BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

26/11/2019
[11/27, 4:45 PM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
MALLAKAR_ BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI
65
Cikin fad’uwar gaba na mik’e zaune sosai ina k’ara duba wayar tabbas shine ya kira ni. Cikin zuciyata nace to me zai ce min lallai ma, kin d’agawa nayi har ra katse wani kiran ya k’ara shigowa ina kallon wayar nan ma ta katse band’aga ba, sai da ya kira sau uku nak’i dagawa sannan ya hak’ura, kwanciya nayi ina sak’e-sak’e a zuciya ta, data ta kara kunnawa aikuwa sak’on shi na farko hannuna na rawa na shiga ina dubawa. Ga Abunda yace.
“Maganar ki gaskiya ne ‘yan mata, Sweetheart bata da wani dangi sai ku domin kune iyayen ta, Abunda na kasa fahimta a maganar da kika ce duk D’an halal ba ya mance alkairi, shin wane alkairi kuka yi min da har na manta? Bayan nan kuma ina so in k’ara jaddada miki cewar Aysha d’iya tace domin nine k’ashin bayan Samar da ita, dukanin Ku baku da iko akanta, ni nake da iko akan kaya ta, so bana son damuwa don Allah daga yau sai yau karki kara yi min magana makamamciyar wannan, ina fatan kin fahimta? Kin turo min Jahid kan bukatar ki, to baki isa ba indai nine uban Aysha bazan tab’a Bari ki raine ta ba ballanta ki koya mata munanan d’abi’un ki, tabbas yanzu na tabbatar da cewa a baya nayi wauta da nake kokarin rabuwa da mace tagari a kanki , na tabbata Mimi alkairi ce a rayuwa ta, kuma duk macan da zan aura sai dai tabi bayanta wallahi,a halin da ake ciki yanzu soyayyar ta ta cika min zuciyata duk da bata Raye, ta inda nake yi wa mata kallon maza ciki kuwa har dake, saboda haka ki kiyaye fad’a min magana ko wace iri ce,ni Amjadu AbulAbbas ma nasara na shafe ki a babin rayuwa ta.”
~AMJD ABUL ABBAS~
Wani irin gumi ne yake tsiyaya a jikina take wasu zafaffan hawaye suka kece min, Dana San wad’annan mugayen maganganun guy nan zai fad’a mun da ban mishi magana ba, hannuna na karkarwa nake bashi amsa….. Da sauri na tura masa, na kashe data hade da jefar da wayar kan Katifa na rungume filo ina tik’ar kuka harda sharb’e majina,wato ni guy nan yake nunawa iyaka ta kan abunda Mimi ta tafi ta bari gashi Ubangji ya zuba min kauna da son baby Aysha a cikin raina, nafi awa guda ina kuka k’asa kasa don kar Umma taji fa kyar na rarrashi kaina tare da alk’awarin cewar bazan kara shiga harkar shi ba har a bada..Data na k’ara kunnuwa ina tunanin zanga sak’on shi domin nasan na fad’a masa bak’aken maganganu Wanda suka fi nashi abun mamaki, ko da na duba sai naga yayi bloking d’ina, sak’on Dana tura masa Yanan yanda yake, ajiye wayar nayi ina da na sanin bud’e whatsp din inda nasan wannan bakin cikin zan riske, da kyar bacci ya dauke ni mai cike da mafarkin baby Aysha da Mahaifiyar ta.
Ko dana tashi da safe sukuku na tashi jikina duk babu kuzari har Umma ta fahimci wan Abu amma bata ce min komai ba, saboda tana tunanin a jizanci ne irin na d’an Adam, sallama nayi mata na tafi makaranta. To ko A skull din ma kasa b’oyewa Munnu nayi sai da na fad’a mata komai kuma na nuna mata text din da ya turo min, Munnu ta dinga mamaki tsabar haushi da takaici yasa ta dinga zaginsa hotonan baby take dubawa sosai tana fad’in”Wallahi karya yake in Ku ya rabaku da ita mu bai isaba sai munje mu daukota Wallahi munganta ai wannan rashin imani ne ace kamar jinin Mimi sai dai mu ganta a hoto gaskiya bai isa ba.”!! Yanda Munnu take masifa sai ya bani dariya nace”Munnu ni da zaki bi ta tawa da mun hak’ura wallahi duk son ki da baby baki kaini ba, amma na hak’ura na bar masa kayan sa kamar yanda ya fad’a d’in, nasan duk daran dadewa baby zata neme mu.” Munnu tace”Ai sai munje har gidan mun ganta wallahi hakkin mu, dole zan hurawa Babanmu waya muje tare.” Shuru nayi mata ita kuma ta hau tura hoton baby a wayar ta.
