A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Shiru shiru har magrib driver basu dawoba balle su dauke ta har bayan sallan isha’i takira Alhaji yafi akirga baya dauka, ahaka har bacci ya kwashe su daga ita har Aneesan anan falo.

Kiran sallan asuba yatada Ammin tashi tayi ta tada Aneesa sukaje sukai sallan safiya sanan suka shiga gyaran gida ta kwashe abincin da Dady yasata dafawa jiya ta dumama snan tai tea.

Misalin 8 tana zaune a falo Aneesa zaune agefenta sukaji karan motan yan sanda a tsakar gidan da sauri Ammi ta tashi ta daga labule tana lekawa Dady ne yafito daga mota tareda wasu yan sanda ranshi abace cikin tsananin bacin rai yace “dukan ku kufito tsakar gidan nan, Kareema, Amina, Aliya da Rukayya gabaki dayanku kufito” yanda Dady yakira sunanta kai tsaye yasa tagane ba lafiya Aneesa dake gefenta ta kalla tace “ke bani hijabi na” hijabinta Aneesa tadauko daga kan kujera tabata tasaka sanan tabude kofa tafita Aneesa itama tsa hijabinta tafita amma ta tsaya agaban flat dinsu dan ba’a kira da yaraba itakuma Ammi tai inda suke sauran matan ma sun fiffito, ma’aikatan gidan Dady ya kwalama kira gabaki dayansu kusan ma’aikata takwas duk suka taho wajen aka tsaitsaya anan kallon Dady dagabaki daya ya chanza kana ganinshi kasan baida kwanciyan hankali.

Cikin tsananin fushi da mamaki Dady yace “as long as dasanina dudda abinda kukema Aliyu daidai magana ta banza na rana daya baitaba fadamuku ba, bari kuji da dukanku nan nake, na rantse da girman Allah, na rantse muku da girman Allah duk wanda yace shi da marayan d’ana zaiyi, yaron da baida mahaifiya, baida kani ko kanwa dasuka fito tajini daya, yaro shikadai, abin tausayin yarona, wlh duk wanda yace Aliyu zai taba zan iya ganin bayan mutum aduniyan nan, nida mutum zamu iya zuwa karshen duniya” Dady yay shiru sabida yanda zuciyar shi ke tafarfasa cikin wani irin tone kaman na wanda is about to cry yace “Aliyu was poison!” “innalillahi wa innailaihi raji’un! Poison kuma Alhaji” cewan matayen nashi da duk sunbi sun rude, cikin wani irin yanayin Dady yace “yes Aliyu was poison, idan kunga ruwan poison din da aka tsotso daga cikinshi saikun tsorata, Aliyu gadaishi nanne rai a hannun Allah baimasan inda kanshi yakeba, baima gane kowa, bakinshi gabaki daya yay jajir poison din yabata mai baki yarona na wahala rai a hannun Allah abinda kukeso kuji kenan ko?” Dady ya tambaye su yana kallon fuskokin su yace “dama kun tsaneshi so kuke ku kashe shi ko?” wani irin murmushi Dady yayi yace “to bari kuji kunga wayan nan yan sandan kusan su goma sha bakwai? Kowani dayansu na dauke da poison detector zasu bincika min kowani daki da lungu da sako na gidan nan, kusani, Allah kana shaida wlh kowaye kowaye yay niyyan kashemin d’a I mean kowaye billahillazi bazan barshi ba sai inda karfina yakare aduniyan nan, bazan taba yafema wanda yay niyyan kashemin Aliyu ba, hmmm” ya saukar da wata irin ajiyan zuciya sanan ya kalli yan sandan yace “kufara aikinku officer” cikeda girmanawa babban su yace “yes sir” sanan ya rarraba yaran nashi kowani yana turasu flat daban daban dan bincika ko ina nagidana, sosai gaban Mama ke faduwa tana kara tunani a inama tasaka katin maganin poison din badai tabarshi dakinta ba kaman kuma ta yarda abolan gaban kitchen din su Aneesa bolansu kai she’s contemplating dan tsabagen rudewa tarasa inda tasa daurewa dai tayi ta cije kar wani yagane matsalolinta duk suna tsaye kowanne da abinda ke running azukatan su har wajen minti talatin sanan saiga polisawan from various flat wanda suka fito daga part din Aliyu suka fito dauke da tray da pancake ke kai, sai mug din coffee.

