BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Mimi ta k’araso gurina da sauri ta rike jakar kayan, tana fadin “Me ye haka Habbity.”?

Tab’e bakina nayi nace” Abunda kika gani sakar min don Allah in tafi gida haka.”
Rau-rau idonta yayi tace.” Please Asma’u wallahi in ina ganin ki cikin gidanan nafi walwala ina jin dad’i don Allah kar ki tafi.”

Mujahid ne ya k’araso kusa damu ya Dan bata fuskar sa tare da kallona cikin tuhuma yace.” Ya muka yi dake.”?

Marairaice fuska ta nayi cikin sigir shagwaba da han hankali nace.”My Jahid please Umma bata ji dad’i ba, zazzab’in nan da ake fama dashi, Yanzu ina shiga daki Ya Aminu ya kira ni a waya Dole ce ta sanya ni tafiya please. “

Jakar kayana ya rike yana kallonta kurr! Nasan sigar da nayi magana dashi ne yaja hankalinsa.
Murmushi nayi masa nace”Kayi hakuri kullum ai muna tare a waya ko.”?
Daga kansa yayi kamar wani yaro Karami.

Amjadu yana zaune a daining duk yana ganin abunda yake faruwa haushi duk ya k’umshi ganin yanda Mimi take rarrashin Asma’u tana bata hakuri amma tayi buris da ita.

Da kuzari a jikinsa ya mike gami da Isa inda suke tsaye, Mimi yazo ya kama ya rungume yana rarrashin, shifa yanzu duk wani Abu da zai b’ata mata rai bai so, sosai yake rarrashin ta.

Tace”Hobby kace da ita kar ta tafi.”
Kallona yayi da Jan ido ko bata fada masa ba yasan abunda zai sanya ta bar gidan
Yace.”wai ke dole sai da ita zaki iya rayuwa ne? Uhumm! Kinyi aure kina da ‘yan kin fita daraja ta ko wane fanni kike zubar da hawaye ki a banza ki daina wannan kuka kina ganin lafiya bata is he ki ba.”

Jahid ne yayi masa wani irin kallo yace.” Kalaman ka sunyi tsauri malam, itama Asma’u ta kusa shiga wannan sahu.”!! Yanda Jahid ya fad’i maganar ne ya tabbatar masa da cewar ransa ya b’aci
Dariya yayi kad’an Dan ya kara tun zura musu zuciya yace.” Ai ba karya bane sai ka bari idan ta hau wannan matakin kayi magana.”
Ni kam nan tsaya jin karshen maganar sa ba na futa da sauri domin idan na tsaya zuciya ta tana iya mutuwa saboda yadda nake jin bakin cikin bak’aken maganganun da yake tafka min

Bayan ta Mujahid ya bi da sauri ba tare da yayi musu sallama ba, wani irin tsaki Amjadu din yaja ya ja hannun Mimi dake kokarin mayar da hawayen ta suka koma parlor
Granny tace.” Ai yarinyar ma tayi kokari wallahi kam bana ganin laifin ta, ka shigo gida kamar wani mala’ika sai muzurai kake dole taji zaman gidan ya gundure ta.”
Ba tan ka mata ba ya ja hannun Mimi suka shige dakin shi shi da ita zuciyoyonsu duk babu dad’i
Shi kanshi bai so tafiyar yarinyar ba a wannan lokacin Zata d’ebewa Mimi kewa sosai.

Mujahid ne ya kaini har gida muka yi sallama dashi cikin so da kauna alk’awari yayi min zai zo a sati nan, sai sa motar shi ta bar gurin na ja jakar kayana na wuce gida

Umma na zaune a tsakar gida tana d’aurin kayan miya duk da dare ne amma yara sai shigowa siyan kalanzur suke yi, nayi sallama na gidan.

Cike da mamaki take kallona tace”Kece da daddaran nan.” ? Zama nayi kusa da ita INA fadin”Wallahi kuwa Umma ya dawo me gidan dama nagani da zama .” tace”Dama ba kyaso a tursasaki.”
‘Yar dariya nayi tace”Ya jikin Mimi INA fata da sauki kuma tana cin abunci.”

Jim! Nayi ina tunanin maganar Da Jahid yayi min a mota game da Mimi ni tsoron fadawa Umma nake yi saboda nasan halinta Yanzu zata tada hankalin ta.

Kallona tayi tace” Kinyi shuru.”?

