BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Ko da na koma makaranta ba wani sake ba, kullum muna tare da Munnu muna zancan Mimi da halayen ta na hakuri da ban dariyar ta da saurin kukan ta wani lokacin idan na tuno hae sai na share hawaye sai kawai inyi mata addu’a samun rahamar Allah.
Kullum kuwa sai na damu Umma da zancan babyn Mimi nace ta nemi alfarma gurin Amjad ta dauko ta ta raine ta kamar yanda ta raini Mimi, Umma tace wannan kuma nice zanyi hidima tunda nice mamanta a yanzu, nan na dauki a niyar fad’awa Mujahid kudirina kan Baby Aisha, yarinyar da ta zama cikkakiyar mutum domin yanzu tayi k’wari sosai ta cika wataninta na haihuwa, Jahid yace.” Zai fad’awa mahaifin ta ko zai amunce, dama ya karb’i babyn sa, yau kwana uku kenan, jin abunda Jahid din yace sai ya d’aga min hankali Ashe har sun bashi baby babu labari mu gamu a zaune kullum muna kwadayin ganinta, to yanzu da ya karb’a wa ya kaiwa? Ni kadai nake tambayar kaina, ina dawowa daga makaranta na fad’awa Umma halin da ake ciki, tace “Aikuwa bai kyauta mana ba, muma ai muna da hakki a kanta, gashi kwana biyu ya daina kiran Aminu a waya balle kusan halin da ake ciki.” Nace”Umma to yanzu wa zai kaiwa babyn ma.” Umma tace “Kakarshi mana.” Shiru na minti biyu nace “Umma kakarshi bata da k’wari don Allah ki amunce a dauko ta.” Umma tace”Ai dama bani naki amincewa mutukar zai bamu muna so hakkin sa ne.” Nace “Nayiwa Jahid magana zai nemi alfarma a gurin shi.” “”””
Rayuwa kenan duniya babu tabbas yau kwanan Mimi Hamsin da bakwai a karkashin kasa komai yayi farko yana da k’arshe Amjad ya sake ya barwa Allah komai ya tabbatar dukanin Abunda ya same shi daga Allah ne.
A halin yanzu ya maida hankalin sa ne gurin k’ara bunk’asa harkokinsa na waje, a cewar sa mu’amula da turawa yanzu ya fara saboda wasun su sun fi muslumin mu amana da tausayi, tunda gashi da Dan uwanshi musulmi aka hada baki dashi gurin cutar shi da izgilanci ga Allah ga manzon sa, yana nan ya sanya matakan tsaro ko ta ina yayi lamfu bunkice yake sosai aka mutanan da suka kulla masa sharri, maganar company kuma tunda sun rusa shi babu wasu kudinsa da zai futo dasu ya saka tada wani, suje kawai Wanda bai ji bari ba zai ji hoho.. Loptop ce a kan cinyar shi yana duba sakkonin da Anthony ya turo mishi tsawon lokuta dama wasu ya bashi amsa wasu bai bashi ba, ya bari ne in yaje can sai suyi maganar. Granny CE ta futo daga dakin ta ta zauna kusa dashi.. Hankalinsa na kan Loptop din bai dago ba yace.” Ina Sweetheart yau banji motsin ta ba.” Granny tace”Tana gurun Iyami tun safe da tayi mata wanka take bacci.” Dariya yayi yace.” Wannan Aishar ai rigamammiya ce tafi uwarta fitina.” Granny tace”Mai suna Aisha kuka ne da ita ai.” Yace.” Granny ina tunanin cikin satin nan Zan tafi Chana kuma zan kai wata uku a can insha Allah, amma ina tunanin tafiya in barku fa.”
Granny tace”Allah ya taimaka ni kam babu wata chana da zan biki to kaji.”!! Dariya yayi yace.” Shikkenan zamu je da sweetheart d’ina OK.” Hararshi tayi tace”Kaje ka bawa wa ita wannan garin ai ku da ku ga zaku iya zuwa.” Murmushi yayi kawai ya cigaba da duba lptop d’insa.
A hankali tace”Ni ko nace dama akwai wata magana da na yanke a kanka.” Gyada kansa yayi tare da fadin”Ina sauraren ki.” Tace”Mai zai hana ka nemi auran Hafsatu. Da zan ce ko yarinyar nan Asma’u to amma naga wannan yaron Dan albarka Mujahid yana nemanta ana barin halas Dan kunya ko ba haka ba ne.”? Bata fuska yayi had’e da ya mutse ta yace.”granny ki k’yaleni in huta tukkuna ni kam yanzu babu maganar aure a gurina sai an kwana biyu sannan. ” Tace”Aikuwa dole kayi aure domin shine cikar mutum ka kai munzali kace baza kayi aure ba, baka Isa ba.”
