A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
Sai fushi fushi yake sabida Dad baikiraba shikuma bazai kirashi ba saisama yabarma bodyguard din wayar dan yasan in yana hanunshi zai iya yakirashi, ya tsani British Airways dan sunada wani banzan dabi’an batarma da mutum luggage saisa tun jiyan yasa suyi booking air France, sai tunanin uban zaman dazaiyi cikin jirgin yake inhar basuyi stopover ba flight dinshi is 18hrs flight inkuma jirgin ya tsaya for fueling ko cleaning kokuma wani dai emergency, kokuma weather issue zasu iya 20hrs or more than sef saisa he came prepaid yasa kayan sanyi idan ya shigama he will request for a blanket or showel duk wanda suke danshi gaskiya shi bazai saka pyjamas din airline ba, kuma yanada matsalan jin sanyi sosai, checking in sukayi suka karbi ticket sukai departure lounge basu wani dadeba suka fara boarding karfe 7:15 jirgin su yadaga sai kallon lokacin yake yana kokarin hararo wat time is it yanzu a Nigeria, dan Nigeria is almost 9hrs ahead of California, dan murmushi yayi ganowa dayayi yanzu darene a Nigeria probably hala Dad yay bacci saisa bai kirashi ba.
8:40 na dare jirgin su yasauka a Abuja, fitowa sukayi kana ganinshi kasan yagaji sosai saukowa suka farayi bodyguard dinshi biyeda shi, wuraren Tara suka gama komi suka fito ta arrival sai kalle kalle yake ya tsaya chak dan baiga wani nashiba baiga wani direban gidansu ba baiga Daddy ba, wani irin haushi ne yakamashi yamikama bodyguard hannu alamun yabashi wayarshi, karban wayan yayi dayariga ya kunna mai ya shiga dialog Dan kiran Dad dinshi, fizge waya yaji anyi daga hanunshi da sauri yadago kai wani magidanci ne kamansu daya sak dan shima farine sol alamun tsufa daya bayyana tattare da magidancin ne zaisa kawai kagane ba yan biyu bane uba da d’a ne, dudda fushi yake da Dad amma baisan lokacin dayasaki wani murmushi ba yawani irin rungumeshi ba so tight yace “Daddd dy” murmushi sosai mutumin yayi yana bubbuga bayanshi yace “na’am Aliyu na, sarkin zuciya, Aliyu an mazajena” dariya daga shi har Aliyun sukayi sanan yasake shi ahankali yana kallonshi kaman yanda yake kallonshi yace “muje kahuta kagaji da yawa karka fadi” sukai wajen mota bodyguard na binsu abaya, motoci biyune bodyguard suka shiga dayan Daddy da Aliyu kuma suka shiga motar Daddy, kwanciya yayi ya daura kanshi kan cinyar Dad yana yatsine fuska, kallo baban nashi ya binshi dashi yana mamaki yaushe Aliyu zai chanza yadawo namiji, son jikinshi da rashin kuzari is too much, hanunshi ya chusa cikin kanshi yana mishi head massage yace “sannu kaji Son kagaji sosai ko?” gyadamai kai yayi idanunshi a lumshe yace “bakaine kawani ce mutum yadawo ba, I need hot bath jikina kaman an kakkaryani Dad” “tooofah, sannu yaron kirki, muna zuwa gida zakai wanka kaci abinci saikai wanka abinka” gyadamai kai yayi a shagwabe yana sauke ajiyan zuciya yanajin dadin yanda Dad kemai headmassage din.
