BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Har ya futa ta bishi a bays hannuta rike da ledar magani tace.” Ka manta kuma.” Shiru yayi yana nazari,hannu ya mik’a ya karb’a sukayi sallama ta koma gida

Mota ya bude ya zura ledar maganin kusa dashi ya zauna sosai hade da kunna motar mai gadi ne ya mik’e da sauri ya bude masa Gate ya futa daga gidan.

Kai tsaye,……. Gidansu Asma’u ya nufa.

5/November/2019
[11/6, 5:13 PM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

42

Yana tafe cikin mota yana sauraron wak’ar Joy mutumin shi, gyada kansa yake da alamun Yana jin dadin wak’ar, sai da ya kusa shiga unguwar tasu ne ya kira Mimi a waya, lokacin muna zaune a tsakar gida bayan mun gama cin abunci muna ta fama da wasu shegun cinna ku da suka addabe mu, dama duk lokacin damuna haka suke futowa a gidan ta cikin ramuka suyi ta cizon mu. Wani ne ya cije ni a hannuna ina ta faman sosawa hade da haska gurin da toch din wayar Mimi neman sa nake in kashe, kira naga ya shigo wayar Heartbeat abunda na gani kenan, siririn tsaki naja hade da mik’a mata wayar ta karba hade da tashi daga gurin, Umma ta bita da kallo tana girgiza kanta. Minti uku sai ga ta ta futo da wayar a hannu tana sink’e kai Umma tace “Waye ya kira ki harda barin gurin.”?
A hankali tace” Amajad ne, yazo Umma.” Sakin fuska tayi tace” To masha Allahu, alamu sun nuna ke yake so, tunda gashi ya kira ki a waya yazo zance maza je ki shirya Ubangiji Allah ya sanya alkairi.” Umma ta k’arashe maganar cike da murna da farin ciki.

Mimi ko kunya ta shiga dakinmu da sauri, sai abun ya bani mamaki ganin d’azu take kuka tana cewa ta hak’ura dashi ta barmin amma dubi yanda take rawar kafa saboda zuwan sa. Ni dai shiru nayi kawai, har ta futo Cikin shiri sai zabga kamshi take. Tace”Umma sai na dawo.” Umma tace.” Ki gaishe shi da kyau kuma ki iya ladabi da biyyaya.” Tace”To tana k’okarin futa sai farin ciki take.
Hira muke da Umma sama-sama nake jin ta domin a lokacin bana cikin hayyacina wani irin lami bakina yayi sai kace mace mai yaron ciki haka nake jin wata irin kasala da sagewar gwiwa jiki babu k’wari na shige dakinmu hade da fadawa kan katifa ruf da ciki rumtse idona nayi sam zuciya ta babu dad’i ni kadai nasan abunda yake damuna.

Parking yayi bakin hanya hade da kunna Fitilar wayar sa, unguwar duhu dumd’um!! Sai hasken masu ababen siyarwa dake kan hanya, masu charge masu wanki da guga, masu provision da sauran su, yaji dadin haka domin baya son ya futo har jama’a suka gane shi, wayar Mimi ya kira hade da fada mata gashinan ya iso. Lokacin tana kan hanya. Inda ya Saba parking ta nufa cikin yanayin tafiyar ta tsallaka titi tayi ta isa kusa da motar hade da d’an kwankwasa wa, a hankali ya bude motar tare da haske fuskar ta da wayar hannunshi, sakin Fuska yayi yace.” Momy na tafi ta kowa.” Mimi tayi wani fari da ido. Yace.” Shigo ciki mana.” Cike da kunya ta shiga motar ya mai da murfin ya rufe. Kashe ta yake da kallonsa na goggun ‘yan duniya, sunkuyar da kanta take tana fadin”Sonka zai iya kashe ni.” Cikin zuciyar ta tayi maganar
Yace.” Bamu gaisa ba Momyna kunyar ki na bani mamaki tana d’aya daga cikin abunda yasa naji kin kwanta min a raina”
Mimi tayi murmushi yace.” Ok ni ne yafi kamata na gaishe ki tunda nine danki. Kinga kuwa dole in nemi albarka.” ‘Yar dariya tayi sai kace sokuwa, tace”Ina wuni”?

Cikin sangarta yace.” Umum!! Nine zan fara gaishe ki.” Mimi taji kamar tana yawo kan gaji mare don shauki gaskiya guy nan ya iya love.