‘Yar dariya yayi yace.” Granny nayi aure har na samu riba mutuwa ta rabani da mata ta, ki k’yale ni na huta tukkuna zanyi amma ba yanzu ba.” Tace.” Ni kam bazan ta kallon ka a haka ba dole ni nayi maka aure. ” dariya yake yana mamakin rigimar ta, yace.” Ok kiyi min aure sai in barki da matar wallahi inyi tafiya ta tunda bani na saki ba.” Granny ta hau zuba masa masifa, dafe kansa yayi yace.” Ina aiki kin hani oh my god.”!!! Iyami ce ta shigo da Baby Aisha a goye a bayanta tana motsi, alamun ta tashi. Granny tace” Ta tashi ne.”? Iyami tace”Gashinan fa da alama Dadynta take so.” Rufe loptp din yayi yana kokarin karb’a baby daga hannun granny sai murmushi yake, yarinya tayi mulmul da ita tayi wata irin kib’a hasken fatarta ya kara futowa Iyami ta iya raino gaskiya sai wani kamshi take yi, tana cikin kayansu na jira jira abun gwanin sha’awa, leb’anshi ya manna a kumcinta yana sakin ajiyar zuciya yace.” Momyna ‘yar rigima hummmm! Yau ba kuka kenan. “? Kamar yana da magana da babban mutum haka yake yin magana da baby Aisha.
Granny tace”Aiki ya same ka kana magana kamar kana magana da babban mutum.” Dariya yayi hade da kamo bakin baby yana Dan tsotsa yarinyar ta fara mamular leb’an shi da sauri.
‘Yar dariya yayi ya cire bakinsa ya kalli Iyami dake zaune kusa da granny yace.” Allah Iyami zanci tarar ki sweet heart dina yunwa take ji ga alamu nan na gani.” Iyami tace”Afuwa Uban gida dama yanzu nake so in dama mata madarar ta, kaga ai bacci take kuma sweeh Hart din naka ci ne da ita Wallahi .” Dariya ya kyalkyale dashi jin yanda Iyami take fadi wai sweeh hart. Yace.” Ungo ta ki bata bana so tayi kuka yanzu dai kin San halinta.” Iyami ta karb’e ta da sauri ta futa…… Wayar shi tayi k’ara yana dubawa yaga Jahid ne, murmushi yayi hade da daga wayar sallama yayi Jahid yace.” Kana gida ne.” ?
“Eh ina Gida yanzu amma k’arfe biyar dai-dai zanje government house.” Jahid yace.” OK ganinan zuwa nima ina Gida kasan yau Sunday muna Hutu. ” Amjad yace.” OK sai ka shigo din.” Kashe wayar yayi ya cigaba da abunda yake yi.
Minti goma tsakani sai ga Jahid ya shigo parlor yana zama yace.” Ina baby Aysha take.” Amjad ya rufe loptop tare da fad’in”Tana gurin me raino yanzu kuwa ta dauke ta suka bar gurinan granny ma yanzu ta tashi.” Jahid yayi Dariya tare da fadin “Babu wasa cikin al’amarin muna so ka bamu baby Aysha fa.”” ! Amjad yace.” Ai gatanan ga kanan Aboki baby Aysha taku ce kai da Madam.” Jahid yace.” Thank you my friend, wallahi Asma’u ce tun jiya ta dame ni lallai a basu ita shine nace zanyi maka magana nasan dai baza ka hana ba.” Tunda ya ambaci sunan Asma’u ranshi ya b’aci don har sai da fuskarsa ta nuna ya kalli Jahid din babu alamun wasa a tare dashi yace.” Babu wannan maganar my friend babu Wanda zan iya bawa sweet heart gaskiyar magana.” Jahid yace.” Kuma yanzu kace ka bani ita.”
“Yes Ni nace na baka ita saboda nasan muna tare da Kai har abada, naji ka sanyo min zancan wata Asma’u ne, am sorry my friend Asma’u bata da haleyan K’warai Wanda zata iya tarbiyan tar da d’an wani. Bana jin Zan iya bari baby Aysha ta yini a gidansu ma balle har ta kaita ga kwana gudun ta d’auko d’abiun yarinyar.” Jahid ya sha kunnu mutuka yace.” Kayi dai-dai Asma’u kake ciwa fuska a gabana ko.”? Dariya Amjadu ya sanya tare da fad’in”Sorry halin ta ne fa, amma da baka yimin wannan maganar ba ni babu ruwana.” Jahid ya bude hannunsa dake kan kafad’un sa yace.” Wato kana nufin matar da zan aura bata da tarbiya ko me.”? Hannu Amjad ya d’aga cikin sigar bada hakuri fuskarsa da murmushi yace.” Ban fad’i haka ba my friend…………………….