BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Iyami ya mik’awa baby din ya kalli agogon dake daure a hannunsa, Cikin nutsuwa yace.” Ni zan tafi sai munyi waya ko
“? Granny tace” Allah ya kiyaye hanya muna maka fatan alkairi,Iyami ma fatan alkairi take masa ya fuce daga parlor da sauri,baby ta bishi da kallo tana d’aga hannunwan ta, yarinyar sun saba sosai da baban ta.
Yana futa su Rambo suka rufa masa baya, kai tsaye airport suka kaishi sai da suka ga tashin jirgin su sannan suka bar gurin. Hade da yi masa fatan dawo wa lafiya.


Gurin Jahid naji cewar yayi tafiya sai ban nuna komai ba, ko da wasa ban fada masa abunda ya faru tsakanina dashi ba, haka muke tafiya dashi cike da kauna da kulawa kullum kuwa idan ya shiga gaida granny sai ya dauko min picture din baby ya turo min, mu yini muna kallonta ni da Umma.
Allah mai iko tsakanin Ya Aminu da Munnu soyayya ce mai k’arfi ta kullu shiyasa ma Munnu ta rage zuwa gidanmu a cewar ta wai kunyar Umma take ji,magar auran su ta kankama inda Baban su Munnu da Kawu Yunusa suka tsaida magana insha Allah wata uku za’a d’aura auransu tunda Ya Aminu ya yarda ta cigaba da makaranta a gidan shi, Kawu Yunusa da kansa yazo gidanmu ya karewa Umma zagi har dani sai da ya had’a ya dinga zaginmu da cin mutumci iri-iri wai tunda na ki auran Amjadu to in fito da miji a hada da Aminu ya fuskanci wannan yaron da yake Neman aurena Mujahid yaudara ta zaiyi tunda gashinan kullum sai yace zai turo magabatan sa a tsaida magana sai yak’i saboda haka inyi maza in futo da miji ko kuma Wallahi ya d’aura min aure da Musa tunda dama tuntuni shine ya fara cewa yana sona.” Ranar kuka ns yini ina yi ina samun chaji a waya ta ns kira Jahid din tare da fashe masa da kuka duk na kwashe Abunda yake faruwa na fada masa. Shima babu shiri ya je ya Sanar da mahaifin sa halin da ake ciki. Take Alhaji Auwalu yace.” Zai tura akai kud’in aure da sadaki. To ko da Jahid ya samu mahaifiyar sa da maganar tsalle tayi ta dire tace wallahi Sam! Bata yadda yaje ya auro ‘yar talakawa ba, domin baza ta tab’a had’a jinita da talakawa masu dattin hula ba, tsaf! Ta sanya akaje akayi mata bunkican su waye su Asma’u kai har gidan su sai Da tasa aka binkito mata. Aikuwa ita da Aminiyar ta suka shirya cikin shiga ta alfarma suka tafi gidan, Baban abunda ya tayar mata da hankali yanda taga wani k’aramin gida kamar akurki wai nan gidan Mujahid dinta zaije ya nemi aure salon ya zubar mata da mutumci da kima a fusace! Suka shiga gidan Momy Mujahid din ns karkada key dinta motar ta cikin izgili
Ina sunkuye bakin rijiya ina dauraye hijabai na, Umma kuma na cikin rumfa tana d’aurin sukari hira baby Aysha muke yi da ita kawai naji wani mugun kamshi ya bak’unci hancina sawun tafiya naji na kalli kofar shigowa da sauri, wasu hamshakan mata ne suka shigo cikin ya tsine fuska sukayi sallama, na d’ago Cikin nutsuwa nake amsa musu, Hajiya Fatima ta kalleni ya a mutse tace”Da’alama kece “Asma’u ko.”? Babu walwala a tare dani nace” Nice.” Kallon banza tayi min ta wani ya mutse fuskar ta had’e da tofar da miyau! “She is ugly girl!!.” Ta fad’a tana kallon Momyn Jahid dake bin tsakar Gidanmu da kallo kamar Wanda take Neman wani Abu…. Wani irin tsinkewar zuciya naji lokacin da tafad’i min wannan Kalmar kallo nake binsu dashi cikin mamaki!! Momy Jahid ta kalleni a wulakance tace”Ke! Ina uwarki kwad’ayyaya gurun ta nazo ni.” Umms ta futo tana fad’in “Asma’u ke da waye ne.”? Cikin takaici da jin haushi nace “Umma wad’annan sakarkarun matan ne suka shigo mana gida babu sallama ko wacce tana fama ra karnin bleecing sune har suke kiran wani da mummuna.”! Momy Jahid ta kawo min wani bahagon mari tare da fadin” Ke don ubanki kin San kuwa ni wacece a gari nan. “? Kaucewa nayi da sauri ina fadin ” Sanin ko ke wacece bai dame ni ba nasan dai ke macace mara tarbiyya mace mai izgil…… Kafin in karasa Umma ta gwab’e min bakina tare da fad’in”Asma’u baki da hankali ko.”? Nace. ” Umma kin….. Tsawa tw buga min tare da fadin”,wallahi in bakiyi shiru ba ranki zai b’aci a gurina.”!!Momy Mujahid tace “Ki k’yaleta ta zageni da kyau! Nagode Allah da ya nuna min halin ki tun kafin Dana ya aure ki dama jama’ar gari na fadin haka a kanki,to bari kuji gargadi na daku da babban murya tun wuri Ku janye jikin Ku domin har indai nice mahaifiyar Mujahid wallahi bazai aure ki ba bazan hada jini da talakawa fakirai irin Ku ba, mutsiyata kawai.”

