BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Tun kafin su karasa hospital din Jahid ya kira waya cewar su futo da gado ga emergency nan, aikuwa suna shiga ciki da sauri wasu mata ma’aikata suka turo gado na d’aukar marasa lafiya, ya bude motar da sauri ya zagayo ya budewa Amjad din dake ruk’unk’ume da Mimi dake cikin halin rai da rayuwa.
Futowa yayi ko kallonsu bai yi balle ya saurari abunda suke CE masa, Mimi na rungume a jikinsa ya wuce su. Dr Jahid ya bishi a baya, suna nurses din suka rufa musu baya da sauri.

Likitoci kusan biyar kan Mimi ciki kuwa har da Jahid din sun dukufa domin ceto rayuwar ta.

Yana zaune a reception ya hade fuskarsa da tafukan hannayen sa, kwata-kwata baya so ya bude idonsa ganin irin kallon da jama’ar gurin suke masa, wato yanzu ya zama abun kallo kenan? Tsoron sa d’aya kada Allah ya kawo ‘yan jarida gurin, yasan sai sun fed’e biri har hutsiyar ta.
Aikuwa Ko minti talatin bai yi da zama a gurin ba suka shiga su uku. Daya daga gidan redio daya daga gidan television daya kuma daga gidan jaridar Gaskiya dokin k’arfe
Kewaye shi sukayi suna gyara kayan aikin su, ya d’ago kanshi Yana kallon su da idanunsa wanda sukayi wani irin ja!! Babu fargaba a tare dasu tunda a kan aikin su suke .
Daya daga Cikin su yace.” Ranka ya dad’e me zaka ce game da zargin da mutane suke maka.”? Shiru yayi musu yana binsu da kallo
D’ayan yace.” Kuma muna son karin baya ni daga bakin ka, shin zargin da ake maka cewar ka had’a baki da yahudawa domin Ku tuzarta Allah da manzon shin hakane.”?
Amjadu yaji wani k’aton bakin ciki ya tokare masa a mak’ogwaro shiru yayi bai ce musu komai ba, kallonsu kawai yake kamar zautacce.! D’ayan da bai yi magana ba shine yace.” Ranka ya dade jama’ar gari sun ci alwashin sai sun kashe ka kan abunda ka aikata sai sun k’one gidan ka sai sun k’one company ka, sai sun kona ka, yanzu dai sun samu nasarar k’one company ka kurmus! Ta inda babu wani Abu da zaka Mora a cikinsa, abun mamaki da daure kai kuma sunyi zanga-zanga sun je har inda kake sun kasa aikata Abunda suka yi niyya, gashi kuma yanzu mungan ka a hospital cikin halin damuwa da d’imuwa ran ka ya Dade muna bukatar garin haske a gurin ka.

A jiyar zuciya ya sauke ya mike tsaye da sauri! Suka fara kara masa lasifikar su a bakin sa,
Sunkuyar da kansa yayi kasa hade da soka hannunwan shi duk biyun cikin aljihun wandon dake jikinshi yace.” Alhmdullahi Allah ne abun godiya a halin yanzu.” Shiru ya rasa gurin, ga ‘yan kallo duk sun nutsu
Ya cigaba da cewa”Ban yi niyyar magana daku ba amma dole tasa zan fad’i Abu guda akan wannan k’azafi da akai min, cewar ni Amjadu Abul Abbas zan tsaurara bunkice akan mutanan da suka shirya min wannan sharrin, mutukar na kama su, babu shakka dani dasu za muyi kare buri jini dasu, domin sai dai a dauki gawarsu ko a dauki tawa, ni Amjadu bana had’a Allah da ma’aiki da kowa, Wallahi wallahi sai dai idan na kashe su hukuma ta kashe ni, duk Wanda zai yi wasa da Allah da manzo to tabbata barin sa a ban duniya shirka CE,idan ban kashe su ba, I promise Sai na raunatasu! Sai na jikkatasu! Sai na sassab’a musu kamannii!!!!!, wannan shine magana ta.”!!!
Ya fada yayin da yake wata irin zabura!!!!
Dan jarida d’aya yace.” Ranka ya Dade shin baka jin ciwo da bakin ciki akan b’arnar da akai maka, gashi duka duka company ka ko shekara guda bai yi ba shin yake jin zuciyar ka a wannan lokacin.”?

Girgiza kansa yayi ba tare da wata damuwa ba yace.” Company na da suka k’ona bai min ciwo ba, da sun barshi ma ni da kaina zan zazzaga masa fetur in kona shi, saboda bashi da amfani a gurina, company da ya tara miyagu marasa tsoran Allah a ciki barinsa babban hadari ne, naji dad’i mutuka da suka kona shi. ” ya k’arasa maganar sa yana futo da hankici daga aljihunsa ya goge fuskarsa.

