BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Hawaye Ya Aminu ya share ya futa daga gidan da sauri domin samo abun hawa.
Ni da Umma muka futa daga gidan kamar wasu zautattu! Shi kanshi hijab din dana sa a baibai na sanya shi, hawaye ne kawai yake zura ra a idona shikkenan Mimi sai ta Allah a yanda na ganta ina gani kamar kafin mu Isa a sibitin za’ace ta mutu.

24/11/2019
[11/25, 8:46 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

62

Lokacin da muka Isa asibitin goma da rabi ta wuce, Dan dai ma daran azimi ne akwai jama’a a bakin asibitin suna siye da siyarwa, har ciki mai a dai-dai ta sahun ya shiga damu, Ya Aminu ya biyashi kud’in sa, ni kam tuni na Dade da futowa daga a dai-dai sahun sai kyarma jikina yake yi.

Ko da muka shiga ciki babu mutane sosai wasu kujera muka samu muka zauna. Ya Aminu ya nufi wani d’aki da sauri.
Waya ta dake hannuna na kunna na fara Neman numbar Jahid, sai da na kira sau biyar a kashe, cikin mutuwar jiki na aje wayar a cinya ta, Ya Aminu ya futo daga dakin da ya shiga ya nufo mu, fuskar sa babu walwala
Gaban Umma ya tsaya yace. “Yanzu wata nurse take min bayani cewar Mimi tana ciki har yanzu ba’a futo da ita ba, kuma abun mamaki na dauka zamu samu mijin nata anan gurin bab…….. Kafin Ya Aminu ya rufe bakin sa, Jahid da Amjadu sun futo daga wani d’aki. Da sauri Jahid ya k’araso gurin mu. Shi kam Amjad yana tsaye a gurin da yake.
Jahid ya kalli Umma tare da fadin” Ashe har kun samu labari.”
Umma tace”Ba dole ba wannan tashin hankali dai Allah ya sawwake, mana shi, yanzu ya jikin Mimi yake. “!!?
Jahid yace.” Jikinta Alhmdullahi Umma ku kwantar da hankalin Ku, jini ake bukata sosai za’a kara mata saboda ta zubar da jini sakomakon fad’uwar da tayi.”

Mik’ewa nayi zumbur nace”Muje ka sa mata nawa jinin kaji Don Allah ka cece rayuwar ta.” Murya ta na rawa na k’arashe maganar.

Jahid yace.” Dole haka za’ayi muje a dauka a auna mu gani, idan yayi dai-dai sai a d’aura mata yanzu ma an d’ibi na Amjadu ne.”

Kallon shi nayi dake tsaye kamar wani maraya sai ya bani tausayi mutuka wata zuciyar tace ba abun tausayi bane mutumin nan.

Wani daki muka shiga da Jahid ya dauki jinina ya duba yayi dai-dai Dana Mimi take ya umarce ni na kwanta kan wani gado domin ya dauki jinin.

Amjad kuwa jingina yayi jikin bango hade da lumshe idonsa Sam ya kasa zuwa ma ya gaishe da Umma saboda halin masifar da yake ciki…..Muryar Granny yaji ta shigo gurin cikin kuka take fadin”Sai da tace kar ka futa kar ka futa ka futa gashi da ka futa ka dawo sumul k’alau! Da kai ita kuma saboda tsananin son da take maka, ta fadi kan cikin ta.”!
Komai a kunne magangan da granny take yi domin dakin da nake ciki a bude yake, Jahid na kalla Ina daga kwance nace “Nasan kasan dukanin abunda ya faru don Allah ka fad’a min komai.”?

Ba tare da tunanin komai ba Jahid yace.” Wallahi Asma’u tsautsayi ne ya afka kan Mimi lokacin da abun ya afku, tana hana Amjad din futa saboda jama’ar garin da suka kawo masa hari har gida, garin kokarin rik’o rigar sa, kawai santsi ya kwashe ta ta fad’i kan cikin ta to shine fa take ta zubda jini, amma insha Allahu zata dawo normal.
Murya ta a cunkushe nace”Kana nufin ya sane ya futa bayan tace masa kar ya futa yanzu me futar tashi ta jawo mana, ai dai gashinan da kunnen ka kaji Abunda kakar shi take fad’a ko.” ? Jahid ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin “Tsautsayi fa baya wuce ranar sa, don Allah mu bar maganar bana so Ku Dora alhakin abun kan shi.” Shiru nayi ganin ranshi ya b’aci Jahid yana da saukin kai da dad’in mu’amula amma baya son musu da taurin kai shiyasa nayi shiru kawai amma cikin zuciya ta nayi alk’awari sai na fad’awa guy nan magana a kan Mimi komai daran dad’ewa kawai don yaga tana da hakuri sai ya dunga gara ta kamar gare-gare kullum cikin damuwar sa, da bata mata rai.

