A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Ahankali Aneesa da tun lokacin dataji muryan Rauda na kwalama Dady kira ta tashi ta tsaya a window tana kallon tsakar gidan tana kuka sosai ta sulale akasa gani datayi anfito da Aliyu kaman wanda yamutu kumfa nabin bakinshi yana did diga a compound dinsu, sai karanto duka addu’an datasani take so dama da gaske yake baida lafiya dama da gaske ne, she regret abinda tamai she regretted it, wani irin kuka tafashe dashi da tadade batai irinshi ba.
Wani babban private asibiti number asibiti da manyan Abuja keji dashi suka tafi, tun kafin sukai Dady ya danna ma babban likitan asibitin kira akan gashinan zuwa da danshi baida lafiya atanadi komi, Ammi tasan cewa Dady na tsananin son Aliyu amma bata taba sanin haka yake mai wanan mahaukacin son ba, Alhaji yadawo kaman wani zararre har fakan idanunshi take tana tofamai addu’a akai sanan tana kiramai sunayen Allah yana karba, cikin ikon Allah suka kai asibitin already anzuba nurses da hadadden gado agaban reception ana jiran senate president da danshi karban Aliyu da kaman babu rai ajikinshi sukayi ciki dashi Dady yabisu akai theater dashi aka rufo kofa batare da anbari Dady yabisu cikiba,.
Ahankali Ammi tazo har inda take, dan murmushi yakakalo mata ganin yanda dukta damu fuskarta ya shafa murya chan kasa yace “kidena damuwa am fine okay” gyadamai kai tayi tareda kakalo mai murmushi dan tasan he’s just saying that to make her feel better, to calm her down, ahankali yace “muje su kaiki gida kiyi wanka akwai najasa a jikin mu” cikeda damuwa Ammi tace “kaifa?” “anjima zanzo nai wankan in sha Allah” gyadamai kai tayi tarike hannunta cikeda so sukai inda bodyguards dinshi suke tsaye yace “ku kaita gida” cikeda girmama wa sukace to sukai gaba Dady yace “bisu, I love you” gyadamai kai tayi ahankali tace “I love you too, be safe for me okay” gyadamata kai yayi tajuya tafita tana waigenshi kaman yanda shima yakasa dena kallonta yana bala’in son Ammi sosai harta shiga mota saida aka tada motan sukabar asibitin sanan yakoma gaban dakin yaciro wayanshi daga aljihu ya kira Momma.