BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Amjadu ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin”Yau saura kwana nawa d’aurin aure.”? Kawu yace.” Kwana shida ne.” Shiru na minti biyu sannan yace.” Yau muna laraba ko.”? Kawu yace.’k’warai kuwa” Yace. “Idan Allah ya kaimu jibi d’aurin aure insha Allahu Ku zauna cikin shiri daga yanzu a fara shiri duk wani Abu da ake bukata kayi min magana kar ka samu damuwa.
Kawu yaji wani irin sanyin dad’i ya shiga ransa yace.”Insha Allahu komai za a yi kamar yanda kake so Allah ya kara arziki da wadata.” Amjad yace.” Ameen suma Ameen ina so in zauna da Waliyin ita Mimi domin akwai wasu muhiman tambayoyi da zanyi mishi.” Kawu yace.” Ai babu damuwa yana aiki ne a babbar makarantar ta PCE nan kofar famfo.” Gyada kansa yayi yace.” Insha Allah zan same shi a ofis din.” Nan suka yi sallama da juna.

Wanka ya shiga a gurguje ya kimtsa jikinsa ya futo sai zabga kamshi yake kamar ko da yaushe , fuskar sa a daure ya futa, abun mamaki da daure kai can ya hango ‘yan jarida suna rigima da masu gadi gurin wai lallai sai sun shigo Estate din.”

Mota ya nufa zuciyarsa nayi masa suya wato yanzu za a sanya shi a bakin duniya kenan Saboda ana zargin zai auri Shegiya mata uba, shi yarinyar da suke maganar ta ba su San ba sonta yake ba, kaddara ce kawai auran su, da ita zasu sashi a duniya duk Wanda yayi masa tunon asiri nan bai kyauta masa ba.

Ganin shi ya futo yasa suka dinga kokawar shiga cike da b’acin rai yace.” Doh doh kayi kamar zaka bi takan ‘yan iska da mota.” Aikuwa Doh_ doh ya fafuri motar da guda! Lokaci guda suka watse amma duk da haka wasu daga cikinsu sai da suka dinga d’aukar motar tashi hoto masu vedio ma nayi kamar bala’i suka bi motar da gudu suna fadin”Yallab’ai me zaka ce a game da jita-jitar da jama’ar gari suke a kanka wai zaka auri shegiya Mara Uba shin hakane ko karya ne, Yallab’ai muna so mu ji ta bakin ka.”

Ko kallonsu bai yi ballanta su saka ran zai amsa musu motar ta b’acewa ganinsu. Sai da sukayi nisa sosai sannan yace.” Doh ka kaini makarantar FCE Yanzu.” Doh yace.” OK Sir. motar na shiga makarantar samari da ‘yan mata suka yi mata Caa! Da ido kasamcewar duk inda motar shi take an Santa saboda tambarin da yake bayanta. Doh.. Yayi parking inda aka tana da kana ya futo da sauri ya bude masa kofar motar.

A hankali yace.” Ka shiga ciki makarantar ka bunkita min ofis din Muktar Inuwa Gyaranya.” Shine ai nihin sunan Kawun Mimi wato Baban su Munnu kenan. Nan da nan doh-doh ya tafi cika umarnin da aka bashi


Muna cikin tsananin tashin hankali da rud’u tun lokacin da Umma taji labarin abunda jama’ar gari suke fada a kan Mimi take kuka ta tana fadin”Yarinyar sinna ake shigantawa ni Mariya Innalillahi kuka take sosai tun muna daurewa har muma muka fara taya ta, Ya Aminu ya shigo gidan shima ranshi a bace domin yaga sai Wani irin kallo jama’ar gari suke masa sai kace Wanda yayi sata ko maita Mimi ya kalle ranshi a mutukar bace yace.” Kukan karya kike yi Mimi, ko kin dauka auran Wanda ya shahara a duniya wasa ne? Kin dauka in kin auri Young millionaire zaki samu irin kwanciyar hankalin da kike so, to bari kiji auran irin su Sai kayi ta fuskantar kalubale kinga ishara yanzu da Uwar ki da ubanki jama’ar gari suna kiran ki da shegiya, tom me zakice game da wannan zargin da suke miki, ku sani ga ‘yan jarida can a waje suna kokarin shigowa cikin gidan nan nine na hana su na rufe kofar gidan da sakata. “

Mimi kukan ta ya tsananta ta inda ta fara karkarwa tari ya sark’e ta har tana kokarin kifawa k’irjinta ta rike tam da hannu biyu sai tari take ga hawaye na zuba daga idonta. Hankali a tashe nayi kanta ina kuka wurjajan ina ji kamar in tashi in gaggaura Aminu mari, murya ta a sama nace.” Ya Aminu ka k’yaleta mana baka ga tari ya sark’e ta ba.”!!!! Ko kallona baiyi ba ya futa daga rumfar a fusace,!! Ni da Umma muka rike ta sosai muna dukan bayan ta duk mun gigice.!