Agaban wani babban gida sukai horn wani soja yabude musu Gate din, tashi yayi ahankali ya zauna yana kallon babban gidan nasu da babu kowa a ciki, shiga ciki sukayi sukai parking bude musu kofar motar akayi, ahankali suka fiffito daga motan yana kallon gidan, babban gidane dake dauke da manya manyan flat flat guda hudu, sai daga tachan dayan bangaren kuma wani babban flat guda daya ne, shidai babu yanda zaiyi da Dad ne amma harga Allah baison dawowa Nigeria ba, ya tsani gidan mahaifin shi sosai, he hates this house with all his heart, dafashi da akayi yasa yadaga kai ya kalli Dad din yadan turo baki kaman mai shirin yin kuka, murmushi Dad yamai tareda sumbatan goshinshi yace “all is well Aliyu am here for you kaji relax, muje” gyadamai kai yayi suka fara tafiya bodyguard kuma nawajen mota suna fito da kayayyakin su daga boot, wata yar budurwace doguwa dabazata wuce 20yrs ba sanye dawata doguwan rigan atampa tafito daga wani daki dasuke kira da laundry tariko wani white folded zanin gado a hanunta tajuyo, ganin Aliyu tareda Dady yasa ta tsaya chak tareda bude baki cikeda mamaki danko kadan Dady bai sanar dasu zai dawoba, tsayawa Aliyun yayi shima yana kallonta da idanunshi dake cikeda gajiya, murmushi Dady yayi yace “gata wajenka nan ai banfada mataba I want to surprise her taganka kawai kaman daga sama” murmushi sosai yayi yana kallonta batare dayace mata komiba ya daga mata gira daya alamun kallon fa baki sanni bane? Watsar da zanin gadon tayi akasa tsabagen rudewa tasa hanunta takai kan saman idanunta ta murza idanun irin ta kara tabbatarwa ba gizo idanunta kemata ba sanan tabude su, tagadai still dai yana tsaye inda yake kusada Daddy dake sanye da babban riga that means Yaya Aliyun tane, wani irin ihu tayi dayacika gidan. “Yaya Aliyuuuu, Yaya Aliyu oyoyo” ta tafi dawani irin mugun gudu hakan yasa yabude mata hannu da gudu taje tai wani irin tsalle tafada jikinshi ta rungumeshi sosai her heart couldn’t contain her happiness sai kuka, hakan yasa Dady yace “kagamin shagwababbiyar yarinya, kin wani dane jikinshi zaki karyamin shi saikuma ki sakinmai kuka dukshi kadai, haukatashi kikeso kiyine daga dawowan shi, cikashi” kojin maganganun Daddyn suma batayi sai kuka take bayanta ya shafa ya bubbuga alamun tai shiru, jin karan bude buden kofofi wanan nabin wanan yasa yadago kai matayen Dadyne kowacce tadan leko dakai daga flat dinta ga yara manya da kananu duk sunaso sufito suga ihun mai akeyi a tsakar gida sun hanasu fita, fuskarnan bayabo ba fallasa duk sai kallonshi suke kaman yau suka fara ganinshi, babban cikin matan ne tadan tabe baki tace “ahhhh manyan baki su Aliyu ne agarin, mutanen turai saukan yaushe ko sanarmana ba’ayi ba, hala cinye dan gwal din zamuyi maigida” tasake tabe baki tana kallon Rauda da har lokacin ke rungume da Aliyun tace “sannu da zuwa Aliyu, kekuma ina zanin gadon danace kikawo min uwar shishigi?” kafin Rauda tai magana Dad yace “ahadama Aliyu lafiyayyen abinci Kareema” dan juya ido tayi tace “haba Alhaji saida abinci yakare kasan yawan yaran gidan nan gasuda shegen ci barin ma yaran Amaryan ka, aida kafadamana zaizo dasaimu saka dashi a girki, shi yaro kasan bacin abincin yan aiki yakeba dasai ace suhadamai koyar Indomie ce, kaga kumani wash Allah” tadan yatsine fuska tana dafa kafarta tace “kasan ina fama da wanan ciwon kafan bazan iya shiga wani kitchen ba Alhaji sanyin kashi dazaran dare yayi saidai kaji kasusuwana nakiran salla” shiru Dady yayi yana kallonta baiso yay hayaniya agaban Aliyu da dawowan shi kenan baiso yatadamai da hankali da sauri Rauda ta tashi daga jikin Aliyun tace “nizan ma girki kaji yayan mu, maizan dafama?” kafin ma yay magana Kareema tace “wai bazaki wuce kidau zanin gadon chan dakika watsar akasa kije ki shimfidamin agado ba” wani mugun kallo Daddy ya watsa mata yace “kije ki dauka dakanki, girki zatama dan uwanta” Daddy ya kalli Raudan datai zuru zuru dan tsoron masifar uwarta take Yace “wuce je store ki dauko all abunda zakiyi amfani dashi kizo side din Aliyun kiyi girkin awajen” gyadamai kai tayi tace “to Daddy” tama Ya Aliyun murmushi tajuya da sauri tawuce, Dady ya kalli sauran matan biyu dasuka tsaya suna kallonsu yace “duk baku iya gaisuwa bako” ko wacce da kallan nata reaction din dasukayi da kyar sukace “sannu da zuwa Aliyu” ko amsasu Aliyu baiyiba Yajuya yay part hanyar side dinshi, Amaryan Dady mai suna Amina tace “yaro baisan ya gaida manyan Shiba saidai asa manya su gaidashi sabida sonkai, mumadai Allah bamu y’ay’a mazan nan, kuma kar wata takara kiran yarana ” dan juyowa Dady yayi ya kalleta jin yanda take jefanshi da kananun magana ta shige dakinta baice komiba amma wlh duk zasuci ubansu yasan maganin su, shida sune su zuba indai kan Aliyun dudda sun haifamai yara zai iya sakin yan bura’uba yakawo nany su kulamai da yaranshi, billahillazi duk wanda zai tabamai Aliyu marayan danshi nan mara uwa sai yay yakin biafra da mutum.
[4/5, 8:05 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA