BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Mik’ewa tayi tana gyara d’aurin zanin ta tace”Ku tashi mu shiga ciki muna da kafafunmu sai anyi mana iso Ku muje muga halin da take ciki baiwar Allah.”
Aikuwa bayan ta muka bi, ni da Umma. Mimi na zaune kan bed kanta a kasa hawaye na zurarowa a kuncin ta kuka take sosai, muka shiga, da sauri naje na rungume ta, tare da fashewa da kuka INA fadin “Mimi ALLAH ya saka miki dukanin Wanda ya cuce ki.” Rungume ni tayi tana kuka sosai.
Umma da granny suka k’araso gurin suna rarrashin mu, mussaman ita Mimi din. Zama nayi kusa da ita hannuna cikin NATA, Yanzu zuciya ta tayi sanyi sosai na yarda mafarki karya ne tun daga Mimi zaune a gaba muna magana da ita….. Dakin suka shigo hade da sallama. Tunda nayi masa kallo guda na dauke kaina ina mamakin yanda hallintun sa suka jurkita mutum Dan gaye Dan kwalisa mai kudi mai kyau mai jiji da kansa amma lokaci guda kamanin sa duk sun sauya ya fyade lokaci guda, fuskarsa Tayi fururu, shi kanshi takalimin dake k’afafun shi na wanka ne, kayan jikinsa ne kawai masu kyau.
Kai tsaye gurin Mimi ya nufa ya zauna kusa da ita inda bayana da nashi ya kusa haduwa sai nayi saurin mik’ewa daga gurin, na koma kusa da Umma na tsaya, shi da Mimi kallon juna suke yi sun kasa magana shine ma yayi k’arfin halin fadin “Momy ya jikin ki hope yanzu ba kyajin ko wane irin ciwo ko.”? Gyada kanta tayi har yanzu hawaye bai daina zuba mata ba.
Sosai yake rarrashin ta da kalamai masu dad’i ko kunyar Umma baya ji har sai da yaga ta saki tana dariya sannan ya daina shima ya saki jikinsa sosai ana hira dashi sama-sama shi da Umma granny na sanya musu baki.
Kimanin Rabin a wa yayi ya mike tare da fadin zai je gida yayi wanka zai dawo bayan sallahr azahar. Sallama yayi wa su Umma ni bishi da wani mugun kallo na tsana da kyama ji nake bani da babban makiyi a duniya karma shi saboda guy a fiye son kanshi a duniya.
Takardar scanning ta futa Dr Jahid ya shiga damuwa sosai da yaga abunda yake faruwa wato baby girl dake cikin Mimi ta juya ma’ana kwanciyar ta ta sauya daga inda ake bukata tana zaune daram! Cikin Mimi gashi cibiyar ta ta nade mata wuyan ta, amma tana rayuwa a haka Cikin hukuncin Allah, lafiyarta lau, cikin ya nuna wata shida da kwana takwas wato ya shiga wata na bakwai duk wasu hallitu ubangiji ya gama abun shi, wahudun kahar Dole ya kwantar da Mimi a asibiti domin kula da cikin ta da ranar haihuwa, domin kar hankalin su ya tashi ya sanya yak’i fada musu abunda yake faruwa ganin yanda duk suka saki jikinsu har shi Amjad din da ya dakatar da komai na rayuwar sa, yanzu ta lafiyar matar sa yake.
Ko da ya fada musu maganar bata gado basu kawo komai ba, har shi Amjad din ya yarda saboda Jahid din yace masa yana so Mimi ta samu cikkakiyar kulawa har ta haihu, shiyasa ya yarda da hakan.
Kwananmu bakwai a sibitin Mimi ta warware sosai babu inda bata zuwa, domiin Jahid cewa yayi muna futowa da ita tana zurga zurga saboda shi yana gani kafin lokacin haihuwar tata kwanciyar baby ya dawo dai-dai kamar yanda ake so.
Ganin ta warware sosai ya sanya na tafi gida saboda makaranta Mimi bata so tafiya ta ba amma da na rarrashe ta na kawo mata misalai sai ta hak’ura.
