BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Kai tsaye….. Kawu yace.” Shine abunda nake Nufi.”
Aminu ya guda kansa yana murmushi me ciwo yace.” Impossible, bazai tab’a yiwu wa ba Kawu Mimi ‘yar kace nima inda kara d’an ka ne nasan baza ka bawa Mimi bare ba gani a zaune, ina so saboda haka yanda aka karb’i kud’in aure na da Mimi to babu mahalukin da ya Isa ya hana tabbatuwar auramu idan ba Wanda ya hallice mu ba.”
Cike da d’umbun mamaki Kawu yake kallon Aminu ganin yanda yake wani irin huci!! Yace.” Aminu ka fahimce ni mana ba wai ina k’in ka ban……… Kafin ya karasa Aminu ya daga masa hannu a fusace.!!! Yace.” Kawu ga magana nan ta futo kanunamin bakai ka haife ni b…. Cike da b’acin rai Kawu yace.” Rashin kunya zakayi min Aminu. “
Daga kafad’a yayi tare da fadin “Babu maganar rashin kunya anan Kawu gaskiya ce ni nayi rantsuwar babu Wanda ya Isa ya hanani auran Mimi.”

Ganin tsageran cin da Aminu yake masa ne yasa ya fusata shima yace.” Aminu indai nine waliyin Aishatu to baza ka aure ta ba.”
Aikuwa sai ya ingiza Aminu ta inda ya shiga sirfa masa rashin kunya wanda ya jawo hankalimu Kansu dukanimu mu k’araso gurin tare da tambayar ba’asi
Abunda Aminu yake yi yayi bala’in konawa Umma rai ta cire hannunta ta zabga masa mari cikin tsawa tace”Na kara jin bakinka a gurinan Aminu sai na tsine maka, a tunanin ka wannan tsagerancin da rashin kunyar da kake yi shine zai sanya a baka auran Mimi ko meye.”?

Kawu yace.” Kyaleshi ya zage ni son ransa lokacin sa ne.”
Wuce mu yayi tafi can bakin get ya zauna tare da masu gadi

Fada sosai Umma take wa Aminu Tace” Haka ake soyayya da hauka Aminu ka futo da son zuciyarka a fili kana ganin mawuyacin halin da yarinyar nan take ciki shine zakaje gwara ta mutu a kan ka janye kudirin ka a kanta, me yasa ita lokacin da ka fad’i har ka kwanta a asibiti tace”Zata aure ka alhalin ga Wanda zuciyar ta take so Mimi yarinya ce me ladabi da gudun b’acin rain wani ta so ta faranta maka ta faran wa zuciyata ba tare da ta damu da nata farin cikin ba, shine yanzu tana cikin halin rai da rayuwa kake mummunan magana a kanta Aminu wannan ba soyayya bace.”!!!!
Umma ta karasa maganar ta tana haki! Kana ganinta zaka fahimci tana cikin tsananin b’acin rai da damuwa
Cikin kuka na futar hayyaci nace”Wallahi tallahi Umma mutukar Ya Aminu bai janye kudirinsa ba nima bazan aure shi ba, sai dai mu zauna a haka, kawai a aura mata Wanda zuciyarta take so ta huta da wannan azabar da take sha.”
Umma tace.” Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Mimi bata da Miji sai Amjadu dole a bawa zuciyarta hakuri abata abunda take so.”
Ya Aminu ya kalleni ya kalli Umma zuciyarsa nayi masa wani irin ciwo yace.” Umma don bani da kudi bani da aikin yi bani da mota bani da babur bani da keken hawa kana bani da kudi a banki kuke mun haka,? Meye laifi na meye? Aibuna anan Zan kula da Mimi zan tsare mutumcin ta zan sanya ta farin ciki! Umma kar Ku kware min baya akan Mimi Ku duba halin da zan shiga a kanta soyayyar ta tana iya kashe ni!!!!! Umma ni danki ne baza ki so wani bayan ni ba, Umma ki dube ni da idanun rahama!! Ki tuna so da kaunar da kike min Umma ki bani Mimi domin itace farin cikin rayuwata.”!!!!!!!! Ya k’arashe maganar sa hawaye na zubowa daga idanunsa

Umma ta zube a gurin Tare da dafe k’irjinta tana salati aunt Hauwa da Ummansu Munnu suka rike ta hawaye ne ya fara zirarawo daga idanunta muryarta na rawa tace”Ya Allah ka ije mun wannan masifa da ta tun karo ni, Allah ka sanyaya min kasa kawo karshen wannan badak’ala!! Sai hawaye sharrrrrrrr-sharrrrrrrr suka fara zuba a kuncinta.
Duk taurin zuciya irin ta aunt Hauwa hawaye ta fara sharewa ganin Umma tana kuka abunda zai sanya Umma kuka ba Karami bane hakuri kurum suke bata

Ni ko da sauri na bar gurin bayan na warce wayar Munnu dake tsaye, wani d’an korido na nufa dake Cikin asibitin na fara Neman numbar sa, sai da tayi ringing sai uku ba a dauka ba,

