A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Shigowa gidan Nazif yayi yay parking motarshi Mama dahar lokacin ke jikin window tana kallon komi dake faruwa na tsakar gidanne gabanta nafaduwa tana addu’a Allah yabata nasara ne tabude kofa da sauri tamai alamu da hannu daya yakarso da sauri, karasowa yayi kafin ma yay magana taja hannunshi suka shiga dakin tamaida kofan falon tarufe, hada ido yayi da Rauda dake zaune da kanninta suna kallon cartoon, daure fuska tayi kaman batasan shiba dan ta mugun tsananshi yanzu, hararanta Mama tayi tace “bance ki cinyemin d’a da idanunki dasukai kama dana ubanki ba mai bakin hali kawai, common tashi kifitan min daga flat, wuce kitafi wurin Yayan ki mayya nasan abinda kikeso kenan” da sauri Rauda ta kalleta dan bata yadda da abinda taji Mama tafada yanzun nanba, anya Mama ce zata turata wurin Ya Aliyu willingly kuwa?, cikin daga murya da masifa Mama tace “kindaiji menace ko, tashi ki barmin daki kiwuce wajen Yayanki magana zanyi da Nazif mai mahimmanci” dawani irin gudu Rauda tai tsalle ta mike tsaye tai hanyar fita Nazif yabita da kallo, cikin rawan jiki Mama tace “kai yanzu ba lokacin kallon Rauda bane wani muhimmin abu nikeso kamin yanzun nan muje kaga” sama tai dashi wani dakin Dady tabude ta shiga yana biyeda ita tasa Hajar gadi afalo dazaran taga Abba kokuma Rauda tafada mata kota mata signal…….

Sallama Rauda tai a part din Aliyun jin shiru yasa tabude kofa ta shiga abinta ta maida kofan tarufe tana hararan TV dake aiki a tashan kwallo tace “shi ya Aliyu kullum, kullum ball, ball ball uhm” tai maganan tana daukan remote ta chanza channel zuwa cartoon ta ijiye remote din tai hanyar bedroom dinshi tana kwalmai kira. “Ya Aliyu, Ya Aliyu kana bathroom ne? Ya Aliyu” agaban bakin kofanshi ta tsaya tai knocking jin shiru yasa tabude ahankali dan tasaba shiga dakinshi kai tsaye daman kuma baya hanata, dayake itama daga rana take batagani sosai dudda bedside lamp dinshi akunne yake, ahankali tadaga hannunta zata kunna switch din wutan dakin tace “bacci kakene Ya Aliyu?” kunna wutan tayi dakin yay haske, idanunta ne suka sauka kan Aliyu dake kasa yana wani irin mimmikewa kaman wanda ake zarema rai idanunshi na juyawa, harshen shi yafito daga bakinshi wani irin kumfa nabin gefen bakin nashi, wani irin talo idanu waje Rauda tayi tana kara kallon Ya Aliyu danta tabbatar shine koba shi bane yana sanye da dogon jeans dinshi blue jikinshi ba riga lying on the floor yana fizge fizge jijiyoyin wuyanshi dana fuskanshi sun fito tsabagen yanda yake stretching din azaba, wani irin ihu Rauda tayi da saida gabaki dayan flat din Aliyu ya amsa. “Ya Aliyuuuuuuuu!” da gudu tai kanshi ta tsugunna agabanshi tana tabbatashi bama tasan metake yiba. “Ya Aliyu, Ya Aliyu, Ya Aliyu menene menene wanan sabulu kasha ne?” ganin Aliyu baimasan waye akanshi ba kakkari yake yana har yanzu harshen shi awaje bakinshi nafitar d kumfa yasa tai wani irin jumping tsaye tama rasa mezatayi da gudu tafita tana kwalama Dady kira da duka muryanta. “Dady, Dady, Daddy Ya Aliyu” yanda take kwalama Dady kira zaka zaci ta haukace ne da gudu tai flat din Dady hannu ta daura kan handle ta shiga murzawa amma kofan a kulle hakan yasa tasa duka hannayenta ta shiga bubbugawa tana kwalama Dady kira. “Daddy, Dady, Dady Ya Aliyu, Dady ya Aliyu zai mutu wlh, wayyo Allah Ya Aliyu Dady”

