BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Girgiza kaina nayi ina tunanin abunda zanyi na huce takaicin abunda guy nan yake min aka ‘yar Mimi wai ni yake kira da mayya lallai duniya. Ji nayi wasu hawaye na kokarin zubo min. Cikin zuciya ta nace zaka cigaba da kirana da wannan sunan indai akan baby ne. Nafi maye ma maita!
Umma taji dadin ganin baby sosai ta karbe ta ta rungume ta sosai a jikinta tana kallon Munnu tace”Ki bar min ita ta kwana a gurina gobe sai ki zo ki dauke ta ki kaita can gidan NAKU.” Munnu tace”To Shikkenan, haka tayi mana sallama cike da jin kunyar Umma.


Amjad Kuwa bayan futar Su Asma’u ne ya kira wayar granny domin ya ji gwalatun babyn shi dama baya minti ashirin bai kira waya ba, kawai granny tace masa wai su Asma’u sun zu sun tafi da ita, a lokacin ji yayi kamar ya bar Abunda yake yi ya dira najeria ya yaga yarinyar saboda rashin zuciyarta har granny ma sai da ta fuskanci b’acin ransa dama ta saba indai akan baby ne rufe ido yake yayi kamar bai San mutum ba shiyasa Iyami take takatsatsan dashi, kashe wayarta tayi ta k’yale shi shine fa ya kira Asma’u a waya ya sauke mata rashin mutumci, ya Riga ya saba da baby kullum kafin yayi bacci sai sunyi hira Sam bai ji dadin wannan Abu ba, Dan dai kawai yana ganin mutumcin Mutumin ne.


Kwata kwata na mance da rashin mutumcin da guy yayi min, hidimar baby kawai nake yi yini Abu daya. Don har gidan aunt Hauwa mukaje da ita wai lallai sai na bar mata ita naje bazan iya ba. Ko sallama banyi mata ba na futo daga gidan.

Misalin goma na dare na gama lallab’ata tayi bacci na bude data muna hira da Mujahid, kira ya shigo wayata, ina dubawa naga numbar k’asar waje ne sai nayi mamakin waye zai kirani da wannan numbar ne. Cikin sanyin murya nayi sallama, nashi b’angaran yaji wani irin fad’uwar gaba jin muryar ta da alamun bacci ta kashe masa jiki, gyaran murya yayi yana kokarin dai-dai ta nutsuwar shi, yace.” Ki duba na miki magana ta whstsap ki bani amsa yanzu.”! D’iff! Ya kashe wayar mik’ewa zaune nayi da sauri ina kara duba numbar, tabbas shine domin numbar irin ta d’azu ce da ya kira lokacin muna a dai-dai sahu. Messages na fara dubawa Aikuwa na ga nashi can k’asa, ni ban ma San sanda ya shigo ba, girgiza kaina nayi kawai na bude ina dubawa.

Ki turo min numbar wannan k’awar taki ina so muyi hira da Sweetheart

Abunda ya rubuta kenan. Na karanta ya Kai sau goma da gayya na kashe data ta ganin yana online nasan ni yake jira. Cikin rashin sa’a kuma Jahid ya kirani a waya ganin na rufe data yace.” Ko bace zakiyi ne naga kin rufe data gashi ni kuma ban gaji Da jin muryar ki ba.” Nace”Nima haka my Jahid muyi hira mai dad’i aikuwa muka dinga hiraramu ta soyayya

Amjad nashi b’angaran yana sauraron yaga ta turo masa da numbar Munnu kawai sai yaga ta rufe data kuma gashi ta ga sakon bashi,ranshi a b’ace ” ya fara kiran wayar ta a karo na biyu . wayar taki tafiya sai ace masa busy ya kira ya kai sau goma busy jifar da wayar yayi kan bed din da yake kwance yana Jan wani mutsiyacin tsaki tare da mamaki dawa take yin waya tsawon wannan lokacin……………………..

