BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

 Bacci ne ya soma fizgar sa kad'an-kad'an yaji ringing din wayar sa, cikin kunnen sa, dalili airpic din dake manne a kunnen sa, a hankali ya dauki wayar dake saman k'irjinsa yana dubawa. Mik'ewa yayi da sauri ganin numbar da ta kirashi.

Ba tare da ya cire airpix din ba ya latsa wayar tare da fadin”Salamu alaikum.” Murya Asma’u yaji sama-sama ta amsa da wa’alaikasalm. ” gabansa ya fad’i sosai lumshe idonsa yayi hade da cije leb’anshi fargabar abunda zaiji daga bakin ta yake.”

Kai tsaye yaji tace”Barka da yamma.” A hankali yace.” Barka ya kike Husnah.”!!
“Lafiya.’! Tafad’a babu wani sassauci ta cigaba da cewa ” Yanzu Kawu Yunusa ya bar gidanmu bayan ya Sanar damu sak’on ka.”

“Owk” shine abunda Yace yaja bakinsa yayi shiru yana sauraran ta. Ta cigaba da cewa” Allah ya kadddara ni ba matar ka bace, ina yi maka fatan alkairi idan son da kake min na gaskiya ne, to a madadina da aka zab’a akan Mimi ni na hak’ura ka mai da maganar auranmu kan ‘yar Uwata domin ceto rayuwar ta.”.

Wani irin gumi ne yake tsayaya daga jikinsa bakinsa yayi wani irin daci ya soma Jin zazzab’i na shigar shi, jin abunda take cewa, amma da yake NAMIJIN duniya ne, muryarsa a tsaye yace.” Meye hujjar ki ta fad’ar haka, shin nine bakya so ko kuma akwai wata manufa taki.”? Cike da dakiyar zuciya tace.” Eh duk biyun ne bawai bana sonka ba ne, Mimi tafi ni sonka bayan haka kuma kayi mata alk’awarin aure ka yaudare ta da kalaman ka hade da zakin bakin ka, kayi kwance kwance ka lasa mata Zuma a baki daga baya kuma kace ka fasa auran ta, shin baka tunanin halin da zata shifa ko kuma kana so mu rasa ta, son da Mimi take maka zai iya kashe ta.”!

Wani irin yammm!! Yake ji a jikinsa tsigar jikinsa tana Mik’ewa jin abunda yarinyar take fada, a kausashe yace.” Shine Hujjar ki.”! ?
“Eh shine Hujja ta.” Ta fada babu wasa a cikin maganar ta.”

Ajiyar zuciya ya sauke minti uku tsakani yace.”Shikkenan tunda haka kika Zab’a mana ni dake muyi rayuwa na karb’i Mimi a matsayin mata kamar yanda kika bukata, Allah ya sa haka shi yafi alkairi.”.
Da sauri nace”Ameen auran Mimi alkairi ne a gare ka insha Allahu.” Kashe wayarsa yayi ba tare da yace min komai ba.

Lokacin naji damuwar da ke cikin raina ta ragu burina kawai inga Mimi gidan Amjadu mu huta da wannan masifar, duk abunda ya faru tsakanina dashi na Sanar da Umma ita ma taji dadin yanda ya amunce lokaci guda.

Hannusa ya sanya ya dafe kansa dashi lokaci guda kansa ya shiga Sara masa wani irin bakin ciki da damuwa sun taro sun tsaya masa a mak’ogwaro da kyar yake had’iyar yau!! Sosai yake jin bakin ciki da takaicin zafafen maganganun da yarinyar ta watsa masa lallai inda ranka kasha kallo wai shine yau ‘ya mace take furta cewa bata son sa baki da baki yarinyar ma k’arama irin Asma’u.

14/November/2019
[11/15, 10:20 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

52

Yana zaune a gurin hannunsa saman goshin sa granny da Iyami me aikinta suka shigo parlor Iyami ta nufi daining tana gyara gurin, ita kuma Granny ta k’araso kusa dashi da sauri ganin yanda yake cije bakinsa yasa ta dafa kafadar sa, tare da fadin”Kar ka sake ka sanya damuwa cikin zuciyar ka har ta haifar maka da wani ciwon ni dai a ra’ayi na nafi so ka auri ‘yar bak’ar yarinyar a cikin su biyun naga kamar tana da kunya da hankali.” Ta k’arashe maganar ta a tausashe.

Da kyar ya iya bude bakinsa yace.” Tace bata sona Granny. ” Zama tayi kusa dashi cike da mamaki tace” Amma Wannan anyi ‘yar banza ta samu namiji me zafi da kwarjini kamar tace bata so, in banda ma Matsalar ka nasan ko mata dozin aka aje maka zaka iya dasu, amma wannan yarinyar ta bani haushi wallahi. ” Kwanciya ya gyara hade da lumshe idonsa shi kadai yasan abunda yake damun zuciyar sa. Granny kuwa mita take tayi tace”Tun farko sai da nace maka kaje ka nemi auran Hafsatu ka kiji kaga ni ai abunda nake guje maka.”

