BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Jahid na tsaye yana kallon shi cike da tausayi da alhini, mik’ewa yayi hade da sanya tafukan hannayen shi ya shafe fuskar shi, ya kalli Jahid din a dake yace.” Muje.” Jahid ya bishi a baya suka futa.
Ko da ya shigo dakin da muke bai yadda ya had’a ido da kowa ba yace.” Zamu je gida yanzu Jahid ya bamu sallama.”
Granny da Umma ba yara bane balle maganar sa ta shige su Granny tace”Kai k’ato bana son kumbiya-kumbiya kawai ka fad’a ma kome yi mu ‘yan Adam ne zamu dauki kaddara rufewar bata da amfani, shin ya jikin Aishatu ne.”? Yana kokarin futa yace.” Allah ya amshi ta.” Wani irin ihu! Na kurma had’e da bin bayan sa a guje, ina kokarin taddashi tafiyar mu ba d’aya bace ina kuka nake fad’in”Karya kake mugu azzalimi sai dai idan Kaine ka kashe mana ita, idan hakan ta kasance sai na dauki fansa.”!!!!!!! Ko juyowa bai ba, ya shiga wani daki, kokarin binsa nake wasu nurses suka rirrike ni suna bani hakuri, wani k’arfi ne ya zo min a lokacin na fuzge daga jikin su sai kace wata mai iskokai na afka dakin a guje! Abunda na gani ya sani jin wani irin jiri tuni na fad’i a gurin ina kallonsu dishi-dishi inda suke kokarin Dora mimi kan wani gado Duk an dad’adaure mata k’afafunta da hannaye ta babu Wanda yabi ta kaina harshi kanshi Jahid din suka tura Mimi dake kwance kan Wani k’arfe suka futa.
Silalewa nayi na fad’i a gurin ba tare dana San a wace duniyar nake ciki ba.
Tuni Umma da Granny sun futa sun tsaitsaya aka futo da gawar Mimi tare da sanya ta a motar asibiti Umma sai share hawaye take yi, suka shiga, dravar yaja motar, lokacin kowa ya manta dani sai Jahid din da ya dawo ta kaina shine duk yayi min taimakon su na likitoci na dawo hayyacina kuka sosai nake yi had’e da dukan shi kamar mahaukaci nake cewa an hada baki dashi an kashe min Mimi, ganin kamar bata cikin hankalin ta ya sanya yayi mata allura take bacci me nauyi yayi gaba da ni.
Wasu nurses ya sanya suka shigar masa da ita mota, ya bar asibitin cikin halin damuwa da tashin hankali, Kamar gawa a ka shiga dani cikin gidan Amjadu inda ya cika da Jama’a maza da mata lokacin tuni an shirya gawar Mimi an futo da ita, saboda haka Jahid kawai ya tsaya nan aka sallace shi da ita, shine a gefe Amjad din a gafe suka dauki makarar dukanin su zuciyoyin su babu dad’i amma dai komai ubangji ya saukar kan bawan shi ne dai-dai.
25/11/2019
[11/26, 9:20 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
MALLAKAR_ BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI
63
Mutuwar Mimi ta girgiza zuk’atan Al’umma bamu kad’ai ba hatta da masu gadin gidan sai da suka ji a mutuwar a jikin su, Jama’a kuwa daga ko ina b’arkowa suke yi ta’aziyya wasu kuma gulma ce take kawo su, domin ‘yan jarida sun ruga sun gama wa tsawa duniya cewa mutuwar mayar Young millionaire tana da nasaba ne da harin da jama’ar gari suka kai masa, wa ‘yanda basu San yayi aure ba suka dinga mamaki shine suke zuwa zaman makoki, mai girma governor Sarkin kano duk dasu akai sadakar uku, su mai citta ma duk dasu babu tsoron Allah ko na kwabo a tare dasu, a fili sun nunawa Amjadu kara a zuciyarsu kuwa murna suke yi sosai, shi kuwa governor abun ne ya soma bashi tsoro ganin yanda yazo zaman sa na k’arshe jama’ar gari na raka shi da dutsina suna fadin “Ba mayi.”!!! Kuma tunda ga mutuwar Mimi jama’a suka fara gane cewa harda sa hannun governor akan sharrin da akai wa Amjdin, ranar a tsorace ya bar kofar gidan Amjad ganin yanda matasa suke jifansa kamar ba governor ba, sai da jami’an tsaro suka fara sakin harbi sannan kowa yq shifa taitayin sa, Umma kuwa jin irin zantukan da jama’ar gari suke yi kan mutuwar Mimi yasa tace” Suyi hakuri kar su bata wa Mimi gawa kawai Allah ya amshi abunsa lokacin da yaso.
Yau kwanan Mimi bakwai a karkashin k’asa, na fige na tsigale sai Umma tayi da gaske nake cin abinci kullum ina zaune zukud’inm! Ko kuma in tafi dakin ta in kwanta kam bed dinta hade da rungume wani k’aramin hoton mu, dake cikin frem a kan drowr gefan gado ta aje shi, kuka nake yi sosai, Umma granny dashi kanshi Uban gayya naga duk sun saki jikinsu har hira suke yi suci abunci hankali kwance kuma suyi dariya, ni kadai ce nake cikin halin damuwa da bakin cikin rashin Mimi, tsakanina dashi kallone domun tunda Mimi ta mutum magana ta fatar baki bata hada mu dashi yau kwanakinmu bakwai kenan a cikin gidan shi, ya sake sosai yayi wanka ya shirya harda fesa turare sai abun yayi ta bani mamaki ina zargin sa, dama ya fi son Mimi ta mutu ya cigaba da tsula tsiyarsa take wata irin tsanar sa ta cika min zuciya ta.
