BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

29/11/2019

BABBAN YARO

MALLAKAR_BINTA UMAR

68

Yafi Rabin a wa a Zaune a gurin sannan ya mike Cikin mutuwar jiki ya shiga toilet alwala ya dauro ya fito yana hada hanya, dadduma ya shimfid’a ya fara sallahr nafila cike da Neman zabin Allah domin shu kanshi al’amarin sa tsoro yake bashi. Komai ya da gule masa lokaci guda, bayan yayi idar ya jima yana rokon Allah ya kawo masa dauki a rayuwar sa, yaji wani sanyi cikin zuciyar sa, kwanciya yayi kan daddumar bacci ya dauke shi mai nauyin gaske.
Ni kam bayan mun gama waya da Jahid tunani na fad’a mai tsayi zahiri dai gashi mahaifiyar shi ta nuna bata kaunata karara ko yanzu sai da ya kara fad’a min irin artabun da suke bugawa da ita kan Dole ya janye maganar saboda ta samu labarin kai kud’in da akayi a family lokacin da taje gidan buki suka dinga yi mata Allah ya sanya alkairi, sai abun yayi ta bata mamaki sai daga baya ta fahimta, shine tasa akai kiran sa, ta kare masa tanadi har tana ikirarin zata tsine masa in har bai janye maganar ba, duk yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta na lura Jahid idonshi ya rufe a kaina baya tsoron Abunda zai je ya dawo, dole in Sanar da Umma halin da ake ciki, yanzu jikina ya fara sanyi da al’amarin hak’ika ina son Jahid tsakani da Allah kuma bazan so ya fad’a cikin halaka ba, tunani na gwara ya hak’ura kawai domin ya samu albarka iyaye da wannan tunane-tunanen nayi bacci kwata-kwata na manta da Wani Amjad da damuwar shi. Da safe duk na warware wa Umma abunda yake faruwa tace”Asma’u dama ni tuntuni sai DW nace ki hak’ura da yaron nan tunda uwarsa bata so kika k’i, kuma kin san halin Kawun Ku ba kirki ne dashi Yanzu in wata magana ta sake faruwa zasu har gida su ci mun mutunci ne ki jawo tashin hankali ya kare a kaina da ban ji ba ban gani ba.” Shiru nayi wasu zafafan hawaye na zubo min duk ja rasa wane tunani ma zanyi.. Karar waya ta naji a dakinmu da sauri naje na dauko ina duba baby dake bacci cikin kwanciyar hankali, INA dubawa naga jahid din ne ya kira sallama nayi ya amsa murya babu dad’i ya Dora da fadin”Asma’u duk abunda kike ki aje don Allah ki mai da wa da mutumin nan yarinyar shi, wallahi yai shi ya tashe ni daga bacci dama ga shi da kyar na samu ya dauke ina fama da damuwa.”
Nima cikin damuwa nace”Jahid ka kwantar da hankalin ka dama yau nayi niyyar mai da ita saboda Umma tace a k’yaleta ne yasa saboda sanyi jiya amma insha Allahu yau zan mai da ita Nima na huta da jaraba.” Kashe wayar nayi a fusace! Ban saurari maganar shi ba. Hakan ce ta kasance bayan sallahr la’asar Munnu tazo gidanmu nan muka tafi domin mai Da baby kamar yanda nayiwa Jahid din alk’awari munnu tq kalleni cikin damuwa tace”Asma’u fyskar ki ta nuna alamun damuwa tabbas da Abunda yake damun ki.”