Jini Leda biyu a kauda a jikina nan Jahid din yace min na kwanta kan gadon na huta mintuna talatin, INA kallon shi ya futa daga d’akin. Granny ce ta fad’o dakin tana kuka tana k’ara tisa maganar da abunda ya faru. Fad’i take “wannan yarinya Ubangiji Allah ya tashi kafad’unta amma babu shakka tana shan wahalar rayuwa. ” Shiru nayi mata kawai ina bin ta da kallo.
Amjadu masjid ya nufa domin yin sallah istigufari kawai yake a fili da Cikin zuciyarsa. Ta shi nayi jikina babu kuzari na futo daga dakin, har yanzu su Umma na zaune cikin sauraron hukuncin Ubangiji, kusan awa guda da shigar Jahid dakin da Mimi take ya futo, kallon mu yayi ya kalli a gogon hannunsa sha biyu na dare saura minti ashirin, futa yayi ya nufi gurin Amjad dake cikin mota
Amjad yace.” Ta farko ko.”? Daga kai Jahid yayi a hankali yace “Alhmdullahi ta farko kuma munyi nasarar tsayar da jinin insha Allahu an sanya mata, shi gobe dole za’ayi scanning din cikin domin ganin wane hali yake ciki.
Sunkuyar da kansa yayi cikin tawakalli yace.” Allah ya kaimu lafiya Jahid ina cikin halin damuwa ina bukatar rarrashin.” Kafadunsa ya dafa yana rarrashin sa da kalamai masu sanyi.
Amjadu Rambo ya sanya ya je can Mai takobi ya karb’o nau’i kan abunci da abun sha, duk ya sanya ya shiga dasu gurin mu, tsabar damuwa da fargaba bata bari munci komai ba, ko da asubah ruwa kawai muka sha fafur abunci yak’i samun shiga a gurin mu, Ya Aminu dama ya tafi gida ni da Umma ne kawai sai granny

Ko da muka yi sallahr asubah bamu koma ba, muna zaune daki daya muna jiran hukuncin ubangji, granny na zaune kan dadduma da carbi a hannu Umma na kwance gefan ta. Itama dai carbin ne a hannunta tana ja, cikin damuwa, ni kam ai fad’ar halin damuwar da nake ciki sai a hankali, a Dan baccin da ya kwashe ni ne nayi mafarkin gani ga Mimi a tsaye a wani gurin tana sanye da wasu fararan kaya duk jikinta fuskar ta dauke da wani irin annuri ta kara haske mutuka, hannu nake mik’a mata tana mik’o min NATA hannun tana min murmushi, so nake in kamo hannunta na kasa gani dai a kusa da ita amma na kasa kamo hannunta, gani nayi ta juya da sauri ba tare da tace min komai ba ta fara d’ago min hannunta kafin in Ankara na nema ta na rasa. Ni da kaina na fassarawa kaina wannan mafarkin tabbas Mimi zata yi nisa da rayuwar mu Mimi zata yi nisa damu. Shine fa tunda na tashi na kasa sukuni ina kwance kan wani k’aramin gado nayi lamo wasu irin hawaye masu zafi suna zubo min.


K’arfe bakwai dai-dai Jahid ya shigo a sibitin cikin mota ya tadda Amjad yana bacci a zaune ya bashi tausayi mutuka ya kalli su Rambo dake tsaye jikin motar yace.”Kar Wanda ya tashe shi Ku k’yale shi ya samu bacci shima Hutu ne. A gurin shi.”
Gyada kai suka yi alamun sun amsa.

Kai tsaye dakin da Mimi take ya nufa, lokacin mu bamu futo ba, shiyasa bamu ga zuwan shi ba, abun mamaki yana shiga dakin yaga nurses tsaye a kanta d’aya na goge mata baki daya na kokarin gyara gadon, yaji dadin yanda ya same ta, gaisawa yayi dasu, suka futa da sauri, shi kuma ya kalli Mimi fuskarsa a sake yace.” Madam ya jikin ki.”? A hankali tace”Da sauki.” Yace.” Me kike ji yana miki ciwo a jikin ki.”
Cikin ta ta nuna da hannunta.” Yace.” Kiyi hakuri zaji sauki insha Allahu.” Mimi ta gyda kanta, gurin yayi shiru na minti biyu dago kanta tayi, cikin sanyin murya tace”Sun kashe shi ko.”!!!? Jahid ya girgiza kansa alamar a’a saboda ya San ko wa take nufi…. Bude baki tayi zata yi magana yace.” Ko in kira miki shi ne.”? Gyada kanta tayi, ya mike da sauri ya futa, lokacin mun futo, muna zaune a wasu kujeru, granny ce ta tare shi tare da fadin”Kai Mujahid ka futo zigwi-zigwi ko kallon mu naka yi ba kun barmu cikin alhini da tashin hankali ko.”
Jahid shiru yayi mata kawai ya futa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button