Sai ana hudu ne ya dauka muryarsa da yanayin bacci yayi sallamsa da sauri nace.” Kanwa ta kar tsami! Kwarna fi ya kwanta. “!!!! Jin muryar yarinyar ya sashi mik’ewa zaune da sauri hade da yaye blanket din jikinshi na ci gaba da cewa ” Yanzu haka muna babban asibiti na zana Mimi a kwance rai a hannun Allah bayan tafiyar ka, jini ya tsinke mata ta baki ta hanci!!!! Ta galabaita mutuka duk ta dalilin ka!!! Ina kara fada maka duk abunda ya same ta Kaine sila Kaine! Mujaza!! Mahaifiyar mu ta zubar da hawaye akan haka, mun zubar da hawaye a kan haka, duk wani mai imani ya kalli Halin da Mimi ta shiga a yanzu sai ya tausaya mata, insha Allahu duk wani sharrinka sai ya koma kanka ka cuce mu, ka yaudare mu, Ka azabatar da zuciyar Mimi akan sonka kullum kana fada cewar zaka aure ta, alhalin karya kake!!! Wallahi mutukar ka bari Mimi ta mutu baka yi Wani Abu akai ba nima sai na kashe ka.”!!!!!!!!!!! Kamar wata mahaukaciya haka na k’arashe maganar….. Wata irin zufa ce ta keto masa duk da cewar akwai AC a dakin Muryarshi sanyi k’alau yace.” Asma’u.!!! ” saurin kashe wayar nayi na zube a gurin hade da fashewa da kuka mai cin rai.

Mik’ewa yayi da sauri ya duro daga bed din toilet ya nufa ya dauro alwala ya futo yana kallon agogo bango uku shaura na dare,
Jallabiya ce a jikinsa sai garan wando ya dauki wata rigar sanyi sa mai hula ya sanya kai a gogonsa ya d’aura ya dauki key ya futa da sauri.

Rbow suka ji ana kokarin tada mota hankali a tashe suka futo daga gurinsu, suna tambayar sa yace.” Su koma kawai shima yanzu zai dawo jikinsu duk babu k’wari suka tsaya a gurin har sai da suka ga futar shi Daga gidan.

Kai tsaye……Asibitin Zana ya nufa zuciyarsa kwata-kwata babu dad’i abun yana mutukar bashi mamaki shi dai yasan babu wata Kalmar so da ya tab’a fadawa Mimi wacce har suke zargin sa da ya yaudara ta, maganar auran ta kuwa ya fada ne saboda son da take masa gami da ganin yanda suka shak’u da Asma’u yana ganin ko ya aure su su biyu ba za a samu matsala ba, yanayin dabi’un Mimi da nutsuwar ta gami da kunyar ta suna bashi sha’awa amma zallah so gangariya babu Wanda yake wa sai Asma’u duk cikin ‘yan matansa babu wacce ta samu wannan matsayin kamar ta hak’ika Asma tana da babban matsayi a zuciyarsa.

Da wannan tunane-tunanen ya Isa asubitin, Madi suka bude masa kofar ya shigo cikin sauri suka biyo motar da gudu yana parking suka bude masa kofa suna yi masa barka da zuwa.
Amsa musu yayi babu yabo babu fallasa, ya wuce ciki.
Suka tsaya suna binshi da kallo tare da tunani wane dalili ne ya kawo shi asibitin ? Suna zargin yau ya zagayo su ne duba marasa lafiya da. da bada tallafi kamar yanda ya saba, murna suke sosai yau zasu cika aljihunansu.

Wayarsa ya futo da ita yana laluben numbar da ta kira shi da ita yanzu….

10/November/2019
[11/11, 9:19 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

48

Ringing d’in wayar ne ya dawo dani cikin hankalina wayar na duba sai naga numbar sa, da kamar kar in dauka wata zuciyar tace”Dauki kiji me zai ce miki.
Jin alamun ta daga wayar ne yasa yace.” Gani cikin hospital din ki futo kiyi min jagora har inda kuke.”
Bai saurari Abunda zata ce ba ya kashe wayar sa.
Futowa nayi daga gurin da nake.
Har yanzu suna tsaye kan Umma sun yi mata rumfa Aminu sai fiffita yake mata.
Aunt Hauwa ta kalle ni tare da fadin”Da ina kika shiga tun d’azu. “
Cikin wayan cewa nace”Futsari naje nayi.”
Raba ido nake yi a gurin ko Allah zai sanya I n hango shi
Da yanayin tafiyar shi na gane shi.
Shiru nayi har ya k’araso gurin.
Cike da mamaki suke kallonsa.
Ya mik’awa Aminu Hannu su gaisa.
Da kyar ya mik’a masa nasa hannun kamar yanda yayi masa jiya.
Umma ya kalla yace.” Umma Ashe bayan tafiya ta jiki ya rike CE.”
Umma ta gyara zamanta hade da gyara mayafin ta tace”Wallahi kuwa aman jini take sosai.”
Gaban shi ya fadin jin abunda Umma tace, Yace.” Bari in ga dector babu matsala insha Allahu komai zai zo da sauki.”
Binsa mukayi da kallo har ya shige ciki abun mamaki babu Wanda ya hana shi shiga cikin ma’aikatan sai ma da d’a gyara masa hanyar wuce da suka yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button