Officer ne yanunama Dady mug da tray dasuka saka a forensic Bag yace “Sir he was poison ta wayanan abincin biyu, coffee akwai high level a poison a coffee nan sanan akwai a pancake dinan bari kaga” kallon daya daga cikin ma’aikatan yayi yace “get me water” da sauri mai aikin yatafi dauko ruwa officer kuma ya tsugunna ahankali yay unzipping bag din already da safan hannu a hannunshi yaciro mug din sanan yaciro pancake din daidai Gardner yakawo ruwa a babban buta karba officer yayi, ahankali Officer ya tsiyaya ruwa kan empty coffee mug din chaaaa ruwan yahau kumfa amma ba sosai ba sabida babu coffee saiya tsiyaya ruwa kan pancake din saiga kumfa shima nan wurin yadauki hayaniya, mikewa tsaye officer yayi ya kalli Abba daya tsaya yana kallon ikon Allah yace “waye yabashi abincin nan?” cikeda mamaki Dady yace “Aneesah nace tamai pancake da coffee but ai Aneesa can’t do this” da sauri officer yace “waye Aneesa” juyawa Ammi da gabanta kewani irin faduwa tayi takira Anessa dake gaban flat dinsu alamun tazo fara zuwa tayi gabanta na dukn uku uku daidai nan wasu polisawa guda biyu suka fito daga part din Ammi, wani katin nagani suka mikama ogan nasu daidai Aneesa ta iso wajen ahankali tace “gani” da hannu officer yadaga mata yace “tsaya tukunna” ya kalli Dady yamai pointing flat din su Ammi yace “wacece mai flat dinchan” da sauri Dady yace “amarya tace gatanan” yamai pointing Ammi dake kallonsu, dan ajiyan zuciya officer ya sauke yamikama Dady katin maganin yace “ga poison din da aka sama Aliyu a abinci nan, a bolan gaban kitchen din flat din amaryan ka aka gani” da sauri Ammi tace “innalillahi wa innailaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musibati wakhlifni khairan minha” taron jama’an yadauki kara kaman jira ake akira sunan ta Maman su Rauda tace “Allahu akbar ana zaton aga wuta tamakera sai akaga akasin hakan” cha cha cha sukahau yada kananun zancen duk Dady najinsu amma idanunshi nakan Ammi ne dayaga hankalinta yatashi and zuciyar shi bataso ta yadda itace no she can’t betray him like that, kallon officer yayi yace “officer are you sure wanan poison ne sanan are you sure a bolansu aka gani?” ahankali officer yace “gasunan daga shashinta suka fito ai bari kaga” tsugunnawa yasake yi duk aka bishi da kallo akai shiru ballo kwaya daya yayi yajefa a ruwan mug din kofin wani iri chichi hi ruwan yayi yafara komawa bakin kirin salati aka dauka ana tafi da sauri Ammi tace “Alhaji me zamuyi da irin wanan maganin, tunda nazo gidan nan ko ciwon kai bamu yiba bamamu da nagani balle har munsami wanan za…..” hannu officer yadaga mata yace “excuse me Madam ban katse kiba saura abu na karshe” wani karamin leda yamikama Dady da dan kunne kwaya daya keciki yace “wanan earing din kwaya daya munganshi akasan uwar dakan Aliyu ne” da sauri Dady yaciro dankunnen daga leda yadaga sama yace “dan kunen waye wanan?” faduwa gaban Aneesa yayi da sauri tasa hannunta ta taba dayan kunnenta aiko babu dayan da kunnenta, kafe dan kunen Ammi tayi da ido kirjinta na bugawa ganin dan kunen Aneesa ne tama kasa magana, ahankali Aneesa tadaga hannunta bakinta na rawa tace “n….n…nawane Abba” shewa Mama tadauka tace “ahayye nanaye idan baka mutuba zakaga abu aduniya” cikin