BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Yana kwance kan bed din granny ya cire babbar rigar jikinshi daga shi sai singlet da dogon wandon arniyar shadda da yayi futar d’aurin auren sa, da ita, juyi kawai yake yi zuciyarsa babu dad’i, ji yayi kawai yana sha’awar jin muryar Asma’u yasan hakan ba dai-dai bane, to ya rasa ya zaiyi da zuciyar sa, wacce take nema tafi karfinsa a kan Asma’u, wayar sa ya dauka ya kira numbar Mimi yana fatan Asma’u ta dauka kamar ko da yaushe, sai dai sab’anin haka Muryar Mimi yaji tana yi masa sallama, lumshe idonsa yayi hade da d’an cije lips d’insa na kasa, yace.” momyna ya hidima.”? Mimi ta damkewar wayar sosai wani irin dad’i na ziyartar zuciyar ta, a hankali tace.” Alhamdullahi.” “Ok babu wata matsala ko.” “Eh babu mungode sosai da Hidima” murmushi yayi kawai yana jin tausayin yarinyar yasan so masifa ne, abunda yake ji a halin yanzu yasan shi take ji a zuciyar ta dole ya girmama mai sonshi yace.” Haka nake so, Idan anjima Ku shirya akwai Walima da abokina masu mak’otaka dani suka shirya min,zan aiko a dauke Ku a mota OK.” Mimi tace.” Insha Allahu. Kokarin kashe wayar yake tace” ko in bawa Asma’u wayar ne.” ? Girgiza kansa yayi kamar tana kallonsa yace.” K’yaleta kawai Momyna zamu gaisa idan anjima OK.”
Kafin Mimi tace Wani Abu ya kashe wayar yana jin wani mugun daci a bakinsa, ko wane ango yana farin ciki ranar d’aurin auransa mussaman idan ya tuna amaryar sa, amma shi ranar d’aurin sa ta zame masa ranar bakin cikinsa Asma’u ta cuce shi, bai ta tunanin zai fada rudani na so irin wannan ba.dole yayi kokarin sa Mimi cikin zuciyar sa, ko don ya haddasa Asma’u ciwan zuciya kamar yadda take kokarin haddasa masa, wannan itace shawarar da ya yanke.
Mimi ta dawo fuskar ta cike da walwala da farin ciki, tace”Asma’u yace.” Mu shirya bayan sallah magariba zai turo a dauke mu akwai walima da a bokanshi suka hada masa, da har nace ko in baki wayar Ku gaisa yace A’a in k’yale ki.” ‘Yan dakin suka kwashe da dariya tare da fad’in”Haka kurrum yana jin zakin muryar ki, zaki had’a shi da masifaffiya mai saurin baki, mai zai fuskanta ya burgini da ya gwale ki.” Dariya suka kwashe da ita har Mimi din, wani irin b’acin rai ne ya kamani lokaci guda, ganin yanda suke min dariya sai naga kamar da gayya suke yi min har ita Mimi din, raina ya b’aci mutuka, Mimi tace. A bani wayar yace baya bukata lallai ma guy nan, cikin jin haushin su nace banzaye ‘yan iska kawai baku da aiki sai iskanci da dariya Ko wacce ta rasa mashinshini don Allah a daure ayi aure ko kwa rage zumudi da tsiyayar da kuke yi.” Ihu!! Suka sanya kamar wasu shashasha, Maryam tace”Dallah malama yi mana shiru ke akwai wacce ta fiki zuba, daga an fara zancan aure zaki hau lumshe ido idonki har ja yake yi “yar iska, hahahahaha ” ta k’arashe maganar tana dariya Tare da bawa ta kusa da ita hannu suka tafa tsaki naja me k’arfi nace “Kanku a keji, kun dai ji Abunda Mimi tace ko, gaskiya Ku kintsa sosai bana son shirme a gurin ku zama manyan baby’s kar Ku bani kunya shegu.” Munnu tace”Dole ne ai nasan gurin zai had’a had’addan Samari gaskiya
Dariya muka kwashe da ita nace”Munnu ta Shamsu kenan” Hararata tayi, ni ko na cigaba da shiryawa ta ina mata dariya, aunt Hauwa ce ta lek’o dakin tare da kiran Mimi hannunta taja suka futa, nace”Mimi yau kin bannu a gurin aunt Hauwa.