Umma da Granny ne suke jiyyar ta sai Ummansu Munnu dake zuwa kullum tana kawo musu abunci bayan an sha ruwa, duk da cewa Amjadu yana iya bakin kokari su akan su, komai sai ya sanya an kawo musu na ci da bukatar rayuwa.
Ni ma ina zuwa amma ba kullum ba, watarana idan muka taso daga makaranta ni da Munnu sai mu wuce aikuwa Mimi tayi ta murna, ranar yini muke ni da Munnu muna sanya ta motsa jikin ta, kamar yanda Jahid ya fada.
Yau sati na guda da barin asibiti Wanda yayi dai-dai da satin Mimi biyu a asibitin kuma yau sallahr saura kwana bakwai sati daya kenan. Ranar juma’a ne na tashi da wani irin mutuwar jiki. Naji bana son zuwa skull din, cikin sauri na shirya jikina na bar gidan, kai tsaye asibitin nasarawa na nufa, duk sunyi mamakin ganina lokacin makaranta nace musu yau baza ni ba, muna tsaka da hira Mimi ta mike ta shiga toilet din dake cikin dakin. Minti biyu naji ta kwalamin kira, da sauri na bude band’akin na shiga ina fadin”Menen….. Kafin in karasa naga jini jazur nabin kasan gurin gata a tsugune ta rike kan famfo na toliet din tana cije bakinta cikin azaba ta rike Cikin nata tana ynukurin tashi tsaye amma ta kasa
[11/25, 7:38 AM] BintuUmarAbbale: Hannun ta na rike ina kokarin mikar da ita tsaye abun ya gagara, babban abunda ya bani tsoro da ita shine yanda naga jini na zuba da sauri na fita na kira Umma ta shigo taga halin da ake ciki, itama hankalin ta ya tashi tace”Maza ki karawo Jahid din zubar jini na da matsala futa nayi da sauri kafafuna na rawa, Granny tana tambaya ta menene? Ko juyowa banyi ba, Ina kokarin shiga ofis din ne shi kuma yana kokarin futowa muka buga karo dashi, dauke kaina nayi daga kanshi ina kokarin shigewa, tunda ya ganta a d’amauce ya tabbatar akwai matsala da sauri ya fada dakin da Mimi take, dama zuwan shi kenan asibiti ya tsaya ofis din Jahid domin su gaisa, yana shiga yaga granny tsaye kofar toilet tana fadin”Kama ta Ku futo a hankali, kai amma dai jinin yayi yawa likita yazo ya duba ta.” Granny yake kokarin bugewa yana kutsa kai ban dakin inda Umma take kokarin mikar da Mimi ta kasa ko da d’aga k’afarta guda d’aya, da sauri ya mik’awa granny wayoyin shi ya tartare hannun rigar shi, ba tare da damuwar komai ba ya d’auki Mimi hankalin sa duk a tashe ya futo da ita jikinsa duk jini hakanan itama doguwar rigar dake jikinta sharkaf take da jini. Hannunta ta mik’a ta kamo wuyansa tana lumshe ido dishi-dishi take gani. Ya kwantar da ita da sauri ya futa daga dakin, Jahid da Asma’u ya ci karo dasu, sai yayi saurin koma wa dakin, shi kuwa Jahid ganin jikin Amjad din da jini ya tabbatar masa da akwai matsala, aikuwa suna shiga dakin suka tadda Mimi tana wani irin buge-buge kan bed din tana wani cije bakin ta ga idanunta sunyi sama sun k’afe fari tas!! Da su. Innalillahi wa’ina ilahi raji’un ” Shine Abunda Jahid ya fad’a ya futa daga dakin da saurin tsiya, mu kuwa rifuwa mukayi kanta Umma addu’a kawai take tofa mata, ni kam baki na ya kulle a lokacin kallon ta nake kurrum tana buge-buge na rasa wane taimako zanyi mata, a takaice ma da naji ina Neman fad’uwa sai na zube a gurin ina fad’in “Innalillahi wa’ina ilahi raji’un.” Amjad hannunta yake kokarin rikewa abun ya faskara domin yau duk k’arfin sa Mimi yafi shi, kokarin fadowa take daga bed din yayi saurin tare ta ta fad’i jikin shi, har ila yau ba daina cije-cije da take ba.
