are very very stupid, zan tsinka maka mari, zan mugun tsinka maka mari stupid boy duk shi kadai tama uban zagin nan, jin kanshi na neman fita yasa yatashi da kyar ya lallaba yadau paracetamol dake kan side drawer shi ya balla ya jefa abaki sanin babu kyau shan kagani babu komi acikinshi yasa yamika hannu yadauki coffee data kawomai dake kan tray dudda baiyi niyyan cin abincin ba yakafa abaki daga kwancen dayake saida ya shanye duka sanan ya yar da cup din kasa, yaja bargo yana lullubewa dan bala’in zazzabi da ciwon cikin fitina ke nukurkusan shi kaman zai mutu.

next page, anjima da magrib, in sha Allah
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    4️⃣3️⃣

Dan shiru yayi na yan seconds kafin ahankali yace “is that all you want namiki koda wasu abubuwan kuma?” da sauri tajuyo tai facing nashi tace “kaga ko inaso da asuba idan katashi kaje mosque kai sallan ka a jam’i bayan ka idar kai azkar kai karatun Al ‘Qur’ ani saika dawo gida ka chanza kaya kazo gym kai training sosai harsai zufa ya wanke ka sanan saikaje kayi wanka, dazaran kayi wanka saika shirya office saika shigo flat dinmu na ganka naji dadi araina sai muyi breakfast tare, bayan munyi breakfast tare saiku fita tareda Dady katafi office, around 4 idan kadawo kai wanka ka chanza kaya saika fita ball irin yanda samari sukeyi da yamma sai bayan magrib saika dawo gida kasake yin wanka kahuta shikenan abinda nakeso” tamai wani irin murmushi tana kallon fuskanshi, shidai inhar zai dinga ganin wanan murmushi a fuskanta always inkuma har abinda takeso kenan zai iya mata kome takeso aduniyan nan, he love he has for Aneesa knows no boundary, lumshe ido yayi yabude yace “shikenan I will do anything for you Fateema na” murmushi tayi akunyace tana boye fuska murya chan kasa yace “kinsan ni menake so kimin?” da sauri tadago kai ta kalleshi tana girgizakai, ahankali yace “banson kikarama any namiji magana in your life, kowani taimako ko help kikeso komin ina nake ki kirani I will come, banson kowa ya rabeki, zan iya kashe duk wanda yazo yace yana sonki, kisa har lahira, u are my wife Aneesa, Ke gonata ce baby wanda ya isa yazo yace zai shiga gonata ko zai hada wata mu’amalat da ita, promise me I will always be the man u will always love till eternity” gyadamai kai tayi ahankali murya chan kasa tace “namaka Alkawari Ya Aliyu na” murmushi yamata yace “inaso nafada ma Dady ina sonki I want to marry you” makemai kafada tayi alamun a’a, kaman zaiyi kuka yace “why now?” ahankali tace “kaga Ammi na da Abban ka basu dade dayin aure ba mubari sundanyi kwana biyu saimu fadamusu, kumani inaso nai jamb har University nafara ko 100 level ne saimuyi aure” girgiza mata kai yayi kaman zai sakin mata kuka yace “zan iya jira kiyi jamb din tunda ending of this month ne but bazan tsaya jiranki har kifara University ba, ni nakosa nai aure, nakosa kizama matata ki haifan mini plenty babies” murmushi tayi akunyace zai sake magana washing machine din ya shiga kara din din din, alamun yagama wankin tass, kashe machine din yayi yaciro mata kayan yasa mata a bucket yace “muje backyard muyi shanya” daukan mata bucket din yayi itakuma ta dauki empty basket din suka fita har sunkai wurin kofan fita tace “laaa Ya Aliyu ka manta bakadau neck tie din Dady dayace ba” murmushi yayi yace “bakin mantan dani duniyan danake ba, am coming” ajiye bucket din yayi yawuce yakoma ciki tanabin bayanshi da kallo ganin haryadan soma chanza mata daga fara excerise dinshi, akasa ya hango necktie din kusa da kofan wani dan daki haka da suke zuba su omo da hypo abubuwan dai wanki , tsugunnawa yayi yace “gat u” yadauka harzai tashi idanunshi suka sauka kan kafafu hudu tacikin dakin omon, da alamu akwai mutane a wajen kenan all maganganun dayayi da Aneesa angama saurara kafafun babban mace dana yarinya dayagani ne yasa bai bude kofan ba yatabe baki yamike tsaye yasami Aneesa abakin kofa sukai backyard a binsu ko ajikinshi.

