BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

30/11/2019

BABAN YARO

*MALLAKAR BINTA UMAR

69

Shirye-shirye ta kowa wane fanni ya kammala Ya Aminu ya had’a lefe na gani na fad’a sosai Umma da aunt hauwa sukayi kokari a kansa, yanzu nawa lefan ake jira sai a fara Rabin goro kullum muna tare da Jahid a waya muna shirya tsarin buki da yanda zai kasance.

Momyn Mujahid ce take kai kawo a parlor ta takasa tsaye ta kasa zaune wato Mujahid ya yaudare ta ya rufe ta sun hada baki da ubanshi ya bujerawa bukatar ta, lallai ne ka haifi da a cikin ka ya wulakanta ka lallai zata nuna masa iyakarsa, yanzu ta sakko daga sama dalili shi mijin NATA ya kira ta tazo taga kayan lefa kuma saboda sun raina mata hankali wai itace zata nemi masu kaiwa don haka baram!_baram suka rabu da mijin nata ta sauko a fusace jiran zuwan Jahid din take domin tayi masa magana ta k’arshe kan auran.

Tunda ya shigo yaga tana kai kawo hankalinsa ya tashi yasan dole duk abunda yake b’oye wa ta sani, ko k’araso wa bata bari yayi ba ta karasa gurinsa a zafafe ta zabga masa mari Tana huci! Kamar zakanya tace”Ni zaka yaudara Jahid wato kun hada haki da ubanka kun rufe ni saboda baka dauke ni a bakin komai ba ko? Jahid yayi shiru hade da yin kasa da kansa. Ta cigaba da cewa “Wallahi in har nice na haifeka baza ka auri yarinyar da ta zageni ba, idan kuma kayi ganganinci auranta to babu shakka a ranar zaka sake ta ko kuma in d’aga maka nono don tsine maka zanyi wallahi tallahi kaji domin bazan yi kaffara ba.”!!! Ta k’arashe maganar tata a zafafe! Ya wani irin huci!
Jahid ya shiga cikin wani irin mugun yanayi a lokacin gumi ya dinga tsiyayar a jikinsa duk yanda yaso ya fahimtar da mahaifiyar sa al’amarin ta kasa fahimta. Wasu mazan sukan fuskanci matsala daga gurin matayen su a sanda zasu kara aure, shi daga gurin mahaifiyar shi ya fuskanci matsala. Mik’ewa yayi baya ko kallon gabansa, ya fita daga parlor. Wani irin kallo ta bishi dashi ta ta tabka wani irin tsaki, ta zauna kan kujera tana fadin” da in hada jini da talaka gwara duk abunda zai faru ya faru.

Jahid kuwa kai tsaye b’angaran Amjad ya nufa a lokacin hankalin sa a tashe! Granny na ganinsa cikin wannan halin ta tabbatar babu lafiya, zama yayi kan kujera hade da dafe kansa, granny Tace “Tabbas komai yayi tsanani maganin sa Allah, Mujahudu akwai damuwa a tattare da kai. Ya d’ago kansa yana kallonta, kawai sai taga hawaye a fuskar sa yana zubah, cikin mamaki tace” kafadamun damuwar ka Insha Allah zan taya ka da addu’a. ” Cikin karkarwar jiki ya warware mata dukanin abunda yake faruwa. Granny ta jima tana mamakin al’amarin daga bisani tace”Tabbas Hajiya Sa’a ta tabka babban kuskure, waye ya fada mata ana jayayya da al’amarin aure duk yanda bakason hada zuri’a da mutum idan Allah ya kaddara faruwan haka babu makawa sai ya faru idan tana tsananta kamar Yanzu Allah sai ya dauke ta ayi babu ita, tashi muje gurin ta.” Jahid ya mike da sauri ita kuma dauki hijab dinta ta zura, suna fita motar Amjad na shigowa gidan, yana kwance a bayan mota ya hango Jahid din da granny sun nufi motar sa, duk da cewa Jahud ya fahimce shine bai tsaya ba, da gudu ya fafari motar sumar bar gidan.. Shi kuma Amjad sai dinga tunanin ko wanine babu lafiya cikin iyalin Jahid din, ya dauki granny domin taje ta dubasu. Sam bai kawo komai cikin ranshi ba, ya shiga gida yanayin tozali da sweetheart dinshi ya manta da koma.

“Sosai granny take fahimtar da Momy amma ta gagara ganewa da k’arshe ma so tayi tai mata rashin kunya inda take fadin” Kinga Hajiya d’anki ko nawa da zaki dame ni lallai sai na yarda, shin kin Sam irin rashin mutumcin da yarinyar tayi min kuwa, tsinanniyar yarinya mummuna ‘yar gidan malam shehu irin wannan har ta kalle mu ni da aminyata tace muna warin dauka da bleecing a i wallahi Jahid ya sake ya auri yarinyar nan sai na tsinke masa.”

