BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Granny da Mimi suka nufo kicin din da sauri. Surutun granny yaji tun kafin su k’araso kicin din ya sa ya mike da sauri! Kofar da zata sada ka da store ya bude da sauri ya mai da kofar ya rufe.
Mik’ewa nayi da sauri sai haki nake yi. Rigata na gyara da sauri! Na dauki wuk’ar da ta fad’i kasa. Suka shigo kicin din.
Granny tace”Menene kike yin ihu!? Ina kuka nace”Granny yanke wa nayi.”
Mimi ta k’araso gurin tana duba hannuna kuka ta sanya tace”Muje ki zauna na fasa cin miyar.”
Nace”Mimi me zaki ci ki bari in k’arasa miki domin yau Zan tafi.” Granny tace” A’a kije ki huta kinji yau dai daya.”
Rike hannuna tayi muka futa daga kicin din gabana na fad’uwa.
Yana dai na jin motsin su ya futo yana Jan tsaki. Parlor ya shiga lokacin duk suna dakin Mimi. Kai tsaye dakin shi ya nufa, dole ya sake yin wanka, domin jikinsa duk ya b’aci ga wata irin kullewa da mararsa take masa, ba bu tantama dole ya nemi me biya masa buk’ata.
Kuka Mimi take min kar in tafi ita a ganin ta nice garkuwar ta a gidan nace”Mimi ciwo da lafiya duk na Allah ne ki kwantar da hankalin ki insha Allahu zaki samu lafiya.”
Granny ta sanya bakin ta tace”Kiyi hakuri ki zauna mata tunda tana son zaman ki kuma tana walwala zaki samu lada gurin Allah, kinji ko, ubangiji Allah yayi miki albarka.’
Karamcin matar ya sanya na hak’ura amma ni kaina nasan zama a gidan hadari ne ina ganin mutumin nan zai iya fad’o min tsakar dare. Dole in dawo kwana da granny.
Sai daf da sallahr magrib ya futo daga dakin shi, lokacin muna zaune a parlor muna kallo ko ince suna kallo domin ni Sam bana Cikin hankalina.
Yana sanye da jallabiya ash coulor hannunshi rike da carbi me maddanai, yayi shirin zuwa masjid, Granny ta kalle shi tare da fadin”Au! Kana cikin gidan Ashe.”? Babu walwala yace.” Eh zan je massalaci.”kallonsa nayi cike da wani irin tsanar sa, kullum yana nunawa duniya shi na Allah ne amma bayan fage yana aikata sab’o Allah ya shirye shi idan me shiryuwa ne.
Futa yayi ba tare da ya kalle mu ba, granny tace.” Yau me zamu ci ne me mana girki ta yanke a hannu.”
Mimi tace”Rambo yayi mana take away kawai.
“Ke kika San wani take away ni kam ban San shi ba, gashi me gidan ki ya dawo bai ci abunci ba kuma naga baki damu ba, ya kamata ki shiga kicin din in zaki iya kiyi masa girki ko.”
Mimi tace”Granny baki San halinsa ba, wallahi zai iya cewa baya ci.” Shiru tayi minti biyu tace”Nasan halinsa farin sani, amma bari inyi sallah ni da kaina zan shiga kicin din.”
Kafin Isha’i granny ta kammala girki tsaf inda ta shirya jalop din macaroni da dankalin turawa hade da kayan Lambu da bushashen kifi
Kamshi ne kawai yake tashi.
Mik’ewa nayi ina taya shirya daining din tsaf ya shigo hankalinsa a kanmu ganin granny a tsaye a gurin ya k’araso da sauri yana fatan ita CE tayi abunci
Matsawa nayi daga gurin da sauri, ni yanzu tsoro yake bani.
Mimi ce ta hada masa abunci ta zauna kusa dashi
Yana ci suna hira sama-sama, ni da granny muna parlor a zaune. Mujahid yayi sallama ya shigo kamar yanda ya saba, babu iso babu komai yana ganin duk an zama d’aya.
21/11/2019
[11/22, 9:48 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
MALLAKAR_ BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI
59
Da murna granny ta tare shi tana fad’in”D’an halak yanzu nake zancan ka, a zuciya ta Ashe kana tafe.”
Mujahid ya k’araso tsakiyar parlor fuskar sa a sake yake fadin” Ina shigo wa naga alamun mutumin ya dawo shiyasa ko gida ban shiga ba na shigo.” Granny tace” Aikuwa ka kyauta. “
Daining din ya nufa yana fadin”Kai baka ce mun kana kan hanya ba, muje dauka ka.”
Amjadu fuskarsa ya ya mutse Sam! Yak’i sakar wa Mujahid din yace.” Akan me zan kashe maka aiki.”
