BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Jikinsa daure da towel ya futo bai ko kalli inda take zaune ba, dama haka kaidar shi take yana jimawa kafin ya hada ido da mace indai yayi sex da ita. Hibbah ta miki a dadaddafe ta shiga toilet ta gasa kanta ta futo ta tar har ta shirya ya fuce daga dakin cikin sauri ta sanya kayanta ta futa…. Yana tsaye a parlor yana idanunsa kan TV yana kallon labarai na k’arfe shida na yamma Hibbah ta futo hannunta ta sanya ta sakalo wuyansa tare da fadin “Mazaje.” Kiss ta manna masa a kumatunsa cike da shauki. Idonsa na tsaye kan TV yana jin abunda take masa, sakin sa tayi ta zauna kan kujera hade da futo da wayar ta tara Neman numbar da ya bata da sunan ta budurwar sa kamar yanda ya fad’a.
Bugu daya tayi aka dauka ……….Hayaniyar da tayi yawa ne yasa na yi saurin futa soro domin naga sabuwar numbar CE, sallama nayi naji shiru INA kokarin kashe wayar naji tayi magana cike da izzah tace.” Sunana Hibbatu y kk?.”? Cike da mamaki nace”Lafiya Lou kefa.”? Ba ta amsa min ba, tace.” Amjad ne ya bani numbar ki Yanzu. ” naji wata irin fad’uwar gaba jin ta ambaci sunan sa. Nace “Lafiya dai in ce ko.”? Kasaitaccan murmushi tayi tace.” Alfarma nake nema a gurin ki, kamar yanda shi uban gayyar ya umarce ni.” Ajiyar zuciya na sauke nace”Ina jiniki ki fad’i abunda zaki fada min INA da uzuri. A Dan tunzure na k’arashe maganar tawa.

Har yanzu yana tsaye inda yake idonshi tsaye a TV amma hankalinsa yanzu na kan maganar da Hibbah takeyi da Asma’u a waya, yana daga inda yake yana jiyo sautin muryar ta, Asma’u akwai zakin murya Uwa uba kuma sai ka saka kunne sosai sannan zaka ji maganar ta saboda yadda take da saurin baki.

Hibbah tace”Yace in nemi alfarma a gurin ki kamar yanda kika yarje masa zai auri matar da kika zab’a masa nima ki yarje masa ya aure ni, domin duk cikin Ku nafi Ku son shi.”

Asma’u taji wata magana kamar ta shashashai sai taga kamar ma da rainin hankali cikin ta, kashe wayar tayi hade da Jan tsaki ta koma cikin gida abunta.

Hibbah tayi sakato da waya a hannunta tana mamaki kiran wayar ta kara yi a karo na biyu har ta katse ba dauka ba, ta kara kira a karo na uku . Da sauri na mike na kara komawa soron a fusace nace”Wai meye hakane malama kin dame ni da kiran waya, mtsssss.! Cike da taikacinta Hibbah tace”Ke ni zaki fad’awa magana kin San ko ni wacece kuwa.”?
“Sanin ko ke wacece bai dame ni ba, nasan dai bazai wuce ire-ire ‘yan matan shi bane irin Ku ‘yan iska karya.” Hibbah ta rike wayar da k’arfi ranta a mugun bace tace.”Ni kike cewa ‘yar iska.” Ko a jikina nace”Yo idan ba ‘yar iska bace ke mecece ke. Har da zaki kirani a waya kice na nema miki alfarma gurinsa ya aure ki, ni meye hadina dashi meye damuwa ta dashi, idan auran ki zai yi sai ya nemi amincewa ta tare na ganku ban San sanda kuka had’u ba, saboda haka kar ki kara kira na a waya mtssssss.” Kashe wayar nayi ina jin wani mugun takaici lallai ma guy nan Dan rainin hankali ne, haka kawai na tsinci kaina da mugun jin haushin sa dashi da ‘yar iskar budurwar tasa, tsaki kurrum nake Tabkawa.