28/11/2019
[11/29, 9:22 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

67

Mun fi rabin awa muna hira da Jahid a waya sannan yayi min sallama tare da fad’in”My Wife insha Allah, kiyi bacci mai dad’i kuma kiyi mafarkin kina gidana da yardar Allah.” Cike da kulawa nace”Insha Allah Jahid zan kwana mana addu’a ni da kai.” Sosai yaji dadin kalamai na cike da farin ciki ya kashe wayar……Mik’ewa nayi nima na futa domin wani irin futsari ne ya kulle min Mara, tsakar gidan shuru Umma ta juma da yin bacci, ina dawo wa na tadda baby ta farka tana cilla k’afafu daukar ta nayi da sauri don kar tayi min kuka, ruwa na fara bata sha ina kokarin bata madarar ta naga ta zura k’aramin ya tsanta a baki tana tsotsa bacci ya dauke ta, ajiyar zuciya na sauke na gyara mata kwanciya na kwanta kusa da ita, bacci ya soma fizgata naji shigowar kira waya ta na manta ban kashe ba, idona a lumshe na dauki wayar ina dubawa tsaki naja kamar in kashe wayar sai kuma wata zuciyar tace dauki kiji me zai miki.” “Hello.” Abunda na fada kenan kamar me ciwon baki,, sama-sama naji shi yana fadin”Ke ni kika rainawa hankali na miki magana kin share ni, kuma na kira wayar ki kina waya Lokaci mai tsayi! Nace “Ki turo min numbar Munnubiya ko.” Kamar wani Ubana haka yake min magana da masifa! Cikin sigar kuntatawa nace”Ni fa duk ka dame da wani surutun ka, bani da numbar Munnu ko ina da ita ma bazan bayar ba, ba dai a kan ‘yar kake min wannan hayaniyar ba Tom sha kurumin ka baby Aysha na gurina yanzu ma ta farka daga bacci na bata ruwa tasha, ka cigaba da kirana mayya a kanta wallahi dad’i nake ji, maganar da wa nake waya bai dame ka ba, mutum na son yayi bacci an dame shi.”!! Kashe wayar nayi gaba ki d’ayan ta, wani irin sanyi naji cikin zuciyata na mayar masa da Martani Nasan yau da kyar in zai iya bacci.

Aikuwa sakato yayi da waya a hannu yana kallon abun kamar almara baby Aysha na hannun Asma’u wato duk kauce kaucen sa yarinyar nan sai da taje ta dauko mata sweetheart, yasan halin Asma’u farin sani bata munafurci yasan da gaske take, shifa yanzu babu wacce yake jin haushi sai granny domin yana ganin itace ta bada fuskar a dauko masa ‘yar sa, da kyar bacci ya dauke shi yana tunanin maganganun da Asma’u ta dankara masa. Abunda yafi tsaya masa a ransa shine tunanin da wa take waya, yasan dai idan da ‘yar uwarta mace take waya baza su kai kusan a wa guda ba, wata zuciyar tace masa ko Mujahid ne? Take ya yardar wa zuciyar sa shi din ne……. Cike da tunani. Ta da mafarkin sweetheart d’insa yayi bacci. Ko da safe ma da ya tashi babu kuzari a jikinsa har abokansa suka gane, nan yace musu baya jin dad’i ne kawai, yini yayi a kwance yana kewar gwalantun baby kuma yayi alk’awarin bazai k’ara kiranta a waya ba balle ta kara fada masa magana shifa Yanzu neman hanyar da zai yi nesa da ita yake saboda alak’arsu da Mujahid.

Da safe da kyar baby Aysha ta yarda da Umma lokacin da zan tafi skull ma sai Goya ta Umma tayi ta shige da ita daki don kar taga futata ko gilmawa ta ta gani zata fara zillo idan kuwa ban dauketa ba sai ta sanya kuka.

Koda muka had’u da Munnu a skull cewa tayi wai kunyar Umma take ji baza ta iya zuwa ta dauki baby ba, sai nace ta bari zan kawo ta insha Allahu. Bayan sallahr la’asar na fito tsaf dani baby na bayan Umma a goye ta sauko ta, ina kokarin sab’ata a kafad’a Umma tace”Ki Goya ta akwai sanyi- sanyi hadarin nan ya zama sanyi, towel din na karba na Goya ta sosai na saki hijab kana nayi wa Umma sallama, gidan su Munnu na nufa kai tsaye.