Amjadu kuwa ranar da yaje amsa kiran da me girma governor yayi masa basu kwashe da dad’i ba, domin wasu zantukan banza yake masa wai yaga jama’ar gari suna zargin sa kan harda sa hannunsa kan afkuwar abunda ya faru, ya kama rantse-rantse yana fad’in kwata-kwata bai San zancan ba, don haka yayi hakuri kar ya kulle CE shi kuma a matsayin sa na shugaba insha Allah zai sanya a tsaurara bunkice domin gano wadanda suka aikata haka.” Kallon shashasha Amjad din yake masa domin ya ma kasa cewa dashi komai kawai ya mike zai bar gurin, governor yadawo dashi, cikin sigar rarrashi yace.” Sai magana ta biyu cewar nayi maka alk’awari insha Allah wannan kujerar tawa Kaine zaka maye gurbin ta, tunda na lura jama’ar gari na sonka zamu had’a baki dakai muyi murdiya ga Wanda yaji zab’e zaka tsaya takara a jam’iyya ta, sai milki ya dawo hannuna.” Amjad yaji kamar ta kwakwkwad’a masa Mari lallai shaye-shayen da yake yi ya soma tab’a masa kwakwalwa da har yake tunanin dashi zaiyi wannan aiki.
Kallon banza Amjad yayi masa yace.” Idan ina sha’awar mulki kai! Baka isa ka sanya ni nayi ba, lokacin da zaka ji ni a duk jam’iyyar da nake so zakayi mamaki so wannan Ba damuwar ka bace tawa ce, maganar zaka tsaurara binkice kan mutanan da suka shirya wannan sharri gami da yin izgili ga Allah da manzon sa, wannan bai dame ni ba, saboda ni nasan ko su waye kar ka bawa kanka wahala kuma zan dauki mataki a Kansu.”!! Tebur din gaban shi ya buga da k’arfi! Ya mike tsaye hade da fad’in”Na barka lafiya.” Futa yayi cikin yanayin tafiyar shi, ta gwarazan maza.
Governor ya bishi da kallon mamaki! Wato duk inda yake tsammanin yaron ya wuce nan, lallai su Alhaji Hashimu mai citta sun shirya masa sakiyar da babu ruwa ya tabbata da babu wannan maganar a kasa, zai iya Jan ra’ayin yaron ya karb’i takarar governor kano a jam’iyyar su, domin ya tabbatar Da babu abunda zai hanashi ya lashe zab’e saboda kaunar da jama’ar gari suke masa, shi kuma tanan sai yayi amfani da damar shi, shiru yayi yana tunanin mutukar ya sauka daga kan mulki kashin sa ya bushe zai tabbata bashi da tsunsu bashi da tarko.
Tsaf ya fito cikin shiri, granny da Iyami na zaune a parlor suna hira, ya k’araso tsakiyar parlorn hannu ya mik’a ya dauki baby dake jikin granny a kwance sai wuntsin-wuntsil take, sama ya d’aga ta kamar yanda ya saba yi mata yana kyalkyala dariya itama na b’angale baki, yafi minti goma yana wasa da yarinyar sannan ya zauna da ita a jikinsa yana fad’in”Baby zanyi missing dinki fa….Granny don Allah Ku shirya mu tafi tare kinji. ” cikin shagwaba yayi maganar, granny tace”Kasan Allah babu inda zamu bika kai dai kaje kurrum Allah ya bada sa’a idan ka dawo ma ina so muje muga ‘yan uwa Chadi. ” yace.” Sai dai idan kin yarda mu tafi tare bayan nagama Abunda ya kaini sai mu wuce Chadi din ko ya kika ce.” Girgiza Kai tayi tana fad’in”Oh-oh!! Kaje dai ka dawo idan kuma kak’i kaini ai da k’afafuna sai in tafi ka dawo ka tadda bama nan.” Yace.” Ki Bari zamu je granny nasan halin don girman Allah kar ki d’aukar min Baby kuje wani guri.” Tsakaninsa da Allah yake maganar. Granny tace”Ikon Allah!! Yanzu ni kakewa gargad’i kan ‘yar ka K’ato! Lallai baka da ta ido!! Dariya yayi ya mike yana fad’in”Granny soyayyar sweetheart dina ta cika min zuciya ta shiyasa idona yake rufewa. ” romot din dake kusa da ita ta dauka ta jefe shi dashi, tace”Marakunya kawai, ni kam bana maka fatan samun matsala da duk matar da zaka aura nasan kam Aysha zaka iya sakin ta.” Babu wasa a fuskar shi yace.” Granny duk wacce zata zauna min da sweet heart lafiya ina maraba da ita, zaman lafiyar mu da ita ta so baby Aysha.” Granny da Iyami suka girgiza kai cikin mamaki