Wata irin zufa ce take keto wa Baban su Munnu bayan ya gama sauran maganar da Amjadu yaje masa da ita, to son ya San meye dalilin da yasa Uban Mimi ya gudu ya barta ko zancan da jama’ar gari suke yi gaskiya ne.”. Hankali a tashe Baban su Munnu ya fara magana kamar haka.
“Hak’ika Aishatu yar halak ce mahaifin ta Dan uwana ne cikin mu daya, mu ‘yan kano ne gaba da baya yan Asalin unguwar Gyaranya dake k’aramar hukumar Dala, tun bayan rasuwar Matar shi wato Aisha mahaifiyar Mimi kenan ya ji zaman garin ya ishe shi bayan sadakar ar’abain ya tafi Neman kudi a cewar sa, yau shekara goma sha shida kenan, ban sanya shi a idona ba sai dai labarin sa yana zuwar mana sa’i da lokaci kuma kullum yar shi tana ranshi yana yi mata ake akai akai, Mariya yar mahaifiyar ta Itace ta dauke ta shayar da ita nonota lokacin tana goyon ‘yar ta Asma’u sai ta had’a ta shayar dasu tare babu abunda zamu ce da Mariya domin ta cika jajurtacciyar macace. Wannan shine ainihin abunda yake faruwa.” Kawu ya k’arashe maganar sa yana goge zufa.!!

Shima Nashi b’angaran wani irin faragaba da fad’uwar gaba ne ya riske shi lokacin da ya gama jin abunda Babansu munnu yake fada, hannunshi na rawa ya Ciro hankici daga aljuhunsa ya fara tsane gumin dake saman goshinsa, minti goma babu Wanda yayi magana a cikinsu, da kyar ya bude baki yace.” Kana so ka fada mun cewar Asma’u da Mimi sun sha nono d’aya kenan.”? Kawun su Munnu ya gyada kansa tare da fadin”k’warai kuwa.”
Amjad ya sauke gwaron numffashi yace.” Aurena da Mimi ya haramta idan Asma’u zan aura idan kuma Mimi zan aura aurena da Asma’u ya haramta.!!!!!!! Babansu Munnu ya tsinci kansa da shiga rud’u da fargaba Sam!! Ya manta da wannan k’aulin Innalillahi wa innailahi raji’un

K’ak’a k’ara k’ak’a tsara

13/November/2019
[11/14, 7:52 PM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

51

Cikin yanayin damuwa Babansu Munnu yace.” Wannan abu akwai rikita-rikita a cikinsa akwai daure kai, tunda ake wannan sabgar ban tab’a tunanin wannan alak’ar ba, Babbar magana ce wannan, tsarin na addini islama babu aure a tsakanin mutum biyu sai dai ka dauki daya ka bar d’aya, sun Riga sun tsotsi nono d’aya mutukar ba d’aya ce ta mutu a cikinsu ba, to baka da damar auran ‘yar uwarta har abada, amma kasan ko wane ijma’in malamai da nasu k’aulin, Allah ne dai masani.”
Babansu Munnu ya kare maganar sa cike da tararrabi yanzu idan Amjadu ya zab’i Asma’u ya bar Mimi wand irin hali zata shiga? Watak’ila ma karshen rayuwar ta yazo.”

Amjadu jikinsa yayi wani irin sanyi tunda yake bai tab’a shiga rud’u da fargaba ba irin na yau, ko mutuwar iyayen sa bai shiga wannan halin ba duk da cewar mutuwar ta girgiza shi sosai wannan yasan dole ce ko wa sai ya d’and’ane ta.

Kusan mintuna goma babu Wanda yayi magana a tsakaninsu dukaninsu suna tunanin ya za’ayi su warware Matsalar, Mik’ewa yayi hade da mik’awa Baban su Munnu hannu sukayi sallama, ba tare da yace masa komai ba ya futa daga ofis din.

Yana shiga mota ya fara kiran wayar Kawu Yunusa buga daya ya dauka hade da yin sallama kamar zai masa sujjada, saboda kwantar da murya. Yace."Aure tsakanina da Mimi ya haramta saboda sun sha nono d'aya da Asma'u tun farko Asma'u ce zab'i na saboda haka na janye Neman auran Mimi ina rokon Allah ya fe min kuskurana, ita kuma Allah ya bata miji nagari."


Kawu Yunusa ya share gumin fuskarsa shima sai yanzu ya tuna da wannan alak'ar mamaki yake sosai me ya hana su tuno da haka sai da magana tayi nisa, idan hakane Ashe Aminu duk abunda yake akan yarinyr babu aure a tsakanin su."

“Kawu Yunusa yayi gyaran murya tare da fad’in “Idan ban da ka tsaurara bunkice a kan al’amarin da sai dai muyi ta tafiya a haka domun idanun mu sun rufe akan al’amarin ta inda muka mance da wannan alak’ar saboda haka yanzu zab’i na gare ka, Kaine zaka zab’awa kan ka matar aure cikin su biyun.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button