BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Ya Aminu da Babban su Munnu sune suke mana cukucukun makaranta nan FCE Babban su Munnu yake sha’awar muyi mu samu ko Diploma ne tsakanin Munnu da Ya Aminu soyayya tayi k’arfi domin Babansu ya kori Shamsu tunda yayi da shi ya turo manya a yi magana shikkenan ya gudu daga ranar be kara zuwa ba.
Gaskiya naji dadin koma wa makarantar da zamu yi ina mutukar son in ga nayi karatu me zurfi a rayuwata.
Ni da Munnu sai shirye-shirye muke yi wacce tayi tayi dani muje gidan Mimi naki zuwa, ita kuma tace baza taje ita kadai ba.
Rayuwa suke da Mimi babu yabo babu fallasa Shine me Dan shige mata jiki ita kuwa kullum kamar suruka take a gurin shi, idan yana guri ta dinga b’oye-boye kenan shi dai sai dai yayi dariya kawai yana mamakin me zata b’oye masa Wanda be gani ba.
Tun ranar da ya kwanta da ita kwamciyar aure bai kara takar ta ba, sai dai duk daran duniya yana ragewa kansa zafi da ita, amma bai kara gangancin yin sex da ita saboda baiji da dad’i ba a farko.
Misalin k’arfe goma sha biyu da rabi na ranar Asabar Wanda yayi dai-dai da satin Mimi biyu gidan Amjadu, tana zaune a parlor ita kadai lokacin ya futa zuwa company sa kuma dai shirye-shiryen tafiya Chana yake yi shiyasa kwana biyu baya zama sosai.
Kallo take yi ita daya kamar tsuntsuwa, sai ta soma jin takun takalmi za’a shigo parlor da sauri ta kallo kofar shigowa, suka Had’a Ido da Alina ta shigo cikin wasu ‘yan iskan kaya fuskar ta tasha make up sai taunar cingum take, hannunta rike key din motar ta tana kar kad’a shi, tazo ta tsaya kan Mimi tana girgiza jikinta, cikin shigar raini.
Mimi tace” Alina babu sallama kika fado min gida.”
Wata irin mahaukaciyar dariya Alina ta kwashe da ita tare da fadin”Su Mimi masu gida!!!! Hahahahaha.” Mimi ta bita da kallo cike da mamaki.
Wani irin tauna tayi wa cingum din bakinta tayi kwai dashi ta kalli Mimi a d’age tace.”Ina sugar Boy yake yi.”?
Alina ce kawai take kiran shi da wannan sunan.”
Mimi tasha kunu tare da fadin “Ban sani ba ni Zak…….. Kafin ta karasa Maganar tata Alina ta wanke ta da mari tare da fadin” Kinyi ganganci Wallahi!! Kinyi gangamcin shiga gona ta, shigiya ‘yar mutsiya ta, kar ki ce bam san abunda yake faruwa tun daga farkon auran Ku har karshen sa, duk nasan komai, Wallahi i n da nasan haka zakuyi min da ban gayyace Ku brhday na ba, Maciya amana kawai.”
Mimi ta mike tsaye da sauri tare da buge hannun Alina dake kokarin kai mata wani sabon marin, tace”Ba Isa kizo har cikin gidana kiyi min iskanci ba, wallahi yanzu zan sanya ayi miki fata-fata a gidan nan.”!! Dariya Alina ta kwashe dashi ta daki! Kirjin Mimi tana watsa mata kallon raini tace”Nasan fa komai banza kawai kema da kike rawar Kai kin aure Sugar Boy a banza domin bake ya ke so. Ba ya fi son wancan mutsiya ciyar yarinyar mummuna Asma’u, to Wallahi duk sai nayi maganin maciya amana kawai.”
Mimi ta fusata ta d’aga hannunta zata kai mata duka Alina ta goce da sauri ta sanya gwiwar hannunta cike da mugunta ta mangare Mimi ta fad’i kan kujera, takalman ta masu tsini ta cire ta fara dukan Mimi dasu abun. Mamaki, Mimi ta fara kokarin k’watar kanta tana kare fuskar ta, inda Alina ta sanya tsinin takalmin ta ta buga mata a goshi da mugun k’arfi sai jini ya soma zuba, da sauri ta futa daga parlor.Mimi ihu kawai take hade da dafa goshin ta dake zubar da jini duk ya b’ata mata fuska.
Alina kuwa a fusace ta figi motar ta ta fuce daga gidan.
Da kyar ta dauki wayar ya ta fara Neman numbar sa, kira kusan biyar bai dauka ba, gashi dai tana ringing aje wayar tayi tana kuka ta nufi firji k’ankara ta dauko ta Dora a goshinta inda yake zubar da jini gurin har ya kumbura yayi tsini
Alina kuwa tana tafiya cikin motar ta tana tunanin sharrin da zata kulawa Mimi gurin Amjadu. Wayar ta dauka ta fara kiran shi, sai da tayi ringing sau uku ba ‘a dauka ba. Ana hudu ne ya d’auka,
Murya sa s tsaye yayi sallama domin ya gane numbar Alina ce.