A hankali yace.” Granny magana ta wuce a halin yanzu insha Allah jibi za’a d’aura min aure da Ma ko wacece na yadda haka Allah ya shirya min.” Tace”Tunda dai kayi niyyar auran mata biyu mai zai hana ka hada da Hafsatu nasan in kayi magana baza su ki ba.”

Jajayen idonsa ya bude ya sauke su a kanta, fuskar shi a murtuke yace.” Ki k’yaleni da wani zance Inji da guda d’ayan ma ni da ba cikkakiyar Lafiya ba.”

Hararasa tayi tace”Au! Ashe munafurci ne yasa kace zaka hada mata biyu hummm! Kai dai ka sani ma kanka.”

Shiru yayi cikin zuciyar sa Yace .” Granny in batayi wasa ba zai sauke fushinsa akan ta yanzu juya mata baya yayi ta gaji da mitar ta tashi daga gurin.
Wayoyinsa duk kashe su Yayi domin baya bukatar damu a halin da yake ciki ji yake zuciyarsa tana iya bugawa ta tarwatse.

Sai daf da magari ba ya tashi daga kwanciyar da Yayi kai tsaye masjid ya nufa yayi sallolinshi tare da addu’ar Neman zabin Allah ya futo daga massalaci Jama’a na ta mik’o masa gaisuwa Amjadu bashi da wulakanci sosai ya tsaya ya gaisa da mutane, cikin ikon Allah yana shiga gidan yaji zuciyar sa tayi masa sanyi, sakamakon karatun alk’uranin dake tashi a parlor Granny ta kamo tashar Saudiya tv Jama’a na ta kewaye dakin Allah (Ka’aba) zama yayi kusa da ita da carbi a hannunta sai da ta kammala tukkuna ta kalleshi cike da kulawa tace.” Iyami ta girki dafaduka shinkafa da daddawa nasan kana son shi, tayi amfani da bussasan kifi yayi dad’i sosai. ” Murmushi yayi yace.”naji dad’i kuwa domin rabo na da cin abunci me nauyi har na manta. Granny ta mike hade da aje carbin NATA a kan kujera tace.” Naga alama kazo kaci ka koshi naga alamun yunwa a tare da kai.”
Mik’ewa yayi yabi bayan ta, yana ‘yar Dariya domin ya kwantar mata da hankali shi kam a irin halin da yake ciki yanzu kome za’a bashi bazai faran ta masa ba Idan ba Asma’u aka bashi ba.”


Shirye shiryen aure ya kammala duk wani Abu da ake bukata akwai shi a aje idan da kud’in ka ka wuce Matsalar komai, Tun safe su Kawu Yunusa suka yo gayya ‘yaya da jikoki suka zo suka kare mana zagi ni da Umma munji bakin ciki da ciwo Abunda suka zo suka yi mana a unguwa amma daga k’arshe muka hak’ura muka cigaba da sabgar mu. Duk Abunda. Amarya take yi nida aunt Hauwa mun sanya Mimi tayi domin me lallai har gida tazo tayi mata ja da baki, aunt ce ta sanya mata man shamfo a kanta, ta had’a kayan gyaran jiki na sanya Mimi a gaba na dinga mulka mata a jiki ina gogewa yinin ranar abunda muka yini kenan, lokaci guda Mimi tayi Wani uban kyau jikinta sai shek’i yake,murmushi kawai take yi ga lallan ta ya futo radau abunka da farar fata.

Bayan mun idar da sallahr La’asar ne, muka tafi can yakasai gurin dinki kayamu kala uku duk iri daya dinki iri daya komai iri daya muka karbo a dai-dai muka shiga muka dawo gida sai murna nake Mimi ta saki ranta, Muna Isa gida muka tadda Munnu tazo dakinmu muka shige muka cigaba da tsara yadda zamu gudanar da walima domin lokaci yazo a kurace gobe daurin aure jibi kuma walima kuma a ranar za’a kai Mimi.


K’arfe biyar da kwata na ranar alahamis yana zaune a harabar gidan shi jikinsa sanye da kayan motsa jiki Rambo ya shigo cikin gida a mota ya gyara parking ya futo hannunsa rike da ledoji manya manya masu dauke da tambari na sunan company nin sa, karasowa yayi kusa da shi tare da fadin”Sir barka da yamma.” Dago kanshi yayi yana kallonsa kana ya amsa, Rambo yace.” Komai ya kammala kamar yanda ka Umarta naje har gidansu na kai kayan. ” Fuskarsa babu wasa yace.” Alhmdullahi ina bunkice da na sanya kayi min.” Rbow yace.” Mahaifin yarinyar dai kamar yanda aka fad’a talaka ne sosai Dan duk ‘yan uwansa sun fi shi rufin asiri yana aikine karkashin company madara ta cowbell bayan rasuwar sa, haka naji daga bakin abokan sana’ar shi ya rasu sanadiyar hatsari a titin sharada mota ta take shi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button