fushi Dady yanuna Mama da yatsa yace “wlh kika sake cewa wani abu anan saina katseki da mari wawiya kawai” yajuya ya kalli Aneesa anatse yace “meyakai dan kunenki dakin Aliyu?” rawa jikinta yahauyi datama rasa dalili dawowa tayi kaman wacce bata iya magana ba kodan sabida yanda kowa na wurin kallonta ne oho bakinta narawa tace “y….ya… Aliyu yace nakawomai abincin bangaren shi cikinshi na ciwo bazai iya zuwa ba” da sauri officer yace “ta ina ya ganki yafada miki hakan?” bakinta narawa sosai tace “w….wa…ya” gyadakai officer yayi yace “ke kika dafa abinci ko kawai baki akayi ki kaimai?” ahankali tace “nina d…afa” “okay keda waye a shashin dakika dafa abincin” “n…ni kadai ne Ammi na wurin Abba?” “tun yaushe Ammi naki ta tafi wurin Abba? Kin fara abinci ko baki faraba?” muryanta narawa sosai tace “ban faraba….l…okacin” dan murmushi officer yayi yanuna mata katin maganin poison din yace “Aneesah sunan ki ko?” da sauri ta gyadamai kai, ahankali yace “kigayamin gaskiya, ni inhar mutum yafadamin gaskiya to komi na zuwan mai ta sauki inyamin karyane yakecin bakar wuya, a ina kika sami katin maganin nan? Kowani yabaki kisa karkimin karya bazan miki komiba, fadamin a ina kika sami katin nan? Wayabaki kisakama Aliyu a abinci?” girgixa kai Aneesa tayi hawaye ya gangaro tace “wlh, wlh nibansan katin maganin nanba, ni wlh banma taba ganinshi arayuwata ba wlh kuwan” hawaye suka zubo sharrr ta share da bayan hannu, murmushi Officer yasake yi yace “kin tsani Aliyu kin tsani Aliyu, luckily sai jiya babanshi yace kidafa mai abinci, sai abin yazama babu kowa adakin shine kika ciro magani kika samai danyaci yamutu hakane Aneesa?” fashewa da kuka tayi sosai tazo kusada Ammi tarike Ammi gam cikeda tsoro tace “Ammi kicemusu ni wlh bansan maganin nanba, ni bazan taba kashe Ya Aliyu ba wlh wlh kuwan” tafashe dawani irin kuka ajikin Ammi ahankali Ammi ke kallon Dady dayay shiru yana kallon Aneesan dake kuka girgiza kai yayi yace “No officer kubar yarinyar nan trust me something happen, Aneesa bazata iya kisa ba, dan ita tadafa abinci doesn’t mean ita tasaka poison, banda haka ba itakadai ne agidan nanba sanan kowa anan can enter bangaren Aliyu” cikeda rashin kunya da rashin mutunci Maman su Rauda tace “me kake nufi Alhaji Aneesa bazata iya kisa ba to mune kenan zamu iya? Sonkai kiri kiri sabida yar gaban goshin kace, mukake zargi kenan mune zamu iya ko, nagadai akwai CCTV agidan aje aduba mana hakanan nifa na tsani zargi koba hakaba Amina” da sauri sukace hakane wlh, officer ne ya kalli Dady yace “Sir akwai CCTV agidan nanne?” gyadamai kai Dady yayi yace “akwai a compound dinan, banda haka akwai CCTV a bangaren Aliyu dashi kanshi baisani dashi ba, CCTV tareda kwan lantarkin dakinshi yake, nasaka ne sabida nasan matayena sun tsaneshi zasu iya komi akanshi saisa nasaka?” da sauri officer yace “ina zamuga footage din” “muje yana secret room dina” ya kalli matan yace “kar wacce ta tafi daki kujiramu anan” hanyar flat din Mama Dady yayi da Officer, wani irin murmushi Mama tayi zuciyata tai sanyi dama takira CCTV ne sabida tasa aduba, Dady yazaci shi kadai ysan password din shiga dakin baisani batun yauba tasan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button