Jahid ya sanya dariya yana kallon Mimi yace.” Kai kake ganin haka amma kafi k’arfin komai a gurina.”
Shuru yayi masa ya cigaba da cin abuncin sa.
Mimi tayi saurin mik’ewa domin kar ya fuskanci komai tace”Dr zauna ina hada maka abunci.”
Zama yayi kamar yanda ta umarce shi.
Yace.” Madam lallai yau lafiya ta samu, har da shiga kicin.”?
Mimi na hada masa abunci tace”Aikin granny ne.”
Girgiza kansa yayi yana fadin ” lallai yau zanci abunci me gamsarwa domin girki tsaffi daban yake da ‘yara.”
Granny ta sa Dariya domin duk tana jin hirar su tana parlor a zaune.
Ni kuwa tun shigowar sa na mike da sauri na bar gurin,
Saboda tun kafin ya zauna naga kallon wulakancin da Amjad din yake masa
Simi-simi ta Mimi ta hada masa abincin ta bar gurin.
Domin itama ta lura da kallon rainin da Amjad din yake masa Sam bata so ayi abun kunya.
Mujahid bude ciki yayi yaci abunci sosai suna hira sama-sama, Wanda shi Jahid din ne yafi magana Amjad sai ya ga dama yake amsa masa.
Tsaf suka kammala ko wanne ya goge bakin shi da tissue, Mujahid ya kalle shi, cikin nutsuwa yace.” K’warai naji dadin dawowar ka wallahi.”
Gyara fuskarsa yayi yace.” Alhamdullahi, nima naji dadin dawowa Cikin nagode K’warai da kulawa Allah ya kara zumunci.”
Jahid yace.” Kar ka damu Aboki duk yiwa kai ne, nima ban sani ba ko akwai ranar da zaka yi min nan gaba.”
Murmushi Amjad yayi halin Jahid yana burge shi guy akwai saukin kai Sam! Bai dauki duniya komai ba.
Mujahid yace.” Cikin madam wata uku ne, amma hakikanin gaskiya tana cikin hadari tare da yaron dake cikin ta, domin NASA anyi mata scanning kuma Abu guda yake nuna min.
Twins ne daya cikin mahaifa daya bayan mahaifa, to amma kasan ba yadda Allah baya tsara al’amarin shi.”” Wani irin shocking jikinsa yayi lokacin da yaji abunda Jahid yake cewa, da sauri yace”Please ka fada min in fahimta Dr akwai k’wayaye na cikin Mimi sai me kuma kace.”?
Ganin Amjad din ya gigice lokaci guda yasa Jahid din yace.” Tabbas hakane amma gurin kwanciyar kowa daban. Ma’ana kowa na da mahaifar shi, kuma d’aya yana zaune a wajen da ba’a so.”
Wata irin zufa ce ta ke to masa.
Take ya ci wata irin fad’uwar gaba ta rikito masa.
Baki na rawa yace.” Jahid meye abun yi yanzu, Ina son baby’s dina duka.”
Cikin damuwa Jahid din yace.” Ka kwantar da hankalin ka, insha Allahu komai zai zo da sauki, aiki kawai za’a yi mata mugani tunda cikin bai yi k’wari ba, sai a cire shi akwai a huta.”
Jim! Yayi yana tunani yace.” Dr babu yadda za’ayi dole sai abunda ka fada.”
Jahid yace.” K’warai kuwa shi ne zamu samu Madam insha Allah Amma tabbas idan cikin jikinta ya kai wata biyar tabbas tana cikin hadari ita da baby.”
Kamar zai yi kuka yace.” OK amma babu abunda zai samu d’ayan ko.” ? Murmushi Jahid yayi yace.” Babu insha Allah mu fatan nasara muke yi.”
Amjad duk ya rud’e Allah da ya hallice shi yana da mutukar son yara mussaman Twins shiyasa yanzu duk ya damu, wani irin tausayin Mimi da kaunar ta suka dura a zuciyarsa. Ya manta ma da haushin Mujahid din da yake ji.
Nan suka zauna suna tattauna maganar, cike da tausayi da al’ajabi.
A nutse na futo ina Jan jakar kayana.
Duk suka bini da kallo har shi uban gayyar.
Granny tace”ke ‘yar nan ina ce ba mun kashe magana ba, ya kuma na ganki da jakar kaya a hannu.”
Tsayuwa nayi bakin kofa babu yabo babu fallasa nace”Granny kiyi hakuri Don Allah, Umma babu lafiya zanje in kama mata aiki. Dama saboda mijinta baya gari ya sanya na zo, to tunda ya dawo zan tafi.”