Jahid kullum yana kirana a waya sai dai Sam bana sakewa dashi domin gani nake yi kamar bakin su da daya da Amjad din, matar shi Hafsa me kirki da ita duk a gama zaman makokin INA lura da ita da yanda take satar kallona a fakaice.
Babu kuzari a jikina na futo daga dakin Mimi hannuna rike da k’aramin hoton mu, kusa da Umma na zaune a hankali nace”Umma zaman me muke yi a gidan nan? Wallahi nagaji gani nake kamar Mimi zata dawo gwara mu tafi.” Umma tace”Eh dama yau kam zamu tafi tunda an share makoki, muna jira maigidan ya futo ne zamu je duba baby insha Allah daga asibitin sai mu wuce gida.” Granny tace”Habadai Ku kuwa ai sai kace Wanda ake kora kwabari kuyi sati biyu mana in baza Ku bari ayi ar’bain ba, har yanzu fa ana zuwa gaisuwa.” Umma tace”Tafiyar tamu ta dole CE Hajiya ni kaina a takure nake a gidanan wallahi, kiyi hakuri duk Wanda zai mun gaisuwa ya same ni a gida.” Granny tace”To Allah dai ya gafartawa wannan yarinya.
Tsaf ya futo Cikin dogayen kaya,na lura tunda akayi mutuwar nan bai sanya k’ananun kaya ba, k’amshin sa ne ya cika parlor ya tsaya bakin kofar shi yana gyara links dinshi, saurin kauda kaina nayi daga kanshi ina jan tsaki kasa-kasa wallahi wani mugun haushin sa nake ji. Umma tace”Ka futo kenan.”? A hankali yace.” Eh Umma Ku tashi muje yanzu, amma naji kuna wata magana ko.” ? Umma tace”Eh kam yau zamu tafi gida.” Yace.” Umma kuyi hakuri ayi sadakar ar’abain mana.” Umma tace”Bazai yiwu ba, INA da uziri Asma’u kuma makaranta zamana a gidanan bashi zai dawo da Mimi ba.” Yace.” Hakane Umma shikkenan Allah yasa ka da alkairi. ” mik’e wa Nayi da sauri na bar gurin, hijab dina na dauko dama tunda nazo kayan Mimi nake amfani dasu, Umma ko granny ce ta dauko mata wasu sabbin atampopi super take sanya wa yanzu daya daga cikinsu a jikin ta, Granny ta mike tana fadin “Baza Ku barni a baya ba, muje inga ‘yar yarinya cikin kwalba.”
Aikuwa ko da sukaje Asibitin fafur likitoci suka hana su shiga ganin baby Aisha yarinyar da Ubanta yayi mata huduba da sunan mahaifiyar ta, shi kam ai dactors din sun San shi farin sani dolen su suke kyaleshi ya shiga yaga babynshi kullum baya iya bacci sai yaje ya ganta haka kazalika kullum kara kaunar yarinyar yake Cikin zuciyar sa, yarinyar kamar su daya da uwarta sai dai ta kwaso hasken fatar shi, fara ce sosai, Amjad kam yafi Mimi haske nesa ba kusa ba, Alhmdullahi tana samun kulawa sosai daga gurin dactors ta fara k’wari da girma jikinta ya fara murjewa tana rayuwa cikin kwalba cikin hukunci ubangji.
Babu yanda muka iya haka muka hakura amma naji babu dad’i a zuciya ta domin naso inga baby nan wallahi ga yanda naji ubanta na fadin kamar si daya da Mimi, Jahid nayi ta kira a waya yak’i dauka saboda yasan zancan dokar asibitin CE, yana ganin kan Asma’u ba zai sanya ya karya ba.
Amjad har gida ya kaimu Cikin motarsa, zuciya babu dad’i na futo daga motar ba tare da na jira su Umma da aunt Hauwa ba, barin su nayi tare dashi suna sallama, Ya Aminu ne kawai a gidan dama yasan da dawowar mu tunda aunt Hauwa tayi masa waya tsaf muka tadda gidan, rumfa na zube kan leda na fara kuka.
Suka shigo suka same ni a haka aunt tace”Wannan wane irin shirme ne.” ? Cikin kuka nace”Aunt don baki San yanda nake ji bane a zuciya wallahi Ashe duk gujewa mutuwa da muke yi akan Mimi tana jika aunt Mimi tasha wahala a rayuwar ta wallahi” aunt tace”Sai hakuri dukanin mai rai mamaci ne addu’a kawai zamu yi mata.”
Ya Aminu ya shigo dakin yana fadin”Wannan kukan da kike yi kina kara mata azaba ne idan ta fado miki a rai kiyi mata addu’a. ” shiru kawai nayi musu.