Yace.” Ya jin dadin ki Monyna hope komai lafiya Lou.”
“Alhmdullahi wallahi.”
Tafad’a fuskarta dauke da murmushi
“Ina Asma’u?
ya tambaye ta kai tsaye!!! Wata irin fad’uwar gaba taji jin ya baci sunan Asma’u.
Bakinta na rawa tace” Tana gida.”
“Owk d’azu mun Dade da yayan Ku a waya ina fatan duk kunji sak’ona ni Amajadu zan aure ku dake da ‘yar uwarki Asma’u.”
Gyada kanta tayi tace”Ya fada ma Umma.”
“Masha Allah.” Ya fada da murmushi a fuskar sa, shiru na minti biyu sannan yayi gyaran murya tare da fadin” Shikkenan kije gida sai munyi waya, sai ki kira min Asma’u itama muyi zance kamar yanda mukayi dake.”
Jiki babu k’wari Mimi ta bude mota ta futa, ya bita da kallo had’e da fadin “Kar ki manta fa ki kashe wayar ki, kafin in kwanta ina son jin muryar ki.” Mimi taji wani sanyi ya tsirga mata a zuciyarta murmushi ta saki tare da fadin”Insha Allah.”
Hannu ya d’aga mata ta tsallaka titi kana ta shiga layin su.
Umma na zaune a inda take tace”Har ya tafi.”? Mimi tace”A’a Asma’u yace.” A kira masa.” Umma tayi shiru cike da mamaki tace.” Asma’u Kuma. ” daga Kai Mimi tayi.
Ina kwance a dakin ina jinsu sama-sama, domin bacci ya soma hawa kaina.
Ina jin sanda Umma take fadin “Sai kije ki kira ta tana daki.”
Mimi ta shigo dakin hade da tsayawa a kaina tana kiran sunana.
Banza nayi mata.
Tace” nasan dai kina ji don yanzu ba lokacin baccin ki bane, kije Amjadu yana kiran ki.”
Mik’ewa zaune nayi nace”Uwar me zanyi masa.”
Tace”Idan kinje sai kiji.”
Yanda ta fad’i maganar na gane taji zafin zagin da nayi.
Tsaki nayi na koma na kwanta.
Tace.don Allah ki tashi kije babu kyau wulakanci.”
Ina daga kwance nace”Kin San Allah Mimi babu inda zanje domin ban ga tsiyar da zan masa ba.
Futa tayi daga dakin.
Can naji Umma na kwala min kira.
Mik’ewa nayi da sauri na futo tsakar gidan INA amsawa
Fuskarta a hade tace “kije kiran da ake miki ko ranki ya b’aci.”
Shiru nayi raina a bace
Cikin tsawa tace.” Ko bakya ji ne.”
Nace” Tom Umma” dakin mu na koma na zurmo hijabina na sallah na futo silafas na zura a kafata na futa.
Tsayuwa nayi a waje ina tunanin ko in lab’e a wani gurin ne. ?
Wata zuciyar tace” kije ki kare masa rashin mutumci tunda yazo unguwar Ku.
Aikuwa tafiya nayi inda nasan zan ganshi
Can na hango motar shi kasancewar ya kunna futular motar.
Ina zuwa gurin na buga motar da k’arfi. Budewa yayi hade da haske fuskata da hasken wayar shi, kalon-kalon muka fara ni dashi. Gani nayi ya kauda kansa yana dariya
Haushi da takaici suka kama ni, sai kace mahaukaciya ya tasa ni a gaba yana dariya. Cike da takaici naja tsaki hade da juyawa da niyyar tafiya, ji nayi an fuzgo min hijabi da k’arfi na fada cikin motar.
Jikinshi ya kwanto kaina ya rufe motar hade da sanya mata security, kallonshi nake a tsorace! Naga fuskarsa a mutukar murtuke Yayi bala’in shan kunu irin Wanda bai tab’a yin irinsa ba,
Ya hasko fuskata sosai da wayar shi, Yana kallona tare da ya mutse fuskar sa.
Kauda kaina nake ganin yadda ya dallare min ido.
Hannunsa guda ya sanya ya shak’o wuyana dake cikin hijabi, Murya k’asa-k’asa yace.” Maimata irin zagin da kikayi min a waya jiya.” Kifkifta idona kawai nake, ya k’ara shak’e min wuyana hade da d’aga kaina sama sosai, yace”Ko bakya ji ne.”?
Da kyar na samu na kakaro magana nace”Sakar mun wuya kar ka kashe ni.”
Kin saki yayi sai ma kara damk’e wuyan yayi, hannuna guda na sa ina kokarin b’anb’are hannunsa daga jikin wuyana, ko motsi ya kiyi, wuyana yayi bala’in sagewa, nace”Ka Sakar min wuyan……. Ka tsani Yayi ta hanyar fad’in” Ki maimata irin zagin da kikayi min jiya Zan sake ki.”
Babu wasa a cikin maganar sa.
Hawaye na ziraro min nace”Wane irin zagi nayi maka, duk abunda na fada maka gaskiya na fada ciki babu sharri ko kashe ni zakayi sai dai ka kashe ni.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button