BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Ko da ya dawo gidan ma fad’a sosai ya dinga sirfawa Mimi har ta dinga mamakin dama haka yake da fad’a kuka take tana bashi hakuri, bedroom d’insa ya shige cike da b’acin rai.!
Wanka yayi ya futo daure da towel me girma zama yayi gefen bed ya dauki lopto dinshi yana dubawa.
Mimi tayi sallama simi-simi ta shigo dakin. Ba tare da ya d’ago kansa ba ya amsa mata sallamar, hankalinsa nakan loptop dinshi.
Zama tayi kusa dashi jikinta a sanyaye!
Da gefan ido ya kalleta yaga goshinta s kumbure d’ago kansa yayi yana kara kallon gurin, shi Sam bai lura da gurin ba
A ya mutse yace.” Kin ce Alina karya take muku ga shaida nanan a goshin ki alamun kun daki juna da ita.”
Shiru Mimi tayi saboda ita yanzu bata son a kara maganar.
Tsaki yaja abunsa ya cigaba da duba loptp dinda
Mintin goma sha biyar ya aje ta gefan bed din, ya kamo Mimi tare da rungume ta a jikinsa.
Goshin ta ya kama ya sanya karfinsa sosai ya hau mulmulawa, kuka take sosai, sai da ya tabbatar gurin ya koma sannan ya sake ta, tare da fadin”Idan har kin San Asma’u zata dinga zuwa gidana tana hada min husuma da tashin hankali tom kice mata inji ni bama Neman ta tayi zaman ta inda take, ina laifin Alina don tazo taya ki murna. Kawai sai Ku hauta da duka sai kace marasa hankali, nasan sharrin duk ba na kowa bane sai na Asma’u.”

Cikin dauriya Mimi tace”Wai Alina ce tace maka har da Asma’u? To wallahi karya take tsabar sharrinta ne, tun ranar da Asma’u tazo gidanan bata kara zuwa ba.” Yace.” Dole ki kare ta dama saboda kar ta tsigale ki, ni dai na fada miki ki kiyaye.” Cikin kwantar da Kai tace shikkenan Insha Allah haka baza ta kara faruwa ba.”
Kwanciya yayi kan bed din yana lumshe idonsa, ita kuma ta tashi jiki babu k’wari ta nufi toilet wanka tayi ta futo salau-salau ta bude wardrobe kayan baccin ta ta dauko ta sanya Riga da wando ne amma irin masu santsin nan, a hankali ta nufo bed din, ta kwanta gefan sa.
Gogan Ku kuwa k’amshin turaran ta ya dame shi, abunka da mayen turare nan take ya jawo ta a zafafe ya hau ya mutsa ta, yanzu Mimi ta saba da jarabar shi, haka ta hak’ura yana ta murza mata nonowa yana wasa da joystick dinshi a gurin. Mimi Sam bata iya komai ba, ta dinga kauda kanta kenan wai ita kunya shi kuma ya dinga buga mata tsaki da harara ya na nuna mata inda zata tab’a masa, idan taki sao ya dau hannunta ya d’ora a gurin.da kyar take kamawa take masa wasa, inda yake sakin wani irin nishi na dad’i
Haka suke rayuwar sai tayi wuta sannan zai yi sex da ita amma yana samu ya kawo sai daya yake rabuwa da ita.


Tsaf ya futo cikin shiri yana sanye da wasu suit blue and white wanda suka yi masa kyau sosai komai na jikin shi kalar blue da white ne, sai kamshi yake Mimi na binsa a baya idanunta duk sun kode da kuka, wai tafiya chana zai yi dagan ya wuce Ingila kuma yak’i Sanar mata da ranar da zai dawo, shine ta damu.

Hannunta ya rike sosai yace.” Momy kiyi hakuri kinji ko, ki kwantar da hankalin ki, granny zata zo ta taya ki zama har in dawo babu matsala cikin tafiya dama nasa ba lokaci zuwa lokaci.” Mimi ta fashe da kuka hade da rungume shi, da kyar ya cire ta daga jikinsa ya futa daga parlor cikin sauri bodyguard d’insa suka rufa masa baya.

Zubewa tayi tsakiyar parlor tana wani irin kuka ta ina zata fara rayuwa a cikin gidanan ita d’aya ko sati biyu bata cika ba an tafi wata uwa duniya an bar ta, kuka take sosai.

Mimi tafi a wa gudu a gurin tana kuka daga bisani ta mike jikinta babu k’wari ta shiga bedroom dinta wayar ta ta dauka ta kira Asma’u.

