BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Yau sati guda kenan da faruwar al’amarin Wanda yayi dai-dai da kwanaki goma da afkuwar al’amarin Auran mu komai ya dai-dai ta, tun ranar da ya kira wayar Mimi na kashe ban kara kunnawa ba sai yau, sun kawo wuta na jona ta a chaji.
Mimi ta shigo dakin jikinta babu k’wari ta zube kan katifa.
Binta nayi da kallo. Nace”Mimi kinga yanda kika rame kuwa.”?
Shuru tayi min
Nace”Wallahi Ki yiwa kanki fada ni yanzu kin daina bani tausayi haushi kike bani wallahi, wai Amjadu shi kadai ne namiji a duniyar nan.”
Shiru dai tayi min bata ce min komai ba.
Tsaki naja na futa daga dakin.
Tun lokacin da ya kira wayar yaji an kashe bai Kara kira ba yasan Mimi baza ta kashe masa waya ba.
Tabbas Asma’u ce shiyasa bai kara kira ba.
Yana zaune gefan bed da wayar a hannunsa numbar ya kira sai yaji ta shiga har ta katse ba a dauka ba, kira ya kara yi a karo na biyu nan ma ta katse ba a dauka ba, a je wayar yayi hade da Jan tsaki a fili yace.” Mata masu aji kenan.” Mik’ewa yayi ya futa parlor.
Mimi na kwance a dakin lokacin da yake kiran wayar tarin da take ne ya hanata d’aukar wayar har ta katse.
Cikin wani irin mugun tari da galabaita ta mike zaune hade da dafe k’irjinta tana cigaba da tarin sosai wa
[11/8, 6:21 PM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
Mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.
45
Ni da Umma muka shigo dakin da sauri!
Mimi na durkushe ta rike k’irjinta tana ta tari.
Da sauri Umma taje ta rike ta ni kuma ns dauko ruwa hade da fasawa na dago kanta ina bata, k’arfin tarin ya hanata ta karb’i ruwan.
Umma tace”Maza kije ki dauko gishiri a kicin.
Cikin tashin hankali na nufi kicin din na dauko ledar gishiri
Umma ta dangwala a hannuta ta sanyawa Mimi a baki tana Dan bubbuga bayanta hade da yi mata sannu.
Mimi idonta ya rufe sosai take tari! Da haki tare da hawaye.
Ni da Umma duk mun shiga tashin hankali.
Nace”Wallahi Umma jiya da daddare haka ta dinga yi da kyar tayi bacci.”
Umma tace”Ikon Allah watak’ila busawar sanyin nan ne,.
Nace”Ina jin hakane ” cikin ikon Allah tarin ya lafa sai dai haki da take yi.
Umma ta rungume ta a jikinta tana yi mata sannu
Ya Aminu ne ya shigo dakin ya tsaya bakin kofa fuskarsa s daure yake tambayar menene?
Umma tace”Mimi ce babu Lafiya in anjima ka siyo mata maganin tare saboda dare.”
Wani irin kallo yake wa Mimi daga bisani kuma ya tab’e bakinsa Yace. ” Umma ki rabu dasu duk karya ne,nasan wannan’yar iskar ce take zugata.”
Umma ta bata fuska tare da fadin”bana son wannan halin naka Aminu ina ruwan Asma’u anan.?
Futa yayi daga dakin ransa a bace.
Nace”Umma shifa bazai taba ganewa ba tunda ya samu ya kubuta Mimi CE abun tausayi.’
Shiru Umma tayi min, sai da taga Mimi tayi bacci sannan ta gyara mata kwanciya ta futa daga dakin jikinta duk babu k’wari.
Kallon Mimi nake gwanin tausayi duk ta rame tayi Dan wuya k’irjinta sai sama yake yana kasa alamun tana jin jiki.
Jikina babu k’wari na kwanta kusa da ita ina tunani
Ringing din wayar naji wacce take jone a chaji na mike da sauri hade da dauka
Babu sauk’i a murya ta nayi sallama
Ajiyar zuciyarsa naji a hankali yace.” Ya kike mata masu aji.”!! Sama nayi da murya ta nace.” Ina nan kallo kamar tsumma a randa, amma kasan da cewar zuciyar da ka yaudara da sunan so kake azabtar da ita tana cikin gararin rayuwa tana cikin halin ha’ulai kullum bata da sukun hawayen idonta ya kasa daina zuba……. Katse ni yayi kafin in karasa magana ta yace.” Wannan wace irin banzar magana kike min kina yi kina daga murya kamar kina yi da sa’an ki, kiyi min magana yanda zan fahimci me kike nufi .”
Haushi maganar shi ta bani saboda haka nace “Da Hausa nake maka magana ba da harshe nasara ba, nace” D’aya zuciyar daka yaudara tana cikin halin ha’ulai da damuwa saboda haka in ta shiga mugun hali to kai ne sila.”
