BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Kai tsaye!! Asibitin zana d’an a dai-dai ta ya sauke mu, Aminu ya sallame shi mu kuma muka taitayi Mimi muka shiga da ita ciki.
Har yanzu tarin take idanunta a rufe gaban rigarta duk ya b’aci da jini
Wani ma’aikacin gurin ne ya k’araso gurunmu da sauri da wani keke dama mun San ka’idar asubitin Mimi muka Dora kan keken ya ja ta da sauri ya shiga ciki da ita.
Tsayuwa muka yi bakin kofa duk jikinmu a sanyaye.
Umma tace”WANNAN kukan da kike bashi ne zai bata lafiya ba, addu’a zakiyi mata kawai.”
Nace”Umma Mimi na bani tausayi haka kurrum zata jawo mana abunda baza mu iya ba.”
Tace”Itama ba ita ta dorawa kanta ba Allah ne saboda haka sai dai mu bar masa.
Yaya Aminu kuwa kai wa yake yana kawowa a filin asibitin idan ka kalli fuskarsa sai ka rantse da bai taba dariya ba tunda uwarshi ta haife shi, shi a ganinsa zuwan guy gidan ne ya dawo da Mimi ciwon ta sabo ta inda har ya tsananta ta fara zubar fa jini dole ya mike tsaye a kan al’amarin domin yana ganin Ana so ayi masa tsakiyar da babu ruwa wani irin haushin guy yake ji da tsanar sa a cikin zuciyarsa
K’arfe goma saura sai ga aunt Hauwa ta shigo asubitin hankalinta a tashe take tambayar abunda ya sami Mimi Umma ta dinga fada mata tun farkon al’amarin
Jama’ar gidansu Motar Babansu Munnu ce ta shigo asubitin Aminu ya karasa da sauri ya bude masa motar
Ya futo tare da Ummansu Munnu da ita Munnu duk babu nutsuwa a tartare dasu.
Su k’araso kusa da mu suna gaisawa da Umma jiki duk babu nutsuwa
Yace.” Ina Aishatu take.” ? Dake da haka yake kiranta
Umma tace.” Tana ciki tun d’azu dector yana dubata.”
Jin Gina yayi jikin bango yana sauke ajiyar zuciya Mahaifin yarinyar ya tuno da yanda yake kaunarta da irin amanar da ya bashi kafin ya tafi Wanda har yanzu ba a San a wace duniyar yake ba, tun bayan rasuwar mahaifiyar Mimi din yaji duniyar ta isheshi ya hada ina sa ina sa, yayi sallama da ‘yan cewar ya tafi Neman kudi tunda ga ranar har yanzu basu sake ganinsa ba amma labari na zuwan musu cewar yana cikin koshin Lafiya, kuma bashi da zance dai na d’iyarsa Aishatu.
[11/10, 6:49 AM] Binta U Abbale: Umma da Ummansu Munna zancan suke yi cikin jimami ni da Munnu kuwa babu abunda muke yi sai aukin kuka
Kusan awar Mimi daya a ciki sannan wata narse ta futo tace”Waye mahaifin yarinyar nan da aka wo ta yanzu emergency. ” Kawu yace.” Ganinan.” Juyawa tayi tana fadin”Muje dector yana son ganinka “.
Dukaninmu sai mukaji kamar mu bi Kawu muji me dector zai ce masa.
Kawu da dector ne a ofis a hankali Dr ya cire farin gilashin dake idonsa ya kalli Kawu suka gaisa a mutumce yace.” Kaine mahaifin yarinyar nan ko.”?
Jiki a sanyaye Kawu yace.” Nine Dr Allah yasa naji alkairi.”
Dr ya gyada kansa tare da fadin ” I’m sorry to say yarinyar ka tana cikin garari rayuwa domun zuciyar ta ta Riga ta tab’u sakamakon tunani da damuwa da ta sanya a ranta bayan haka kuma da akwai a Abunda take mutukar so Wanda aka hanata shi shine mussababbin ciwon nata idan ba ‘ayi gaggawar kwantar mata da hankalin ba, to ana iya rasa ta a ko wane lokaci.”
Kawu ya share zufa da take tsatstsafo masa a goshi yace.” Dr yanzu wane irin taimako za’ayi mana.”?
Dr ya gyada kansa cikin nazari yace.” Taimakon da zan fara yi shine, kuje gida Ku rarrasheta sosai Ku lallame ta tayi kokarin fada muku abunda take so Wanda ta sanya a ranta ya dame ta, idan kun San abun to sai kuyi gaggawar bata shi domin samun zaman lafiya da d’orewar lafiyar ta, bayan haka kuma zan d’aura ta a kan magani insha Allahu mutukar aka bi doka zata samu lafiya, yanzu dai mun dakatar da zubar jinin insha allahu babu matsala.”