Likitoci kusan biyar ne suka rufu a kan Mimi domin ceto rayuwar ta suma sun tsorata da al’amarin kuma yayi musu bazata lallai ubangji Shahidi ne kuma shine yasan gaibu kana taka Allah na tashi, duk iya bunkicen su a kan Mimi bai nuna musu wata alamar na cewa zata yi jijjiga ba, amma dake Allah Allah ne ya saukar da hukuncin sa kan baiwar shi, a war su biyu a kanta suna kokarin shawo kan Matsalar da tsayar da jinin da yake zuba Abu ya fassakara, Wanda a wannan lokacin Mimi ta amsa kiran Ubangji dukanin su sun tsorata mutuka duk da suke likitoci suna ganin irin wannan tashin hankali amma al’amarin Mimi ya girgiza su, Dr Faruk ya lura cikin na na motsi take suka shirya yi mata CS domin a Ciro abunda yake Cikin tunda da ran shi.
Jahid daure wa yake akeyin aikin dashi, zuciyar sa nacan tunanin ya za’ayi ya Sanar da Amjadu wannan mummunan labarin. Cikin hukuncin Allah suka samu nasarar ciro baby girl ‘yar wattani bakwai ba sati d’aya, yarinyar ‘yar mitsitsya da ita, tana cikin koshin lafiya take suka sanya ta Cikin kwalabar su, da aka tana da domin irin su, suka kimtsa gawar Mimi , cike da alhini da tausayi suka futo
Da Amjad suka yi karo tsaye a kofar dakin dasu ke, Jahid yaji gaban shi na fad’uwa, hannunsa yaja suka shiga ofis din sa.
Amajad yace.” Jikina na bani bazan ji alkairi ba daga gare ka, kawai ka fad’a min menene? Domin fuskar ka ta nuna alamun damuwa.” Babu wani kwane-kwane da b’oye-b’oye domin dole ya Sanar dashi hakkin shi, yace.” Allah yayi wa Mimi rasuw….. Kafin ya karasa ya d’aga masa hannu da saurin! Yace.” Kar ka k’arasa min naji.”!!!!!!! Jahid ya mike daga inda yake ya zauna kusa dashi da kalamai masu taushi yace.” Ubangji shine ya hallice ta a sanda yaso babu tsammani kuma a karb’i abunsa a sanda yaso kar ka manta dani da kai duk zamu je inda Mimi taje komai daran dad’ewa mutuwa riga CE, aya ce ga dukanin wani musulmi Mimi tayi sha hada ta mutu ta farkin haihuwa addu’a zaka yi mata.”!!
Hannun Jahid ya rike tamau! Leb’anshi na rawa haka zalika jikin shi na wani irin tsuma yace.” Innalillahi wa’ina ilahi raji’un. “!!!!!!!!! Jahid ya dinga dukan kafad’un shi alamun rarrashin yana tausar zuciyarsa da kalamai masu sanyi, d’ago idonsa yayi Wanda suka zama kamar Jan gauta bakin shi na rawa yace.” Muje a shirya min gawar Momyna ayi mata suttura.”!!
Jahid ya mike tare da shi suka futa kai tsaye dakin dasu ke aje gawarwaki suka nufa, tuni an daure Mimi guri guda tana kwance sambal kan wani siririn gado an lullub’e ta da wani farin zani, fuskar ta ya bude, yaga tayi kyau sai murmushi take kamar yayi mata magana ta amsa, zubewa yayi jikin gado yana sakin wani irin kuka. Tare da fad’in”Momyna Allah ya jikan ki, halin ki nagari ya biki, Momyna na hafe miki insha Allahu kece Uwar gida na a aljannar Fiddausi.”!