BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Nace.” Mimi duk abunda kikayi NIYYA ki bashi domin ki faranta masa kuma kinyi dabara hakan zai k’ara jawo hankalinsa gare ki.” Tace.” Me zan bashi yanzu.”? Dariya na sanya hade da fad’in “Idan baki da abunda zaki bashi in yazo to ki bashi labari mai dad’i da wannan sanyayyar muryar taki.” Dariya tayi hade da bani hannu muka tafa, haka dai na dinga biye wa Mimi da duk abunda zata ce min akan Amjadu kuma bana bata shawarar banza.
K’arfe shida shaura kira ya shigo wayar tata lokacin tana band’aki tana wanka, Kin dauka nayi don na duba naga shine, motsin ta naji bakin rijiya nace”Mimi yi sauri kizo ana kiran waya. ” aikuwa sai gata ta shigo da sauri hannunta na digar ruwa ta karb’i wayar daga hannuna. Kallo na bita dashi. Wata irin murya da ban Santa da ita ba naji tace.” Hello.” Daga bashi bangaran naji muryar shi sama-sama yace.”Momyna kuna ina ina ta kiran waya kusan sau biyar babu wacce ta dauka a cikin Ku.” Muryar ta a sanyaye tace.” Ni ina wanka ne.”
“Asma’u fah.”! Yafad’a babu sauki a muryar shi,kallonta tayi sai kuma naji tace.” Gatanan. ” yace.” Ok kina nufin kice min tana ganin kirana taki d’aukar wayar.”? Mimi shiru tayi taki bashi amsa. Shurun da Mimi tayi shi ya tabbatar masa da abunda yake zargi. Tsaki! Yaja yace.” Ok ki fad’awa granny gani Nazo ta futo mu tafi OK.” Kafin Mimi tace Wani Abu ya kashe wayarsa. Jikinta a sanyaye take kallona nima ita nake kallo nace”Dole ki koyi hakuri fa, kuma kiyi hakuri da halin shi tunda aure zakuyi .” zama tayi kusa dani tare da fadin”Wai sai ki dinga cewa aure zamuyi eh aure zamuyi har dake a ciki ai,ko” mik’ewa nayi ina dariya nace.” Har dani mana, ni ai farin cikin ki ne nawa kar ki damu dani.” Futa nayi daga dakin ba tare da na saurari abunda zata ce ba.”
Cikin sauri Mimi ta shirya ta futo tana ta zabga kamshi ina zaune kofar kicin ina gyara kayan miya na bita da kallo sakin fuskata nayi tare da fadin “Kinyi kyau sosai Mimi.” Mirmushi tayi ta shiga Rumfar inda naji grnnay tana sallama da Umma, suka futo a tare Umma sai godiya take mata, sun kuyar da kaina nayi kasa na cigaba da aikina har tazo kusa dani ta tsaya da sakskkiyar fuska tace.” To ke zan tafi naga sai wani b’uya kike yi ko tsorona kike ji tun kafin ki shigo kinga ‘yar Uwar ki ta saki jikinta mun saba da ita.”
Murmushi nayi nace.” Ki gaida gida mun gode.” ‘Yar dariya tayi tare da fad’in”Na ga alama gudun angon naki kike yi ‘yar uwarki tafi ki sonshi.” Ni dai ban ce komai ba har suka fuce ita da Mimi da aunty Hauwa har soro Umma ta raka ta sannan ta dawo cikin gidan.
Yana zaune cikin mota ya hango zuwan su, Mimi yake kallo tun daga nesa taci Uwar kwalliya abun ya bashi mamaki sosai, yarinyar Da jiya I Yanzu take kwance magashiyan rai a hannun Allah, amma dubi kamar ba ita ba, abunda bai sani ba shine tunda Mimi taji labarin auransu zai yi wu dashi da ita ta watsake tamkar bata tab’a cuta ba, har suka k’araso gurinsa yana mamakin wannan abu .
Murmushi mai k’ayatar wa take sakar masa, Wanda Sam hankalinsa baya kanta yana can gurin Granny wacce take kokarin shiga mota sai mita take masa, yace.” Idan zaman gidan ne bai ishe ki ba sai ki koma ai ban ce miki dole ba.” Tana daga cikin motar take fadin”Wallahi karshen zamana a wancan gidan yazo domin baza ka aje ni ba sai kace mayya ni daya gida kullum kana gidin matan ka, nima gidan naka Zan dawo .” dariya yasa yana kokarin futowa daga motar yace.” Sa ido ne zai kawo ki gidana bana Neman ki.” Bude motar yayi ya futa yana jinta tana surutai ya shareta
Fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Mimi yace.” Momyna jiki yayi kyau gashi har anyi min kwalliya mai kyau da burgewa.” Mimi ta rufe fuskarta cike da kunya, yace.” Kinyi kyau sosai zan so in ta kallon fuskar ki, sai dai Dole zan bar gurin nan saboda idon Jama’a ina fata babu wata matsala ko.”? Cike da shauki Mimi tace.” Babu wata matsala dama ji nayi zuciyata baza ta iya nutsuwa ba dole sai ta ganka.” Murmushi yayi hade da Sosa kansa yace.” Momyna kenan nagode sosai da wannan kaunar ina alfahari dake.”