K’arfe takwas dai-dai gurin Walima ya k’ayatu, nan cikin Estate din aka shirya komai guri Tasha decoration, haske ko ta ina ga wasu shegun kujeru an ajiye guda biyu na ango da amarya ne, su uku ne kacal cikin Estate din, Ma’aruf Mujahid Hafiz sai Amjadu din, dukanin su ma’aikata ne, Hafiz yana aiki a babban banki najeria, shi kuma Ma’auruf yana aiki a babban Asibiti na nasarawa Mujahid yana aiki a Company d’angote cement shine manager dukaninsu suna da aure da yara biyu Hafiz ne me D’a d’aya tunda shi bai jima da yin auran ba, sai Amjad da yayi aure yanzu, suna zama na fahimtar juna a tsakaninsu, kasamcewar su Ma’aikata yasa basa haduwa sosai sai weak end suke had’uwa su gaisa da junansu sai kuma lokacin azimi suke shan ruwa tare, yau idan an sha ruwa gidan wannan gobe a sha gidan wancan, Amjad sai dai yaje domin shi bashi da matar ma, sunyi ciwon baki har sun gaji, Matar Hafiz me suna Samina ita ce ta dinga nanika masa k’anwar ta yana basarwa da ta lura ba auran zaiyi ba kawai sai ta hak’ura, amma dukaninsu sun yi mamaki da suka ji labarin auran sa katsaham! Shine suka shirya masa walima domin taya murna, amma da ba don haka ba , shi babu wani shiri da yayi domin murnar ranar.
Dukaninsu sun gayyaci abokanan su shiyasa guru ya tsaru domin duk manyan ‘yan boko ne samari masu kwalisa gayu kenan, ango kuwa babu wani abokan shi da ya gayyata, to yawanci ma shi bai fiye sakewa da mutane ba, kuma abokan shi da suka shak’u da juna turawa ne, ‘yan gari daban-daban shiyasa sam bai da abokai a najeria sai Wanda ba’a rasa ba.
Shigar wani irin yadi suke yi baki Wanda bantab’a ganin irin shi ba, dinki iri daya huluna iri daya takalman su iri daya kai hatta da agogon hannunsu iri daya ne, sunyi kyau sosai da sosai, Amjad ya futo ango dashi sai gaisawa yake da jama’a fuskar shi babu yabo babu fallasa.
To muma namu b’angaran haka take mun shirya sosai ko wacce ta k’ure kwalliyar ta, ni da Mimi kayan mu iri d’aya, cikin Wanda ya aiko Rambo dasu ne jiya muka dauki wani masifaffan les ruwan Zuma, anyi mishi wani irin dinki mai tutoci gaba da baya dinki Riga da siket ne rigar kuma bata da girma babu abunda yafi burge ni da dinki sai yanda aka kaya ta hannun rigar d’aya dogone d’aya kuma gajere gajeran anyi masa wani falmaran a saman sa cif rigar tayi min amma duk da haka saman k’irjina sai da suka futo k’aida ne dama indai zan sanya Riga pitatd to sai saman nonuwana sun futo har tsagar su, saboda Allah yayi min baiwar su, sai nayi amfani da gyale mai Dan fad’i inda na samu ya rufe min mazaunai na, amma yana da sharara dole sai an ga komai nawa, hakan ma dai dashi gwara babu, ni kuma bazan yi kwalliya ta in sanya babban mayafi ba.
Mimi kam net ta sanya kamar yanda amare suke yi muka futo waje muna ta d’aukar hoto, wayar na hannuna naga kira, shine na daga kaina ina Neman Mimi tana can suna hoto, a dake na daga wayar nayi sallama.