Kaman daga sama Dady yaji ana bubbugawa kofa ana kiranshi da sunan Ya Aliyu dayake suna bedroom ne saisa basujiba, Ammi ce ta tureshi tace “subhanallah, Alhaji Aliyu, tashi muje muga” da sauri Dady yadagata yadau boxer shi yazura tareda daukan jallabiyan shi yasa yay sitting room dinshi da sauri, doguwan riga ta Ammi tazura tareda saka hijabinta tabi bayan Dady da sauri, daidai Dady yabude kofa, da sauri ya tare Rauda dake neman zubewa muryanta harya shake tsabagen yanda take kwalamai kira, da sauri yace “subhanallah bani ruwa Ummu Aliyu” da sauri Ammi takoma ta dauko ruwa tabude mai tabashi karba yayi zaibama Raudan ta karban da hannunshi ta hanyar mikewa daga jikinshi tamai pointing flat din Aliyu tana haki tace “D….Da…dy, Ya….Y….Al….yu mutu, mutu zai mutu” arude Dady yace “w….. Wat? Meya sami Aliyu na?” kasa magana tayi dan her heart is beating way too fast zaunar da ita yayi a wajen yace “jikina yabani ba lafiya zauna da ita anan Ummu Aliyu, bari nadubo Aliyun” da dan gudu gudu sauri sauri Daddy yay flat din Aliyu tareda tura kofan yana kiran Aliyu. “Gadanga na, Gadanga na kana ina? Meya hadaka da Raudan ka ya……” kasa karasa maganan yayi sabida yanda yaga Aliyu na kakarin mutuwa kumfa nafita daga bakinshi kaman yana wasa da shower gel, wani irin bugu kirjinshi yabada “dududu-dum!!!” bakinshi ma rawa ya shigayi, baimasan takamaimen inda hankalinshi yake and not knowing mema zaiyi, ahankali yadaga kafanshi yana pointing Aliyun da yatsa yace “Gadanga na mehaka kakeyi you know this is a hard joke ko” yay maganan yana tsugunnawa agabanshi ahankali yakai yatsanshi kaman wanda yazare yadaura kan tongue dinshi yace “me haka kakeyi? Why are you playing with your tongue kamaida shi ciki wai liquid sabulu ka kurba ne da bakinka ke kumfa haka Gadangana? Why are you struggling and stretching like this? Me kake jujjuya idanunka kana kafar da idanu iyye, kai Aliyu, Son” Dady yakirashi yana jijjigashi……

Ganin Rauda tadawo daidai yasa Ammi ta shafa kanta tana mata murmushi tace “menene why are you like this? Laifi kikama yayan naki?” da sauri Rauda ta girgixa mata kai tace “Mum Aliyu mutuwa Ya Aliyu zaiyi wlh he’s doing somehow?” adan rude cikeda wani irin yanayi Ammi tace “kaman ya mutuwa zaiyi, what sort of joke is that?” da sauri Rauda na kuka sosai tace “wlh wlh da gaske naje dakin naga…..” Ammi bamata tsaya taji mezata ceba ko takalmi ba tasaka ba tai flat din Aliyun tabude kofan, babu kowa falo saidai taji maganan Dady sama sama hakan yasa tai hanyar inda takejin maganganun Dady, abude Dady yabar kofan hakan yasa ta tsaya tsak numfashinta yadan tsaya kafin ahankali yadawo ta shigo dakin sosai tana kallon yanda Dady ya rungume Aliyun dake mukurkuso yana surutai da bamata gane meyake cewa da sauri ta tabashi tace “Alhaji, Alhaji tashi mukaishi asibiti” kallonta Dady yayi for some seconds saikuma yamata murmushin nan nashi mai kyau yace “wasa yakeyi min, soyake yaga nadamu, my Boy is playing pranks, April fool ne don’t worry ummu Aliyu, wasa yake mana ba dazunan muka dawo daga gidan rasuwa tareba so he’s just joking” ahankali Ammi tace “innalillahi wa innailaihi raji’un” kafin da sauri tamike tsaye tafito da saurinta da Rauda dake kuka sosai sukaci karo, da sauri Ammi tace “jeki kiramin bodyguards din baban ku da driver ku imaza Rauda” da gudu Rauda tajuya Ammi kuma takoma daki ko one minute ba’ayiba bodyguards din Dady suka shigo dakin ganin Aliyu ba karamin hankalin su tashi yayi ba da sauri sukai wajen suka karbeshi daga hannun Dady, Dady yamike tsaye yace “kai ina zaku kaimin d’ana wasa fa yakemin” da sauri Ammi ta girgixa mai kai tareda cupping face dinshi ahankali tace “Alhaji look at me, kadawo hayyacin ka okay, Aliyu is sick you need to be back a hayyacin ka your son needs you, call ur doctor Alhaji” da sauri ya lumshe idanunshi kafin ahankali yabude maganganun Ammi sun shiga brain dinshi sunyi resetting na brain din ahankali Ammi tace “kace innalillahi wa innailaihi raji’un” ahankali batare daya bude idanun ba yace “innalillahi wa innailaihi raji’un, Ummu Aliyu da gaske Aliyu na nagani lying here kumfa na fita daga bakinshi?” hannunshi Ammi tarike tace “let’s go to the hospital first bodyguards dinka sun fita dashi” da sauri suka fita Ammi ta zura wani takalmin Aliyun datagani abakin kofa tabi Abba Rauda ma tabisu tana kuka sosai, sauran Matan Dady duk suka fiffito suna kallon ikon Allah jin hayaniya da kukan Rauda daya cika gidan sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button