“Umma jikinta da sauki Alhamdulilahi amma Jahid yace.” Dole ayi mata aiki fa.”!
Cikin fad’uwar gaba Umma ta aje farar ledar dake hannunta, tana kallona .
Nace”Wallahi haka yace domin hakan shine mafuta.
Take naga hawaye yana kokarin zubawa a idonta, muryar ta na rawa tace”Banji dadin wannan labarin ba Asma’u, nifa idan naji ance za’a yiwa mace me ciki aiki sai naga kamar mutuwa zata yi
Nace”Umma ki daina wannan tunanin insha Allahu Mimi zata sauka Lafiya .”
Shiru tay min tana goge hawaye. A fakaice.
Zuciya ta naji ta karya nima na meke da sauri jin hawaye yana kokarin zubo min mutukar nayi kuka a gaban Umma to itama kukan zata yi.
Dakinmu na shiga na tube kayan jikina yunwa nake ji sosai domin ban samu damar cin abunci da granny ta girka ba saboda fargaba.
Da d’aurin k’irji na futo nace”Umma Allah yasa da akwai ruwan zaki a Fula’s Wanka zanyi.” Ba tare da ta kalle ni ba tace”Da akwai cikin babban Fula’s din nan.”
Kicin na nufa da sauri na hada ruwan zafi a bokiti dauka nayi na shiga band’aki.


Tsanin azabar da Mimi ta sha a wannan daran ya d’agawa Amjadu hankali domin kuwa a zaune suka kwana Mimi rungume a jikinsa, kamar ranta zai futa rik’on shi kawai take ya YAFE mata. Saboda tausayin ta bai San sanda ya fara zurarar da hawaye ba, rungume ta yayi tsam!! A jikinsa yana tofa mata addu’oi. Sai daf da asubahi bacci ya dauke ta, shi kuwa dungurgur ya kwana a zaune yana kallonta sai da yaji kiran sallahr sannan ya mike toilet ya shiga yayi Wanka ya futo tsaf shirin massalaci yayi yazo ya tsaya kanta, bacci yaga tanayi sosai, cike da tausayi yake kallon fuskarta inda idonuwan ta suka zurma cuki
[11/22, 8:02 AM] BintuUmarAbbale: Ko da ya dawo daga massalaci Mimi bata tashi ba, bai tashe taba sai ya zauna kusa da ita hade da rik’o hannunta ya rike tam! Ya k’urawa fuskar ta ido, Cikin zuciyar sa ya jinjinawa mata da irin wahalar da suke sha yayi d’aukar ciki da haihuwa.
Ya minti talatin a zaune a gurun yana sakawa da kwancewa, kana ya mike ya dauko wayar sa yana kunnawa sakkoni suka dinga shigo wa Sam bai bi takan su ba, numbar Mujahid ya kira. Mujahid yace.” Gashinan zuwa gidan.
Kashe wayar sa yayi ya futo parlor lokacin granny ta futo tana kicin tana hada musu kalaci zama yayi a cikin kujera cike da damuwa.

Jahid yana shigowa ya ganshi a hargitse zama yayi kusa dashi ya bashi hannu suka gaisa, yace.”yana ga duk ka wani furgice ne.”?
Ajiyar zuciya Amjad ya sauke yace.” Jahid yanzu haka Momy take shan wahala jiya kwanan zaune muka yi na tausaya mata wallahi.”

Jahid yace.” Dole kam abun tausayi CE, dama abunda ya kama ta ayi mata kenan.” Ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu yace.” Da har na fara tunanin futa da ita waje a duba ta.”
Murmushi Jahid yayi yace.” Kar ka damu Aboki duk abunda kake tsammanin za’ayi mata k’asar waje insha Allahu zamu yi mata zan tsaya tsayin daka kan almarin ta kasan sai asibitin mu muna da likitoci k’wararru so kar ka damu.”

Gyada kansa yayi yace.” Yaushe za’ayi aikin.” ? Jahid yace.” Insha Allah ranar Monday za’ayi.” Saura kwana uku kenan.”? Jahid yace.” Eh saura kwana uku. ” OK Allah ya kaimu nagode K’warai. “

Nan granny ta futo daga kicin ta same su, suka gaisa da Mujahid cikin barkwanci sannan ya bar gidan
Amjad din ta kalla a nutse tace” Aishatu ta tashi ne.”? Girgiza kansa yayi kamar wani maraya.
Granny tace”Sai hakuri ka kwantar da hankalin ka naga kamar ka tada hankalin ka, insha Allah komai me wuce wa ne.” Shiru yayi mata kawai. Ita kuma ta wuce daining domin shirya kayan breakfast.


A gajiye na dawo daga makaranta na zube rumfar Umma cikin gajiya da ishirwa nace”Wallahi Umma da nasan zan sha wahala haka da ban dauki azimin nan ba, kinga yau juma’a anyi rana mutuka .”
Tace”Hakane ai zaki samu lada sosai. ” lumshe idona nayi kawai ishirwa Duk ta dame ni, so nake a idar da sallahr la’asar nayi wanka ko zanji dadin jikina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button