Ina d’aukar wayar naji ta fashe da kuka, tsaki naja da k’arfi nace”Wallahi Mimi Matsalar ki ta fara isata da me zanji ne? Da karatun ko da Matsalar ki, kullum sai ki kira ni kina min kuka, ke baza ki iya gyara Matsalar ki da mijin ki ba.”?
Da shashsheka tace”Asma’u yayi tafiya ya barni kuma yak’i fada min yaushe zai dawo.” Tsaki naja a karo na biyu nace”To sai me.”? Kiyi zaman ki mana.” Tace”Yace ma kakar shi zata zo ts taya ni za ma.” Nace”To kin huta ai amma don Allah ki daina Wannan kukan da kike yi bashi da amfani.”
Mimi tace”Habibty Wallahi kwana biyu bana jin dadin jikina kullum bana iya cin abunci ga jiri da tashin zuciya ina ji.” Nace” kinji asibiti ko kin San dai kina da maleria.” Tace.” Banje wallahi, amma don Allah gobe kizo muje ki rakani.” Nace” Allah ya kaimu, yanzu kakar tashi tazo ko kuwa.”?
“Tana kan hanya.” Nace “Shikkenan Allah ya sawake don Allah ki kwantar da hankalin ki.” To tace mun na kashe wayar.
Munnu ta kalle ni tare da fadin “Bata da Lafiya ne.” Nace”Wai zazzab’i take ji da jiri. “
Munnu tasa dariya tare da fadin”Shikkenan Mimi ta hau network sai fatan sauka Lafiya. “
Take naji wani muguwar fad’uwar gaba, na kalli Munnu cikin mamaki nace”Ciki.”? Munnu na dariya tace”Eh mana wallahi ko kaffara bazan yi ba Mimi ciki gare ta, kinsan ranar d’aurin auran ta tayi wank ma tsarki kin manta har su Maryam suka dinga tsokanar ta, tana shiga zatayi gamo aikuwa gashinan. “
Rasa miyau nayi a bakina ya bushe Kama’s gashi babu wani tes ko na kwabo jikina yayi sanyi sosai Wahidun k’ahar Allah mai barwa da hanawa……….

19/11/2019
[11/20, 10:07 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

57

Munnu ce kawai take surutun ta i ta kad’ai ni kam ina can duniyar tunani lamarin ubangiji wai Mimi har tayi ciki zata haihu, Allah babu yanda baya tsara almarin shi. Yanzu Sai dai kawai mu taya ta addu’ar sauka Lafiya, yau sama-sama nake a makarantar, domin na kasa sakewa da abun ya fado min zan ji fad’uwar gaba, ya zama Dole na cire son shi a cikin zuciya tunda yanzu nasan yayi min nisa na har a bada.


Ina koma wa gida Umma take min zancan Miki ta kirata a waya wai bata da lafiya bayan haka kuma Mijinta yayi tafiya tace kije ki taya zama.”

A tausashe nace”Umma nima munyi waya da ita d’azu ta fad’a min, amma ni dai bata ce min naje in taya ta zama ba, tace kakarshi zata zo ta taya ta zama. Amma dai munyi maganar zan rakata hospital taga dactor. “

Umma tace”To tunda kakar shi zata zo sai kiyi zaman ki, ai na dauka ita kadai zata zauna a gidan.”
Girgiza kaina nayi. Mik’ewa nayi na shiga kicin domin wata irin yunwa nake ji.

Washe gari da wuri na shirya Dan ma Allah yasa bamu da lecture a ranan da ko sai dai Mimi ta hak’ura Umma nayi wa sallama na tafi tana fadin ‘ki gaishe min ita da jiki. Umma ba yarinya bace ta fahimci Mimi ta samu ciki. Sosai take murna da farin ciki.

A dai-dai ta sahu na samu har gidan Mimi na biya shi kudinsa sannan na tsallaka Titi na Isa jikin gate din inda nake hango masu gadi a zaune, fuskata ba b’oyayya bace a gurin su, nan d’aya daga ciki ya tawo da sauri ya bude min na shiga ciki ba tare da na kalle shi ba na wuce part din Mimi cikin nutsuwa.

Suna zaune ita da granny a parlor suna hira nayi sallama na shiga, Mimi ta amsa tare,da mik’ewa da sauri ta tare ni, kallon fuskar ta nayi sosai naga ta rame amma tayi haske sosai.

Zama nayi kan kujera ina gaida Granny ta amsa fuskarta a sake, take fadin”ai gwara kuje likita ya dubata tun d’azu take amai gashi bata ci komai ba Mimi na kalla dake ya mutse fuska nace”Ina gani ba sai munje asibiti ko in kira Mujahid ya duba ki, ko ya kika gani.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button