! Girgiza kaina nayi nace”Tabbas Munnu abokin kuka shi ake gayawa mutuwa nan na kwashe duk abunda yake faruwa na fada mata har irin rashin kunyar da nayi Monye Jahid din sai da na fad’a mata. Munnu ta dinga mamaki daga bisani tace”Wallahi wasu masu kud’in haka d’abi’ar su take Sam basa son talaka kiri-kiri ta zo har gida ta ci muku mutumci saboda zubar da girma yanzu kuma idan mukayi aura kuka Tara zuria tace me? Da aure da mutuwa duk na Allah ne mutane ne basa ganewa wallahi.” Nace”Ke wace shawara kike gani.” Tace”Kawai ki cigaba da nan zabin Allah idan da Rabin auran Ku za’ayi dashi amma ko da wasa kar ki nuna masa kin karaya domun kinga shima yana daurewa gashi saboda ke ya bujerewa mahaifiyar sa.” Da wannan zancan muka isa. Babu walwala a tare damu muka shiga, Iyami da Granny na zaune a parlor kamar ko da yaushe ta amsa mana sallama a sake Iyami kuwada saurin ta ta k’araso gurin mu tana fadin “Oyoyo baby kokarin daukar ta take yi nayi saurin kwantota ta dauke ta tana cilla ta sama, yarinyar ta gane ta sai ta fara yi mata dariya. Zama mukayi a nutse muka gaisa da granny dake tambayar mu Umma nace” Tanan k’alau tace ma a gaishe ki da kyau kafin tazo.” Granny tace”Ina amsawa nima…Iyami kawo musu abunci.” Tafad’a tana kallon Iyami dake wasa da baby Granny ta karb’i baby ta nufi kicin, cikin zuciya ta nace yau kam baza muci abincin gidannan ba wallahi Mik’ewa nayi Munnu ta mike granny ta bimu da kallo tana fad’in”Za’a kawo muku abunci kun mik’e.” Nace”A koshe muke Wallahi.” Cikin nazari tace” kamar akwai abunda yake samun Ku kun shigo babu walwala kinji sakewa Lamar yanda kuka saba, yake kawai nayi nace”granny kenan babu komai wallahi mu dai mun tafi sai mun sake zagayo wa.” Hanyar futa muka nufa Abun kamaer almara babyta fashe da kuka tana d’ago hannun ta! Granny tace”To maza Ku dawo Ku tafi da ita gashinan tana kukan rabuwa da Ku
” gaba nayi cikin zuciyata nace yarinyar nan ko kukan me zata yi bai same ni ba wallah” Munnu CE ta koma da baya ni kuwa tuni na fuce da sauri, ina jiyo kukan ta har waje, ko da Munnu taje kin yarda tayi da ita sai kuka take yi Granny tace”Asma’u take nema ba ke ba. iyami ta kwalawa kira tana fadin “Bazan iya da wannan rigimar ba zo ki dauke ta yarinya k’arama da gane mutane.” Iyami ta shigo da sauri ta dauke ta tana rarrashin ta, Munnu tace “Asma’u baby ta gane ki sosai wallahi har nayi sha” awar Dadyn ta ya Baki tunda kuna kusa in Allah yayi nufin auran ki da Mujahid.” Murmushin takaici nayi nace”Munnu kenan, nasan ko mutuwa zanyi bazai bani ba, kar ki so kiji yanda nake jin zafi a zuciyata jin kukan da take yi.” Munnu tace”Allah ya kyauta masa amma gaskiya na lura guy nan ya sanja hali da ba haka yake ba.” “Hummm! Munnu kenan dole yayi abunda yake so tunda gonar sa a ka shiga kuma yana ganin ya wuce komai na rayuwa shiyasa.” Munnu tace”Wallahi maganar ki gaskiya ce Allah ya kyauta.” Nace “Ni Abunda yake damuna Abu daya ne aurana da Jahid wallahi yanzu abun tsoro yake bani ina jin tsoron abunda zanje in Tarar.”! Insha Allahu alkairi zaki yadda ke dai ki cigaba da yin addu’a.’a” nace “Nagode Munnu.” Da Wannan hirarar muka isa gida.