Hibbah ta kalleshi ranta a mugun b’ace Tace”Kaga abunda ka janyo min ko.? Na lura yarinyar nan bata da kirki wallahi sai na koya mata zama a garin kano har ni zata bude baki ta gayawa magana irin wannan.”!! Dariya yake cikin ransa yace.” Indai wannan yarinyar ce halinta ya wuce yanda kike tsammani. A zahiri kuwa cewa yayi “Idan kinga abunda kikayi kina iya tafiya.” Hibbah ta mike ranta a bace ta dauki Jakarta tana fadin”Wato ka gama more ni kana ji wata yar iska na zagina kaki ka dauki mataki shikkenan. ” murmushi yayi yadan Sosa sumar shi, yace.” Nima rarrashin ta nake yi kin San itace ruhina bana son abunda zai b’ats mata rai!!.. Hibbah ta fashe da wani irin kuka me cin rai lallai namiji kanin Ajali kamar ba yanzu ya gama sukuwa a kanta ba ya kwashi romonta amma dubi yanda yake gasa mata magana me zafi.! A fusace!! Ta futa daga parlor . Tsaki yaja me k’arfi hade da zama cikin kujera yana fad’in “Sai kace ni ns kirata ‘yar iska zata zo ta dame ni da kukan banza.” Zama yayi yana shawarwari da zuciyarsa me. Zaiyi ya kuntatawa zuciyar Asma’u kan abunda tayi masa lallai ta dauki bashi domin bazai tab’a yafe mata ba halin da ta sanya zuciyarsa a ciki zai nuna mata shi namijin duniya ne jarumi zai danne sonta cikin zuciyarsa kamar bai tab’a yi ba, sai tagane kuranta zata gane wautar da ta tafka a rayuwar ta.

Bayan Sallah Jama’a aka d’aura auran Asma’u da Mimi a babban masacin juma’a Mai Martaba sarki ne ya karb’i wakilcin Amjadu duk da cewar akwai wakilan sa, d’aurin auran ya samu halatar manya manya mutane sosai abunka da na Jama’a garin labarin d’aurin auran Amjadu ya baza garin kano da ma kewayen ta, ‘yan jarida sun samu abinyi,da kyar ya samu ya futo daga cikin jama’a ya shiga mota ba tare da b’ata lokaci ba ya umarci doh, ya wuce dashi gidan granny saboda yasan in gidansa ya wuce wata Matsalar ce Jama’a gami da ‘yan jarida baza su kyaleshi ba.

15/November/2019
[11/16, 10:02 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

53

To gidan granny ma cike yake da ‘yan uwa da abokanan arzikinta sun zo taya ta farin ciki mutanan Chadi ma suna kan hanyar zuwa, aikuwa suka yi masa caaa! A ka masu tsokanar sa nayi masu fad’a masa magana nayi a fakaice Inna Suwaiba take yar masa da magana yak’i d’iyar ta Hafsa gashinan ya kwasowa kansa kara da kiyashi, wad’anda suka San akwai maganar sune suka fahimci inda ta dosa basu dad’in abunda tace ba ko babu komai ai matar mutum kabarin sa ce, Granny ma bata ji dadin abunda Inna Suwaiba take yi ba, tunda tazo gidan take yar da haibaci sai kace k’aramar yarinya.
Shi dai shigewar sa yayi bedroom din granny don har ga Allah baya cikin nutsuwar sa ballanta ma ya fahimci Abunda Innarshi take nufi


Wallahi duk makiyin mu idan ya kallemu sai mun burge shi, munyi kyau ni da Mimi har mun gaji duk inda muka wuce cikin jama’a sai kaji suna fad’in “Wai wacece amaryar ne tsakanin su biyu sai da a nuna Mimi kawai amma lokaci guda baza ka ban bance mu ba, sai hotona muke da k’awayenmu, ko wacce da k’atuwar wayar ta, nima hannu na rike da wayarshi da ya bawa Mimi mai muguwar camera mai fidda mutum nasa Munnu ta dinga d’aukar mu hoto ni da Mimi, wacce take cikin tsananin farin ciki da annushuwa.
Umma ita da jama’ar ta sai hidima suke yi aunt Hauwa kuwa ai ba’a ganinta, tun da safe da suka gama rigima da Mimi kan wani magani tazo dashi cikin jarka wai lallai Mimi sai ta shanye shi, Mimi taki shine take tayi mata masifa, nice na lallab’ata ina fada mata amfanin maganin a jikinta sannan ta dauka tasha, magani iri-iri aunt Take dirkawa Mimi wai lallai sai tayi ni’ima ni kuwa dariya kawai nake musu mussaman in naga Mimi na kuka tana shan magani. Yanzu ma gidan kawarta ta tafi wai zata karbo wani turare duk dai Mimi ake so tayi amfani dashi kafin a kaita dakin mijinta.

Dakinmu cike da ‘yan uwanmu da k’awayenmu sai surutu kake ji ana shewa zan can aure kawai mukeyi ina gefe ina sanja kayana wayar Mimi tayi kara, dama tana kusa dani ina dubawa naga heartbeat nace” Mimi zo ki d’auka. ” da sauri tazo ta karb’i wayar daga hannuna, ihu! ‘Yan dakin suka sa, suna fadin”Da Alama ango ne ko.”? Gyada kaina nayi nace.” Shine ya kira yaji lafiyar amaryar shi” suka fashe da dariya hade da tafawa suna Fadin “hohh-hohh Yau Mimi zata ji maza.”! Ita dai futa Tayi daga dakin tana murmushi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button