Wani irin mahaukacin kuka ta fashe dashi, tana fadin “Na shiga uku na lalace!! Hubby naje gidanka sun taru sunyi min duka.”
Kasa gane inda maganar ta ta dosa yayi yace.” Ke wai meye ne, ina da uziri yanzu.”
Alina tana gursken kuka tace.” Asma’u da matarka Mimi ne sukayi min dukan mutuwa Yanzu na ina kan hanyar zuwa hospital.”
Cike da mamaki yace.” Me kika yi musu? Kuma me ya kaiki gidana.” Cikin kuka kamar gaske tace”Kasan munyi skull tare dasu sai ince maka gurin zaman mu d’aya dasu, dake ban samu damar zuwa bukin ba, sun gayyace ni, shine naje nayi musu Allah ya sanya alkairi Asma’u tazo gidan ,shine suka taru suka dinga dukana.”
Kashe wayar yayi saboda tsabar takaici, Alina ta fashe da dariya tana draving tace”Shegu ‘yan iska ai tunda bani na aure shi ba, sai na hada muku sharri a gurin sa, wayar sa ta kara kira yana kallon kiran yak’i dauka.
Tunani yake wato bayan futowar shi daga gida Asma’u taje gidan shi, yasan duk abunda Alina ta fad’a Asma’u zata aikata sun mayar masa da gida sansanin yak’i baya ganin laifin kowa sai na Mimi gani yake Asma’u ce take murza akalar ta, sai abunda tace da ita sannan take yi,
Wayarsa ya dauka ranshi a b’ace! Sai yaga kiran Mimi kusan sau shida, lallai zancan kenan, bugu daya wayar tayi Mimi ta d’auka tana shashshekar kuka.
Wata irin tsawa ya buga mata tare Da fadin”Babu babban mai laifi sai ke Momy menene zaku Tara mata a gidana kuna fadace-fadace sai kace wasu yara, na lura sai abunda Asma’u tace kiyi kike yi ko.”!!
Mimi ta tsananta kukan ta tana so ta fahimtar dashi amma Sam yak’i sauraranta masifa yake mata.
Daga k’arshe yace.” Kafin in dawo ki sallami Asma’u domin baza ta zo gidana tana tada min da fitina ba.”
Kashe wayar yayi bai bari tace Komai ba.
Mimi rasa abunda yake mata dad’i tayi goshinta ya suntume yayi tsini ga zugi yana yi mata, ta lailaiya shi, duk da haka babu sauki, kwamciya tayi kar kujera tana kuka tare da tunanin maganganun Amjadu da inda suka dosa, wanene Ya sako Asma’u cikin case din gidan sa, da zai kama fad’ar bakaken maganganu Sam ya maki tsayawa ya saurari maganar ta.
Wayar ta ta d’auka ta nemo numbar Asma’u lokacin ina kwance kam katifa sai juyi naje yi yanzu har na saba da kwanciya ni kadai a daki, k’atuwar waya tace a hannuna wacce Mujahid ya kawo min ita shekaran jiya, yanzu ka chat muke dashi sai dariya nake ni daya.guy ya iya zuba kalaman soyayya ina so ayi ta nuna min so, ina tsaka da bashi amsa kiran Mimi ya shigo cikin wayata
Da sauri na daga wayar murya ta a sake nace”Mimi yane.”? Kuka ta fashe dashi! Nayi saurin mik’ewa zaune tare da fadin “Menene.”? Tace.” Asma’u Alina yazo har gida tayi cin mutumcin har da su duka da mari baki ga yanda ta fasa min goshi ba.” Kai tsaye nace”Zata ai kata abunda yafi haka, tunda naji labarin cewar haukane kawai bata yi ba, da ta samu labarin d’aurin Ku.
Yanzu ke wane mataki kika dauka.”?
Cikin kuka Mimi tace”Asma’u kin San dai halin Alina da sharri da kitifi shi kan shi Amjadu ta hada ni dashi, baki ga yanda ya bugu min waya ba yana cimin mutumci har dake a ciki.”
Shiru nayi ina mamakin maganar ta yo ni me ya kawo ni cikin sabgar su, idan ba Neman fitina ba, meye alakata dasu ina gefe guda.
Nace “Mimi kar ki kara Bari wata ‘yar iska tazo har cikin gidan ki ta doke ki kuma duk sabda Alina ta kara zuwa gidan ki kira ni a waya, Wallahi sai taci kutumar ubanta.”
Mimi tace”Shikkenan ni kaina nayi kokarin k’watar kaina ta samu rinjaye a kaina. ” tsaki naja cike Da takaicin ta da jin haushin ta nace”Banza kema babu abunda zaki iya sai aukin kuka idan zaki d’age ki kwatarwa kanki ‘yanci ki zage ki kwata.”
Ina gama magana ta kashe wayar cike da jin haushin Mimi domin duk shashancin ta ne, mace tazo Har cikin gidan ka ta doke ka, lallai Alina tayi kaurin suna.