Amjad zaune a harami ya d’aga hannunwan sa sama sai kwararo addu’a yake, yana zubar da hawaye ni kaina ya mugun bani tausayi, ya kai Rabin awa cikin wannan halin kana ya shafa addu’ar ya mike a nutse ya dauki daddumar sa da glass d’insa dake aje a gefe ya nufi mazaunin sa, ko da ya isa ba zauna ba toilet ya nufa cikin kuzari yati wanka ya fito fes dashi kasamcewar ana zafi bai shafa mai ba, sai ya shafe jikinsa da turare ya sanya wasu ubansu parkinsan ash coulor hade da wata hula mai kamar net fara tasa da ita, takalmi mai gidan yatsa yayi amfani dashi ya d’aura tsaddan a gogon shi, kana ya manna farin tabarau din shi a fuskarshi, sai ya kara wani uban kyau, kasancewar ya Tara kasumba bai yi aski ba, sai abin ya bada sha’awa Amjadu ya saje da larabawan saudia domun duk kwakwar mutum bazai tab’a cewa ba balarabe bane ga yanayin fatarsa lufluf domin har tafi ta wani balaraben goge wa fuskarsa babu walwala a dauki wayoyin shi hade da wata k’aramar haka irin ta matafiya, kulle dakin yayi da key ya sauka k’asa. Amjad ya nufin koma wa gida Cikin iyalinsa bayan yaje dakin Allah yayi addu’a ga iyayen sa dashi kansa da sauran alumar musulmi.
Yana jirgi ya kira su Rambo ya Sanar musu gashinan kan hanya take suka wuce airport domin tarar sa, Granny ya kira a waya ya fada mata, tace”Amma kayi mana bazata! Mai kake so a girka ma.” ? Murmushi yayi yace.” Granny kuyi min Dambu da zogale.” Dariya tasa tana fadin “Kasamu k’ato Allah ya kawo ka Lafiya.” Kashe wayar tayi tana kiran Iyami. Tace” maza a shirya dambu mai kyau ga k’ato nan kam hanya.” Iyami tace”Wallahi baby ce take kuka har yanzu taki hak’ura kawai tana wasa sai ta fashe da kuka.” Dariya granny tasa tace”Tana tuno uwarta ne, jeki dauko min ita kije kiyi aikin ki.” Da sauri Iyami ta dauko baby dake kuka har da majina. Granny ta mik’a hannu tana son ta karbe ta ta make kafad’a wai baza ta zo ba, dariya tayi tana fadin”Kaga ja’ira dole kuwa komai kukan ki kiyi shiru Ubanki na kan hanya. Tace iyami aje ta kije kiyi aikin ki.” Iyami ta ajeta a kasan gurin ta nufi kicin da sauri. Lokacin baby ta tsandare da kuka, babu shiri granny ta dauke ta ta Goya Tana zagaye parlor da ita, Tunda ya doso kofar parlor yake jin kukan sweetheart dinshi yaji ranshi ya sosu da sauri ya shiga ciki hade da sallama k’asa_kasa granny ta amsa tana masa barka da zuwa, mamaki yake yi ganin baby a bayan granny a goye amma taba kuka, wayoyinsa ya zube kan teble din gaban shi ya fara kokarin daukar babyn da Granny take kokarin kwance ta, yace.” Wai mai akayi mata ne take kuka tun kafin na shigo nake jiyo ihun ta.” Granny tace”Sheganta ka ce kawai wallahi tun da taje gurun uwarta tayi kwana biyu Shikkenan ta dawo mana da rigima Don da kyar ma ta yarda da iyami, nu kuwa sai nayi da gaske nake daukar ta.” Ya gane inda maganar Granny ta dosa, zama yayi cikin kujera yana goge mata fuska da hakincin sa, yace”Granny nifa bana ganin laifin kowa sai naki ke da kika dauke ta kika basu.” Cike da jin haushi yayi maganar. Granny tace”To ka dawo ko zaka fara iyayin naka to me kake nufi iyayenta sunzo su dauke ta sai in hanasu ni kam ban iya wannan k’ek’e da k’ek’en ba irin naka.” Baice komai ba ya sanye leb’anshi na k’asa bakin ta, kamar yanda yake mata tana jin jira, aikuwa ta kama tsotsa yarinyar bata manta ba. Kallon ta yake yana jin wani irin tausayin ta cikin zuciyarsa duk sanda zai kalleta sai ya tuna masa da Wife dinshi Mimi ko da yaje Saudia duk Rabin addu’ar shi tata ce. Baby Aysha ta fara lumshe ido kalaman bacco still leb’anshi take tsotsa kad’an kad’an har bacci ya rinjayeta ta saki. Ajiyar zuciya ya sauke ya rungume ta tsam a jikinsa tare da fad’in”Iyami ta gyara mata gurin kwanciya tayi bacci.”