Daya Dan jarida ne yace.” Ranka ya Dade sai tambaya ta k’arshe kayi hakuri muna son muji me ya kawo ka asibiti gashi dai a zahiri jikinka babu ko kwarzane babu jini balle ace ko daga gurij mutanan da suka kai maka har……. Kafin ya karasa maganar shi ya katse shi ta hanyar fadin”My wife dina tana ciki cikin halin rai da rayuwa duk ta dalilin wannan ibtila’in babu abunda zan ce sai dai Allah Ubangji ya saka mata ga dukkanin mutanan da suka shirya faruwan hakan.””””””Yana gama maganar shi ya maida hannun sa fuskar sa ya rufe ruf! Yana kukan zuciya
Duk wani mai imani da tausayi a lokacin zai tausaya masa mata masu rauni tuni sun soma zubar da hawaye, jiki a sanyaye ‘yan jaridar suka masa sallama suka futa.

Dukanin abunda yake faruwa bamu da labari mun dai ji labarin yanda mutanan gari suka k’one company ya Aminu ya kawo mana video mun gani a wayar abokinsa garba har yanzu Umma kuka take yi tana tunanin wane irin hali Mimi take ciki dashi kanshi Amjadu din, domin da har ta dauki mayafi zata futa Ya Aminu ya hanata da sauri yaje ya kulle kofar waje da kwado domin rigima muke da ita wai sai ta futa taje gurin su Mimi.


Yana zaune a gurin shi kadai sai gilmawar nurses da d’aid’aikun marasa lafiya da suke shigowa asibitin.
A gogon hannunsa ya kalla K’arfe goma shaura, cikin tararrabi da tsinkewar zuciya ya mik’e tsaye yana kallon room din da aka shiga da Mimi ciki.
Kai tsaye ya durfafi d’akin baya ko kallon gabansa.
Karo suka buga da Jahid ya futo daga dakin hannunsa sanye sa safa, duk ta b’aci da jini.!! Wani kallo yayi masa yana bin hannunsa da kallo cikin fad’uwar gaba.!
Jahid ya gyara yanayin fuskar sa, cikin rashin kuzari yace.”tana bukatar jini cikin gaggawa.”!! Amjad kokari yake ya bangaje Jahid ya shiga dakin.
Jahid ya tare hanya cikin sigar rarrashi yace.” Colm down Aboki tsaya ka saurare ni tukkuna.” Cikin damuwa da fargaba yace.” Muje ka sanya mata nawa jinin kar Ku kashe min matana.”!!! Muryar shi na kyarma ya k’arashe maganar tasa.”

Jahid ya rike hannunsa ba tare da ya damu da jini da. Yake hannun nasa ba ya damk’e sosai yace.” A halin yanzu bani da masoyi sama da ita bani da kowa sai ita da abunda yake Cikin ta sai granny su kadai suka rage min a duniya my friend bana so in rasa Momyna.”!!!!! Tsabar tausayi ta hana Jahid cewa komai ya ja hannunsa suka shiga wani d’aki.

A gigice Ya Aminu ya shigo gidan Hannunsa rike da wayar Garba abokisa.
Kamar dai d’azu da ya shigo mana da ita, duk ya rasa inda zai tsoma ransa, ya mik’o min wayar bakinsa na kyarma yakasa cewa komai
Hannu na rawa na fara dubawa
Farko abunda na gani ya sani kurma wani ihu na jefar da wayar hanna hannu na d’ora aka ina fad’in “Innalila wa’ina ilahi raji’un, shikkenan sun kashe mana Mimi mu.”!!!!!!
Umma ta dauki wayar da sauri tana dubawa, Mimi ce rungume a hannun Amjadu lokacin da suka shiga asibitin nasarawa abunka da mutumin da yayi suna a duniya aka samu wasu suka dauke su vedio a wayoyin su, a lokacin suka fara turawa Media hade da sharhi cewa jama’ar gari sun shiga har gidan Young millionaire sun Sassari matar shi mai dauke da ciki Dan wata shida gashinan tana halin rai da rayuwa.!
Abunda ya k’ara tayar mana da hankali shine yanda mu ga jikin Mimi dashi kansa Amjadu din duk ya b’aci da jini duk da cewar dare ne amma akwai hasken fitulu a ko ina na asibitin.
Umma ta mik’e tsaye cikin tawakkali ta kalli Ya Aminu da yayi tsaye a gurin duk ya rasa me zai yi tace” Muje mu gani Aminu Mimi tata kaddarar kenan, bawa baya wucewa kaddarar sa, muje idan ta mutu ne sai mu karbo gawar ta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button