A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Dakin Mama sukayi sukai sama, agaban wani daki ya tsaya da handle din kenan kaman waya ga boturan dannawa, password din yasaka saiga dakin yabudu computers ne wurin shiga adakin, straight computer bangaren Aliyu Dady yanuna musu, officer ya zauna gaban computer yay rewinding back har zuwa footage din jiya, rewinding sosai yayi har zuwa daidai inda Aneesa tazo part dinshi ahankali yace “got it” tsayawa Dady yay akanshi ya shiga kallo kirjinshi na bugawa shigowa part din tayi rike da tray ta kalli ko ina kaman tana neman wani abu kafin suga tai tafiya da sauri ta shiga falon ta sauke tray din kan center table tana kalle kalle, sai sukaga ta chusa hannunta agefen zaninta basuga metayi ba sundaiga tafito da kwaya daya ta jefa a mug saikuma tadauko daya ta dagargaza kaman yanda ake dagargaza magi da hannu ta barbaza kan saman pancake ta kakkabe hannunta tadauka da sauri tai hanyar bedroom dinshi tabude kofa ta shiga dayake babu CCTV a bedroom dinshi basusan meya faru ba sundaiga chan tafito daga dakin aguje, baya Dady yayi zai fadi tsabagen yanda heartbeat dinshi yay weak polisawan suka tareshi suna salati wani irin fincike kanshi Dady yayi yafita daga dakin da mugun zuciya.
Tundaga yanda Ammi taga fuskarshi gabanta ya shiga faduwa ta shiga ambaton Allah, dawani irin zuciya Dady ke dumfaro su harya karaso inda suke tsaye hannu yasa yawani irin fizgo Aneesa dake tsaye kusada Ammi jikinta na rawa Dady baiyi wata wataba ya daga hannu ya watsa mata lafiyayyen mari “tass!” runste ido Ammi tayi dan har kashinta taji marin da Dady ya dauke Aneesa dashi, fashewa da kuka sosai Aneesa tayi tsabagen tsoro tamika hannunta tana kokarin kamo Ammi tace “wayyo Allah na Ammi, Ammi, Ammi, Ammi n….” zuba mata wani marin Dady yayi akaro na biyu da saita yasa tai shiru tai gum tama kasa magana sai dubu datake gani a idanunta cikin ihu da daga murya Dady ya jijjigata yace “me Aliyu yamiki? Meya miki kikeso kiashi lahira? Ubanwa yasaki kikashe min d’a??” yakara daga hannu zaikai mata mari na uku Ammi ta kirashi. “Alhaji” dago kai yayi ya kalli Ammi idanunta sunyi jajir suna shirin tsiyayar da hawaye, cikin raunin zuciya Ammi tace “kayakuri Alhaji ka kwantar da zuciyan ka abi komi ahankali, Aneesa bazata iya kisa ba, nasan abinda na haifa” cikin wani irin fushi Dady yace “nine makaryaci ko, kina zaton shiri nama yarki? Okay naji shairi namata a CCTV baya shairi ko to muje kigani” ya finciki Aneesa dahar lokacin bata gani sosai yay flat din Mama Ammi tabisu da sauri su Rauda dake kuka sosai da sauran matan Dady ma suka bisu har dakin cameran, shiga dakin Dady yayi rikeda Aneesa kaman wacce tai sata sauran matan ma da Ammi ma ta shigo cikin tsananin fushi Dady yace “play d footage back officer” dan bude idanu Aneesa tayi ta kafe computer da ido, wani irin faduwa gaban Ammi keyi lokacin da sukaga Aneesa ta jefa kwayar a mug da lokacin data dagargaza daya ta zuba akan pancake dakin yadau salati Mama tace “ga irinta nan ai, aure aure yau munga ranan aure aure, ka aurosu karufa mata asiri ka kawota gidanan da ita da agolan yarta, kahada yarta da namu gashinan suke son kashemaka d’a muda muke gidan nan shekara da shekaru ko kurjewa bamu tabasa Aliyu yayi ba amma gasunan dududu satinsu nawa a gidan just sati biyu da kwana daya” tajuya ta kalli Ammi tana mata tafi a fuska tace “to Allah yatona asirin ku, Allah yatona asirin ku kinyi amfani da yarki ta kashe Aliyu an kamaku, Allah saiya sakama Aliyu, butulu kawai murders, Aliyu daya dauke ku a matsayin uwa, andaiji kunya anji kunya, wlh hukuma ce zata rabamu daku, mutumin daya miki komi yafi fitaki kanmu harda siyamiki mota ne zaki kashema da” Dady jiyayi kirjinshi na tafarfasa kan maganganun Mama dan kaman tana