Ummansu Munnu tayi farin ciki sosai ta karb’i baby ta goya ta tam a bayan ta har sai da tayi bacci ta tashi sannan ta sakko da ita, tace ” Ya kamata a gwada bata abunci fa.” Dariya nayi nace”Ta isa cin abunci yanzu.”? Tace”Bari ki gani.” Wake ta Mirza ta sanya mata a baki Aikuwa baby ta lamushe ni da Munnu muka dinga dariya, Ummansu Munnu tace”Yaran yanzu da wayon su ake haifar su, gashi dai daga laluba mata wake ta lamushe, haka Ummansu Munnu tayi mata kusan sau biyar sannan ta k’yaleta ta bata ruwa, kuma Allah ya taimaka bata yi kuka ba, sai bayan magariba Babansu Munnu ya dawo gida, ya dauki baby Aysha yayi mata addu’a hade da sanya mata albarka yayi mata addu’a sosai da sosai kana ya sanya k’aramin yaron shi yaje kanti yayi mata siyayya sosai kalolin biscuits iri-iri Ummansu Munnu tayi ta dariya tana fad’in “Irin wannan siyayar akai wa kishiyata alhalin gani a zaune ba’a min ba, dadin abun dai cin abunci ma ni na koya mata.” Baban su Munnu yace.” Da kin sani Baki koya mata ba ai.” Mudai dariya kurrum muke musu, hira muke da Munnu sosai wacce ta dauke min hankalina sai da Ummansu Munnu ta leko dakin tana fad’in “Asma’u ko anan zaki kwana ne ga hadari nan yana had’owa.” Agogo na kallah da sauri naga tara shaura da sauri na mike INA fad’in “A’a wallahi Yanzu zan tafi.” Baby na dauke wacce ta Dade da yin bacci na Goya ta da sauri na zura hijab na fito wani bakin hadari na gani a gabas Nace”Munnu Allah ya kiyaye ni da dukan ruwa.” Tace “ameen dai amma ni shawara ta ki bari sai gobe kawai kya tafi.” Ko kallonta banyi ba nayi hanyar futa ina sallama da Ummansu dake Uwar daki.
Ina futowa titi aka fara wata irin iska mai k’arfi abubuwan hawa sai gudu suke akan titi duk yawanci motocin gida ne da kyar na samu a d’an sahu Wanda ya rage mutum d’aya a ciki na shiga aikuwa kamar almara ruwa ya kece kamar da bakin kwarya,ni da nake gefe ruwa ya fara duka na, kafin kice me na jike jagab, ta karewa nayi ina tsoran kar ruwa ya taba baby sai ta fara motsi tana k’ananun kuka, gaba na ya fad’i jijjigata nake yi INA so tayi shiru yarinya kamar wacce ake zugawa ga feshin ruwa sai dukan fuskata yake, kamar zanyi kuka nace “Don Allah kayi sauri babyna na Kuka.”! Mai dai-dai ta yace.” Hajiya ai ina ganin parking ma zanyi saboda ban San iya inda ruwan zai tsaya ba, domin karfinsa yayi yawa sai ya tsagaita sai mu tafi.” Kafin ince komai ya tsayar da ‘Dan sahunsa, nace”Na shiga uku ni Asma’u nayi da na sani tawowa da na hak’ura na zauna na kwana gidansu Munnu zai fi min, tausayin baby nake ji jin yadda take sakin ajiyar zuciya tana baya sai kyarmar sanyi jikinta yake yi, ni da ita duk mun jike matan dake a dai dai ta na kalla naga sai hirarasu suke yi babu abunda ya dame su, su kadai ne single babu wacce take da yaro Karami balle tayi fargaba. Sai da aka dauki 30minutes ana ruwa mai k’arfi sannan ya tsagaita sai wata irin iskar sanyi ta soma kadawa, a lokacin naji Baby ya fara atishawa sakkota nayi ina duba jikinta, naga jagab duk da dabarun da nayi mata sai da ta Nike hatta da gashin kanta, kuka take so tayi ta kasa sai sakin atishawa take, hawaye na fara sharewa kana na rungume ta tsam! A jikina Ina fadin”Duk nice na jawo miki babyna.”!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button