! Granny ta bude baki zata kwalawa Iyami kira kamar yanda ta saba. Da sauri ya d’aga mata hannu yana yamutse fuska da ido ya nuna mata baby wai kar ta tashe ta. Tsaki granny yaja ta mike daga gurin. Da kanta taje ta gyara mata gurin kwanciya ta dawo zata karb’i ta kamar kurma haka ya zama Mik’ewa yayi ba tare da ya bata babyn ba ya nufi bedroom d’insa da Yarinyar granny tayi sakaro da baki, tana fad’in”On ni naga iyayi da feleke a ka dawo din zaka fara nuna mana iyakarmu ni da Iyami komai mukayi bamu iya ba hummm! Allah ya sawak’e maka.” Ni da Munnu ne zaune a Uwar dakin aunty Hauwa ta sanya muku tsuguna cikin wani dogon bokitin na k’arfe inda ta sanya wata k’aramar tukunyar k’asa da garwashin wuta had’e da wani mugun turare da wasu saiwowi masu wani irin kamshi, kullemu tayi a dakin har da Dan mukkuli, tsaki babu irin wannan banyi ba, a ganina ni budurwa CE ba bazawara ba, mai zasa aunty Hauwa ta dinga azabtar damu da turaran matsi kawai garin Neman gira a rasa ido, tunda akace saura kwana goma sha hudu d’aurin auranmu aunty hauwa ta sanya mu a gaba, domin har munnu ma da take surukar ta tace ita bata dauke ta a matsayin suruka ba, k’anwar tace duk abunda zata min zata yi mata, kuma bayan haka Si Dan uwanta take gyarawa Munnu tun tana jin kunya ta daina ji domin yau kwananmu uku a gidan aunt Hauwa tana yi mana izaya iri-iri, magani kullum ta dama da nono mai Dan iskan bauri da wani irin k’amshi kai hawa ka taje sai mun shanye tasa, wallahi ina daga tsigar jikina na Mik’ewa saboda yanayin dandanon sa a bakina babu dad’i bauri yaji zak’i d’aci duka, ranar dai da taba ni zubarwa nayi Munnu kuwa saboda kunya sai ta shanye tasa ta aje kofin ni kuwa kullum rigima muke da ita kan hakan. Yanzu ma Mik’ewa nayi da sauri jin wani Abu na zuba daga k’asa na, zani na nasaki na mai da pant dina. Munnu tace”Ya kika tashi ne.” Cikin b’acin rai nace”Munnu ke in zaki zauna zauna ki cigaba da azabtar da kanki kina budurwa ace wani Dole sai kin matse mtssss to wace irin katsewa kuma ake buk’ata. ” munnu tace “Don Allah ki koma ki zauna Wallahi tunda kikaga ta dage akanmu hakan yana da amfani.” Tsaki naja nace”Sai kiyi ke ni dai na gaji.” Kofa na nufa ina bugawa hade da kiran sunan aunt hauwa nace”kizo ki bude min zan shiga band’aki. ” bude min tayi taba fadin kiyi sauri ki fito kar maganin ya sane so nske ya bi jikin Ku sosai.” Hararata nayi ganin ta juya baya zumb’ura baki nayi na shiga band’akin ta dake parlor. Ina tsungawa naga ni bu mai yauki na dilala daga gabana, dama tun da aunt ta sanyamu a gaba nake jin wani azabbaban feelings na taso min. Ruwan zafi cikin wata butar.k’arfe na dauka na daureye gurin sosai sannan na fito raina duk babu dad’i

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button