sosamai inda kemai ciwone, cikin fushi Dady yajijjiga Aneesa dake kuka sosai yace “me dana yamiki Aneesa zaki kasheahi tell me the truth” fashewa da kuka sosai tayi tace “Abba wlh wlh, na rantse maka da girman Allah bani bane wlh, wlh kuw……” wani irin mari Dady ya kifa mata abaki saijini cikin ihu yace “stop lying! Stop lying kifadamin gaskiya, Maman ki tasa ki kashemin Aliyu kowane?” da sauri ta girgixa kai muryanta harbaya fita da kyau tsabagen kuka tace “wlh Abba banine ba, banine ba na rantse maka da girman Allah” cikin wani irin fushi ganin yanda take karya bayan ankamata dumu dumu yasa Dady yarufe ta da duka baji bagani tun Aneesa na ihu tana kiran Ammi hartazo takasa ihu ganin yana neman sumar da ita yasa officer da yaranshi suka rikeshi, yaciro ankwa daga aljihu yakama hannun Aneesa yasamata yace “with all the evidence damuka samu a kanki malama Aneesa, you are under arrest for attempt murder of Aliyu Muhammad Ibrahim you have the right to remain silent anything you say will be used against you” yajuya ya kalli Ammi dake kallon Aneesan dako numfashi bata iyayi yace “ki gayama yarki tafadi gaskiyan duk inda tasamo wanan poison din inba hakaba gidan yari ne makomarta” yaja Aneesan kaman yanajan kare sukai hanyar fita daga dakin Ammi ta tsaya still tana ma Dady wani irin kallo, duk fita akayi daga dakin akabi su officer dan aga inda zasuyi da Aneesa yarage daga Ammi sai Dady adakin, ko kallonta Dady baiyiba azuciye yazo zaibi tagefenta yawuce takama hannunshi tarike lumshe ido Dady yayi Allah kadai yasan iyason dayake ma Ammi dan tabashin nan datayi har brain dinshi yaji, kasa juyowa yayi hakan yasa ahankali Ammi ta zagayo ta gabanshi tasan Dady nacikin tashin hankali, ya acikin matsala saisa dudda uban dukan dayama Aneesa still tamai uzuri batason ko kadan taga bakinshi, ahankali tana kallon fuskan shi tai kneeling akasa ta hade hannayenta ta danne zuciyata sosai dan bata so ta karaya she needs to be strong and fight this battle for her daughter a yanzu Aneesa batada kowa sai ita she’s all alone, Murya chan kasa tace “Alhaji nasan kana cikin tsananin fushi da bacin rai amma dan girman Allah ka sauraren” tadanyi shiru tana sauke ajiyan zuciya tadaga fuskanta ta kallai har yanzu idanunshi a lumshe kaman bayamason ganinta ne, Murya chan kasa tace “Alhaji bantabajin daidai da atom of hatred towards Aliyu ba, na rantse maka da Allah ubangijin mu, ubangijin Al arshi wanda ya busamana numfashi, ubangijin sammai bakwai, wanda ya halicce ni ya hallice ka ya hallici duwatsu da dabboni Alhaji bazan taba tunanin bama Aliyu wani abu danna halaka shi ko kokuma wani abu mai kama da hakan, haka zalika zan iya rantsemaka Aneesa ma bazata iya hakanba, am not justifying abinda Aneesa tayi bakuma kokarin kareta nakeba, but dan Allah ka yakuri, ka sauko da zuciyan ka, dan girman Allah kasaka asaki Aneesa she is too small tazata san rayuwan gidan yari kokuma rayuwan police station the trauma bazai taba barinta ba, Allah kayakuri ka janye case dinan kasa asaki Aneesa tadawo gida let’s solve matsalan nan maturely, matsalan gidane let’s solve it at home dan girman Allah kaji”.
follow me lemme walk on the journey of visuals can be deceptive wlh
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
4️⃣5️⃣
Ko minti biyar baiyiba yawani irin yaye bargon da sauri yatashi zaune sabida jidayayi kaman hanjin cikinshi na harhardewa tundaga wuyan shi har zuwa cikinshi zafi yakemai kaman an watsa garwashin wuta akansu, wani irin kara yayi yana juyi “ahhhh” yajuya yana nukurkusu yana nishin azaba, azaban dayakeji yawuce misali, goran bottle water dake kan side drawer dinshi ne yadauka yabude ya kurba ko ya ragemai ciwon kaman yazuba gishiri a ciwo haka yaji hakan yasa yawani irin bankare yana ihu yana lankwashewa……