Ahankali Mama tabude kofa tafito Hajar datai kini kini da fuska biye da ita tace “nidama Mama naga yanda yake yawan kallon yarinyar, harda jiyama dasuka dawo, ashe sonta yake saisa ya wulakanta Nafisa” shiru Mama tayi tayi mugun nisa atunani, tabata Hajar tayi tace “Mama kinko maji menake cewa kuwa? Tunanin me kikeyi haka?” kallon Hajar Mama tayi for few seconds tace “Hajar lokacin koyama Aliyu lesson yayi and yarinyar nan dakike gani is what am going to use, shekara da shekaru ina harin yaronan Allah bai bani damaba yau da Allah ko yasa mukaji conversation dinsu is a sign cewa kome zanmai yanzu zanyi nasara” murmushi Hajar tayi cikeda jin dadi tace “Mama ki ramamin dukan da mugun yamini, sanan ki rama hana auren Rauda dayayi da Nazif,” gyadamata kai Mama tayi tace “uwa ta auri uban d’a, idan kuma nabari d’an ya auri yarinyan uwan aiza awayi gari mun rasa komine, duka kadaran mahaifinku maidama Aliyu da yarinyar nan su ubanku zaiyi to bazata yuba” dan rage murya tayi kafin tace “kawo kunnenki kiji Hajar” da sauri Hajar ta mikama Maman nata kunne cikeda kosawa taji me maman zatace, wani magana maman tafadi mata akunne a mugun tsorace Hajar ta fizge kunnenta ta kalli fuskar Maman tata tace “Mama kisan kai?” rawa jikinta yafara tana girgizakai tace “a’a gaskiya Mama, kema kinsan banson Ya Aliyu, na tsaneshi sosai kome zamumai mumai banda kissan kai Allah yahana wlh, a’a I always support you Mama kema kin sani but wanan no, kashe shifa Mama zamuyi how? Haba kashe rai nidai a’a Mama” wani mugun harara Mama ta watsa mata tace “dan ubanki kina dagamin murya so kike ajimu?” da sauri tace “sorry Maman mu, ai babu kowa a wurin, mama kinga dai karki kara furta maganan” dan dariya Mama tayi tana kara kallon koina ganin babu ko mahaluki daya yasa tace “listen to me jor, angayamiki banda hankaline? Bakiji kalmata ba zamuyi amfani da yarinyar nanne babu ubanda zaima san damu, we are going to use one bird to kill two stones, kinga dai yanzu daga maman ta har babanku babu wanda yasan da soyayyan su ko so is a good thing gwara mu aiwatar da abin kwanan nan tun kafin asan da suna soyayya, kawo kunnenki kiji plan dina” kunnenta Hajar tabata Mama tamata wasu maganganu dagokai tayi tareda gyadama Maman tasu kai duk tai wani iri harga Allah batason abinda Mama ke shirin aiwatar wa but Yaya zatayi hannunta Mama taja sukai daki tace “don’t forget abinda nafada miki yanzu aikin ki shine samusu ido and watch all their moves, kibar komi a hannuna I will not involve you in this kinji” tai maganan tana bude kofan dakinsu suka shiga inda Rauda da sauran yaran ke kallon cartoons, daure fuska Mama tayi dan haryau bata amsa gaisuwan Raudan sanan tawuce dakinta Hajar tabita abaya suka shiga suka rufo kofa, tabe baki Rauda kawai tayi tacigaba da kallonta abinta.

Yau asabar yaune second week din Ammi agidan Dady, wani irin rayuwa take ginawa itada Dady dako Aliyu abin burgeshi yake, tuni Dady yamata kyautan wata dalleliyar mota, dan Ammi is every with a plus arayuwan shi, she gives him happiness, kwanciyan hankali da komi, kome yace yanaso shi zai ci idan yanacikin matsala he don’t need to say it Ammi na ganin fuskanshi zata gane ta lallasai, in bed kuwa kullum saiyay sumbatu saisa ko kadan baya iya daga mata kafa, gurxanta yake kaman ba gobe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button