Lokaci guda ya fahimci inda maganar ta ta dosa.
Babu ya bo babu fallasa yace.” Bani Momyna mu gaisa. “
A hasale nace”Ya ina yi maka magana daban kana yi min wata maganar, Mimi dai na bacci Wanda muka samu ya dauke ta da kyar don haka bazan tashe ta.”
Na k’arashe maganar tawa a kufule!
Wannan karon akwai sassauci a muryarsa yace.” Nace kiyi min bayani dallah-dallah yanda zan fahimta ni har yanzu ban gane abunda kike nufi ba.”
Nace”Mimi na kwance babu lafiya tana jin jiki saboda sonka shine Abunda nake nufi. Ina jinsa yayi murmushi cikin nutsuwa yace.” To waye mai laifi tsakanin ni da ita da iyayen Ku.”?
Da sauri nace “Kar ka sake ka zage mu ko kafad’i bak’ar magana kan iyayen mu.”
‘Yar dariya naji Yayi yace.” ‘Yan matana kenan, dags magana zan zage iyayen Ku cewa nayi waye mai laifi sai ki bani amsa ta.”
A fusace! Nace “Kai kasani.”
Yace.”OK naji bani Momyna muyi magana. “
“Kasan Allah bazan tashe ta ba wai me ma zaka fada mata ne bayan ka yaudare ta.”
‘Yar dariya yayi tare da fadin”Ina ruwan ki? Ke dai nace ki bani ita.” Shiru yayi sai kuma ya cigaba da cewa”Kina maganar na yaudare ta, nifa ita nace s kawo wa kud’in aure akayi mistake aka kawo miki, bayan nan Kuma maganar Aminu ta futo, ai ni ne ma zan ce an yaudare ni an bani wacce bana ra’ayi.”
Tsaki! Naja na kashe wayar ganin yana nema ya Mai da mutane mahaukata.
Ganin magariba ta kusa ne yasa na tashi Mimi domin baccin magariba babu kyau.
Lokacin Ya Aminu har ya kawo magunguna dasu Lemo da ayaba sai kai wa yake yana kawo wa, in muka hada ido ya buga min harara.
Muna idar da sallah na sanya Mimi a gaba taci abunci sannan na bata magunguna sai ta kwanta.
Nida Umma muna addu’ar Allah yasa kar tarin ya kara sark’e ta.
K’arfe Tara dai-dai naji ringing waya tsaki nayi Dan nasan wanene. Dauka nayi hade da sallama ba tare da ya amsa min ba yace.” Ki futo yanzu ina jiran ki.”
Ya kashe wayarsa.
Umma na kalla naga tana kallona nasan wayar handsfree ne taji komai
Tace “Ki tashi kije su manya mutane basa son jira.”
Nace”Umma wane irin zance ne wannan k’arfe Tara na dare.”
Umma tace”Sai kinyi surutun dai ko ki tashi kije Kuma kar ki sake ki futa da wannan kayan na jikin ki, masu kaurin hayak’i Dan dare yayi ma da sai kinyi wanka, ki gyara fuskar ki duk ki goge wannan maikon na fuskar ki, don nasan bs hankaline dake ba sai ki futa haka.
Mik’ewa nayi na shiga dakinmu wallahi dai dai Umma tace in sanja kaya amma da bazan sanja ba, material dinmu na anko na dauko na tusa a cikina ina nishi na fesa turare na me saukin kudi goge fuska ta kawai nayi da abun goge hoda na yafa mayafi karami. Takalmi plate na sanya a kafata na futo
Umma ta bini da kallo cikin zuciyar ta tana tunanin kayan jikina domin sun futo da sassan jikina,
Shiru kawai tayi nace”Umma na tafi.”
“To ki nutsu dai banda kaifin harshe nasan halin ki.”
Raina babu dad’i na futa daga gidan ina mamakin kallon da Mimi take Min tunda taga na futo.
Dake dare ne kuma babu wuta a gari yasa bansha kallon gurin Samarin layinmu ba.
Na karasa har inda motar tasa take fake.
Sabuwar mota ce yazo da ita, fara tas! Daga yau ya fara shigar ta sai walwali take motar tayi kyau kuma daga ni zata ja kudi sosai.
Cikin zuciyata nace”Kaji dadinka yanda ka samu duniya Allah ya baka lahira.”
Dake motar bata da duhu yana hangota sosai yake kallonta har ta k’araso ya bude motar tare da fadin”Bisimillah..” Kin shiga nayi na jinga jikin motar tare da fadin”Yau kam bazan shiga motar ka ba, domin bansan inda zaka kaini ba, in ka damu ka futo waje sai ka fada min abunda ya kawo ka.”