Kawu yace.” Insha Allahu komai zai zo cikin sauk’i zamu bi doka zamu kuma zauna da yarinyar domin mu tuntube ta muji meye Matsalar.
Dr ya gyda kansa tare da fadin”all right.” rubuce-rubece yayi jikin wata takarda ya mik’a masa tare da fadin idan ka futa zaka ga pharmacy sai ka shiga ka siyo wad’annan magungunan insha Allahu, amma ba yau zamu sallame ta ba sai zuwa gobe dole zamu ga dai-dai tuwar numffashinta.”
Kawu ya karb’i takardar da sauri ya futa.
Yana futowa muka mike da sauri dukaninmu tambayar sa muke jikin Mimi
“Da sauk’i yake cewa kawai ya nufi dakin magani Aminu ya bishi a baya.
Ofis din Dr suka nufa har Aminu Dr Ya kalli Aminu tare da Kawu yace.” Wannan fa.”?
Kawu yace.” Shine Wanda zai aure ta.” Dr yace.” Zauna muyi magana da Kai. “
Aminu ya zauna kan kujera jikinsa sanyi k’alau!
Dr yace.” Kaine kafi kusanci da sosai Kaine zaka fi sanin abunda yake damunta domin sai ta fada maka abunda yake damunta bata fadawa Iyayenta ba, saboda haka Kayi kokarin rarrashinta ta Sanar da kai meye matsalarta domin magance ta kada ka rasa kyakyawar matarka Cikin lokaci kankani.”Ya Aminu yayi shiru yana sauraran Dr da abunda yake fada
Ba sai yayi masa dogon sharhi ba, yasan kome ye yake damun Mimi bai wuce soyayyar Amjadu ba, Wanda yake ganin a kan ya sadaukar masa da ita gwara Mimi ta mutu in yaso kowa ma yayi asara.
Shiru kawai yayi har Dr ya gama maganar shi suka mike da niyyar futa Aminu ya tsaya tare da fadin” Dr babu halin ganinta a yanzu.”? Dr ya gyda kansa tare da fadin” ta samu bacci yanzu sai dai gobe insha Allahu da safe sai Ku shiga Ku ganta kafin a sallame Ku.”
Jiki babu k’wari ya futa daga ofis din.
Fuskarsa na kalla naga yayi kucin-kicin gabana ya fad’i nayi saurin kallon Fuskar Kawu nan ma naga babu sauk’i tuni kukana ya tsananta nace”Ku fada mana ko menene k’afafun Babansu Munnu na rike ina kuka.
Ummansu Munnu ta janye ni tana rarrashinna ni a lokacin sai nake ganin kamar zasu ce Mimi ta mutu ne Sabuda yanda muka kawo ta a sibitin ta futa daga hayyacin ta.
Can gefe guda suka tsaya suna magana. Kawu yace.” Aminu ni a iya fahimta ta nafi tunanin Mimi ta sanya soyayyar wannan Yaro da zai auri Asma’u a cikin ranta ne Wanda yake kokarin haifar mata da WANNAN gagarumar Matsalar shine Abunda nake tunani.”
Aminu ya gyara tsayuwarsa babu sassauci a muryarsa yace.” Dama ni tun kafin muzo gaban likita ya fada mana meye na gane komai, a gaskiya Baba babu mahalukin da zan iya barwa Mimi domin nima idan nayi haka zan iya shiga cikin tashin hankali watak’ila ma nawa yafi nata tunda kowa ya shaida nafi sonta ita bata sona saboda haka ni ina gani kawai daga nan zuwa jini a d’aura mana aure da ita ba sai an jira lokacin da aka sanya ba, idan taji labarin haka nasan dole zata hak’ura ta fawwala Allah kasan dama ance kiyyayyar ‘ya mace bata tasiri ina ganin Mimi zata hak’ura ta zauna dani.”!
Kawu ya gyada kansa yana Nazarin maganar Aminu Yaro Yaro ne, murmushi yayi yace.” Aminu kenan, kamar ka manta abunda Dr yace akan Aishatu, Jin labarin d’aurin auranku zai iya sanyawa zucuyarta ta buga gaba daya ta mutu lokaci guda, kaga kuwa wannan sha’awar taka ba abun dubawa bace.”
Aminu ranshi ya b’aci da jin abunda Kawu yake fada murysrshi a kaurare yace.” Kai ya kake ganin za’ayi.”
Kawu ya kalleshi cike da mamaki jin yana yi masa magana kazar-kazar babu Wani ladabi.
Yace.” Abunda za’ayi shine mu samawa Aishatu abunda take so domun samun ta da tabbatuwar lafiyar ta.
Aminu ya watsa masa wani kallo tare da fadin”Kawu in na fahimce ka anan shine kana so kace min in hak’ura da Mimi in yaso Ku bats Wanda take so kome.”?