Mimi ta dinga jin dad’i a zuciyarta yau gata ga masoyinta Amjadu Sam bata so yayi mata sallama ba, taso suyi ta tsayuwa a gurin tana kallon kyakyawar fuskar shi.
Sai dai motar tayi nisa har ta daina ganinta sannan ta bar gurin cike da nishadi.
Labarin auran Amjadu Young millionaire ya baza garin kano da ka bude redio zan can kenan Young millionaire zai yi aure a Sati biyu masu zuwa inda zai auri ‘yan gida daya ya da k’anwa jama’ar gari na mamakin wannan Abu, masu bin kwakwkwafi kuwa sai da suka bunkito ko su waye ‘yan matan da zai aura hade da bunkice ‘yayan wane mai kud’in ne ko kuma mai mulki a jahar kano da sauran garuruwa.
Abun mamaki surutun jama’ar gari sai ya karu wannan gayawa wannan ‘yan matan da Amjadu Young millionaire yake nema da aure ‘yayan talakawa ne tilis d’aya ubanta ma ba’asan inda yake ba tun tana jaririya ya gudu ya barta ana zargin ma ‘yar shege ce bayan yayi cikin ta ya gudu daga gari, ita kuma d’ayan ubanta ma’aikacin company ne na madara dake Sharada ya mutu bashi da ko kwabo bashi da famsho balle garatuti ya mutu bashi da gidan kansa,sai a company da yayi wa aiki ne suka bar mishi gidan da suka bashi a ro saboda iyalinsa, Duk ana zargin’yan matan da zai aura ‘yayan mace ne.” Duk cikin jarida ta gaskiya dokin k’arfe Amjadu ya karanta wannan labarin. Zufa ce kawai take keto masa ko ta Ina, wani irin kira ya kwalawa Rambo sai gashi ya shigo farlor da sauri. Jaridar ya mik’a masa muryar shi a sama yace.”Kuna ina haka ta faru. “!! ? Rambo ya karb’i Jaridar yana dubawa hannunshi sai rawa yake yi, shima abunda ya gani ya tsorata shi, yasan makiyan sa ne suka shirya wannan Abu domin su tozarta shi, Yace.” Sir ka kwantar da hankslinka wannan duk sharrin jama’a ne kar ka manta kana tare da mahassada ko su zasu aikata maka wannan Abu.”
Mik’ewa yayi yana kai wa da kawo wa a farlor yace.” Kaje ka tsaurara bunkice ka gano gaskiyar abun shin abunda na karanta jikin jaridar nan hakane Mimi Bata da uba shegiya ce kamar yanda suka fad’a shin hakane wannan gida dasu ke ciki na company ne kaje ka tsaurara bunkice ka gano wane company mahaifin Asma’u yayi a aiki a sharada.”
Rambo yace.” Insha Allahu Sir ka kwantar da hankalinka duk sharrine domin da d’aga maka hankali kuma a tozarta ka a don duniya. ” Wayar shi tayi kara Rambo ya mik’o masa da sauri, kunnenshi ya kara wayar a dake yace.” Salamu alaikum. ” Kawu Yunsu Ya amsa cike da tashin hankali yace.” Yaro mai halin manya na bugo ne in kwantar maka da hankali kan abunda jama’ar gari da kafafan yad’a labarai suke shela a kai, ina so in tabbatar maka da cewar mu ‘yar mu Asma’u tsarkakkiya ce da Ubanta kuma muna da nasaba me kyau duk fadin koki da cikarta babu Wanda bai san mahaifinmu Malam Sulaiman mai ishiriniya ba, idan kana so kattabar da haka ka sanya ayi maka bunkice.”” Muryar shi a sama yace.” Babu bunkice da zan sanya ayi min akan Asma’u na yadda da ita Dari bisa Dari, kokwantona yanzu akan Mimi yake shin da gaske ne mahaifin ta ya gudu ya barta ko kuwa.”?
Kawu Yunusa yace.” Hakane tun bayan haihuwar ta ya gud ….. Katse shi kafin ya karasa yace.” Tabbata kenan abunda nake zargi.” Kawu Yunusa har yayi niyyar cewa gaskiya ne sai kuma ya fasa tunowa da yayi da maganar Asma’u inda take fadin bata har indai Mimi bata aure shi ba itama baza ta aure shi ba, yayi saurin cewa.” Yarinyar ‘yar sunna ce sai dai ubanta ya hofintar da ita ne shine mahaifiyar Asma’u ta dauke ta ta raine ta.