Zuciyarsa yaji dam!! Jin muryar ta, dake namiji ne sai ya maze cikin wata ‘yar iskar murya yace.” Mommahh ga motoci nan sun tawo d’aukar Ku, na k’agu naga fuskar ki, wallahi naji k’amshin ki, humm! Ina fatan zan same ki, a yanda nake tsammani, sai kunzo.”! Kashe wayar yayi ba tare da ya bari tace komai ba, ya maida ita aljihunsa, ya cigaba da sabgar shi da jama’a.
Saroro nayi da waya a hannuna gwiwa tayi sanyi sai naji duk wani karsashi da kuzari na, yayi kasa, tunanin guy nake, dama can yana son Mimi Ashe yake pretending ko kuma yanzu ya fara sonta, ni dai tunda nake dashi ban tab’a jinshi da irin wannan muryar ba, gashi yana fad’a mata kalamai na so, zuciyata ta shiga zullumi da wasi-wasi, gashi tayi min wani nauyi ina jin bakin ciki a cikinta da kyar na dai-dai ta kaina na shiga cikin jama’a muka cigaba da hoto amma lokaci lokaci sai inji fad’uwar gaba idan na tuno guy din.
Motoci uku ya turo masu zafi dama ba mu fi mu bakwai ba, muka shiga sai Jan bolo gurin parking motocin suka k’arasa da mu sannan ko wacce ta futo, haske ko ina da ina kamar rana ga wasu manya manyan motoci a fake a gurin, k’amshin turare kuwa na wannan yana wane wancan, can hango shi ya tawo abokanshi biyu a bayan shi, gabana ya dinga bugawa tun kafin su k’araso nake kokarin nemo jarumta ta tana guduwa yayi min masifar kyau! Farin mutum cikin bak’aken kaya, sai ya zama kamar wani tauraro cikin abokan nasa abun mamaki tunda ga nesa nake hango wani kwantaccan murmushi k’ayattace a fuskar sa, Suna karasowa gurin ya rike hannun Mimi tuni abokan shi da masu d’aukar hoto suka fara aikin su, suka fara tafiya mukuma muka rufa musu baya, na lura bani kadai ce na shiga halin d’imuwa ba har da k’awayemu suma duk jikinsu yayi sanyi ganinshi narasa me yasa yake wa mutane kwarjini haka,mussaman mata.
Addu’ar Neman
nake cikin zuciyata, “Wallahu galibun ala’amri.” wannan addu’ar nake yi cikin zuciyata domin ina ganin zuciyata zata iya tona mun asiri, a gurin, shiyasa na dauki alk’awarin bazan k’ara kallon inda yake ba, suna. Tafiya ana musu vedio da hotona har suka Isa gurin zaman su, muma muka samu guri muka zauna, sannan guri yayi shiru mai gabatar wa ya tashi ya gabatar da malamin da zai fad’a kar kam zaman aure da abunda auran ya kunsa
Wa’azi yayi kyau kuma ya fad’ar kar sosai bayan ya gama. Masu rabo suka shigo suka fara raba wasu manya-manyan ledoji komai cikin nutsuwa akeyin shi, ko da wasa naki kallon inda suke zaune, hira ma muke yi da Maryam tana k’ara fada min Yanda Mimi tayi dace da miji tana fadin”Dole sai tayi da gaske domin akwai ‘yan matan shi da suka d’aura arinyar akanta mussaman Alina.” Nace”Dole kuwa Alina kinga ko zuwa bata yi ba.” Maryam tace”Yaushe zata zo matar da tunda taji abun take tada Aljanu.” Dariya nasa Ina rufe fuskata da hannuna kawai sai naga hasken flash dago kaina nayi da sauri, naga d’aya daga cikin abokan shi Wanda suka sanya kaya iri daya yana tsaye a kanmu nida Maryam sai daukarmu a hoto yake mussaman ni. Bata fuska nayi ina kallon shi, murmushi ya sakar min, tare da kashe min ido daya. Dauke kaina nayi ina Jan tsaki k’asa-k’asa. Gurin ya bari yana duba wayar shi, hotona yake dubawa