Mamaki ne ya lullub’e ni jin Ashe da da mahaifiyar Jahid nake magana naji tsoro da kunya sosai amma lokaci guda naji wata irin muguwar tsanar matar domin a rayuwata na tsani masu kudi marasa kaunar talaka ya rab’e su. Cikin daki na shige cike da takaici a fili nace “Wallahi kinci darajar Mujahid ne kawai.” Ashe taji duk da k’asa kasa nayi maganar aikuwa naji tana fad’in”Da kin sani kin dake ni kamar yanda kikayi NIYYA marakunyar yarinya kawai. ” Umma kuwa hakuri kawai take basu Hajiya Fatima ta daka mata wata irin tsawa “Dallah rufe mana baki.”? Umma ta rike hab’a cike da mamaki! Hajiya Fatima ta cigaba Da cewa” DUk laifin naki ne ai hausawa suka ce ido na mudu ba yasan k’ima, in banda abunki ina mu INA Ku kwadayi ne ya rud’e ku kuma kinyi a banza domin dai d’anmu bazai auri yarinyar Ku ba.” Umma taji zafin maganar da Hajiya Fatima ta fad’a to dake kowa na da nashi hankalin, sai ta share kawai tace “Shi aure nufi ne daga Allah idan Mujahid shine mijin Asma’u babu mahalukin da ya isa ya hana, idan kuma bashi bane Allah ne masa ni don haka Ku kwantar da hankalin Ku.”

Momy Jahid ta Ciro d’aurarrun kudi cikin jakar ta dauri uku ta watsa ma Umma a jiki cikin izgili tace”Ki tofar da bakin miyau na bakin ki domun kinyi sab’o Wallahi Mujahid bazai auri yarki ba mutukar ina Raye. “!!! A fusace taja hannun Hjy Fatima suka futa daga gidan.
Umma ta shigo inda nake tana fad’in” Ikon Allah Ashe haka wasu masu kud’in suke? Ashe mahaifiyar Mujahid bata da kirki shikam yaron kirki dashi lallai albasa bata tayi halin ruwa ba.” Nace Umma ki k’yaleta badai Jahid ne bata so na aura tom ni. Kuma sai na aure shi sai inga ya zata yi.”!

Umma tac”A’a ni bana yi miki sha’awar auran shi tunda uwarsa bata so ko anyi anyi auran ma to ba dad’i zakiji ba, kowa ya shaida cewar matar shi mutuniyar kirki ce kingani ke babu Matsalar kishiya tunda ta amunce ko ka bata amunce mijinta ya aure ki ba tom Allah da manzon sa, sun hallasta amma gaskiya matar nan ta bani tsoro.” Nace”Umma ki kwantar da hankalin ki, kamar yanda kika fad’a cewa aure nufi ne na ubangiji to ni ina nan kan bakana Wallahi babu gudu babu ja da baya sai dai in Jahid din ne yace ya janye maganar aure na tom sai in hak’ura. ” Umma tace “To Allah ya zab’a abunda yafi alkairi dai.” Amin nace zuciyata duk babu dad’i.

Kuka sosai Momyn tasa take da kyar ya shawo kanta tayi shiru yace.” Ki fada min ko menene Mommy” Tace”Wai ni yau ka kajawo wa zagi a gurin wadanda basu isa ba, Mujahid yau matar da kake Neman auranta ta zage ni ta kirani karuwa wai mai bleecing sai ta kara fashewa da kuka sosai har da dafe kanta.” Jahid ya sunkuyar da kansa cike da mamaki anya kuwa Asma’u zata iya zagin Momyn sa kamar yanda ta fad’a to wai ma shin a ina suka had’u da juna ne.?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button