Granny tace"Ki daiyi hakuri Asma'u yarinyar arziki ce Wallahi akasi aka samu kuma hada zuria dasu akwai albarka Hajiya baki San ko akwai rabo tsakininsu ba, sai ki mutu saboda wannan abunda kikayi ubangji baya so." Jin abunda granny tace ne yasa Many zuburowa! Tace"kaji ni da tsohuwar najadu tsohuwar kawai! To wallahi sai dai idan kece zaki mutu,au!! Fatan mutuwa kike mun, aikin banza to wallahi ba yanzu zan mutu ba." Jahid ya Dora hannunsa aka cikin tsantsar tashin hankali da nadamar dauko granny inda yasan wannan cin mutumcin za'ayi mata da bai dauko ta ba, ya zama dole duk son da yake wa Asma'u ya hak'ura da ita, domin yana hango mugun rikici a gaba idan ya aure ta Hausawa suka ce idan so cuta ne hakuri magani ne, nan ya mike ya futa daga parlor a karo na biyu, granny ta mike cike da taikacin da b'acin rai tace"Duk yanda naso nussashe dake kin kasa ganewa har kina Neman kiyiwa danki baki, ni zagin da kikayi min bai dame ni ba, tunda kin kwatanta hali irin na Asma'u da kike cewa bata da tarbiyya Shikkenan na barki lafiya." Momy yaja tsaki da k'arfi tana fadin "Allah ya rakataki gona, nace Umma ta gaida Ayshaaaaas."! Granny ko juyowa batayi ba cike da takaici da damuwa ta samu Mujahid tsaye a gurin yana kiranta, mota ya bude mata ta shiga da sauri suka bar gidan. A hanyarsu ne granny take rarrashin sa da kalamai masu sanyi kana tace " Tunda mahaifiyar ka ta nuna bata so tom shawarar da zan baka ka hak'ura ka kwantar da hankalin guri guda rashin Asma'u ba zai hanaka rayuwa ba insha Allah zaka cigaba da rayuwa Cikin amincin Allah da yardar sa, idan Aure kake so ka sake samun mace wacce zucuyarka ta kwanta maka sai is aura mutukar ta amunce din, wannan shine shawara kayi wa uwarka biyayya." Amjad yace." Granny ban taba nadama akan al'amarin auran nan ba sai yau, da Momy ta ci miki mutumci kawai domin kina so ki fahimtar da ita, insha Allahu na hak'ura da Asmau amma INA Neman wata alfarma  agurun ki." Tace" kafad'a komeye insha Allah mutukar INA da iko dashi zanyi maka." Yace." Inaso al'amarin auran nan ya koma kan Amjad ba tare da sani ba inaso ne ranar d'aurin aure yaji bazata !."

Granny tace” hak’ika ka cika Aboki na gari Mujahid kuma idan kayi haka babu shakka ka kyauta min, domin ni kaina ina tunanin matar da zai je ya auro wacce zata kula da baby Aysha tsakani da Allah,Dole sai ita Asma’u da take a matsayin Uwa a gare ta, mungode mutuka da alkairi ka.” Jahud yace.” Granny Amjad yafi k’arfin komai a gurina wallahi.” Tace”Yanzu abun damuwar shine ita Asma’u kana ganin ba’a shiga hakkinta ba.”? Murmushi yayi yace.” Nasan inda zanyi da ita itama baza tasan abunda yake faruwa ba har a d’aura aure zanje cigaba da zuwa gurun ta babu abunda zan FASA, gefe guda kuma zan je na nemi Kawun ta mu kashe magana.” Granny tace”Kayi nufin alkairi Allah yayi maka jagora Kai kuma ubangiji Allah ya sanja maka mafi alkairi. ” murmushi yayi ya cigaba da driving har ya sauke ta gida ya wuce ofis din mahaifinsa domin ya Sanar dashi abunda ya yanke, to shima bai Wani jayyaya ba tunda dai Shi Jahid din yace ya hak’ura to shi meye bashi sai fatan alkairi yayi yace inda Allah zamu cigaba da shirye-shiryen d’aurin aure kamar yanda muka tsara, Cike da kwaran gwiwa Jahid ya nufi gurin Kawu Yunusa, duk abunda yaje faruwa ya Sanar dashi a bazata Kawu yaji al’amarin dad’i kamar ya kashe shi sai ya dinga shiwa Jahid albarka kamar me.”take ya shaidawa ‘yan uwansa suka soma shiri amma ya gargadesu da cewar bayaso maganar ta futa har Asma’u taji. Suka ja bakinsu suka yi shiru.

Duk wasu shirye-shiryen Jahid ya kammala su dai-dai da kayan da zasu sanya ranar d'aurin aure suna hannunsa hakanan kayan lefe na kece raini da ya yahadawa Asmay an kai kwanaki uku da suka wuce, shi ta b'angaran sa komai ya dai-dai ta. A zahiri ya nunawa Momy nsa ya janye maganar shiyasa ta saki ranta, kuma Mijin ta bai kara tayar mata da maganar ba sai ta yadda da maganar.

Saura kwanaki uku d’aurin aure aunt hauwa ta bude mans wuta kullum cikin durkar magani kullum INA kwana da ciwon ciki da wata muguwar Sha’awa Mara fasali sai in sanja pant sau uku a rana, maganar gyaran jiki ba’a cewa komai aunt Hauwa na da abokai iri-iri wata kawarta ce ta tsaya a kanmu ni da Munnu ta hado mana kayan gyara jiki kullum sai munyi dake aunt Hauwa ta iya hadawa sosai take samu a daki muna murje jikinmu bayan mun kama wani irin turare ne mai k’amshin tsiya shima zata sanya mun mulke sako da loko na jikinsu dashi sai munyi a wa daya tukkuna zamu wanke jikinmu tuni wani sihirtaccan kamshi ya kama fatar jikin mu, duk inda muka zauna sai kamshi ni kaina bala’in son k’amshin jikina, kullum muna tare da Jahid a waya, duk wasu k’awayenmu na nesa da na kusa mun gayyace d’aurin auramu, Alina sai wani shishshige min take Sam ban Wani saki jiki da ita ba duk sabgar buki da ita akeyi taki yin zuciya.

Ranar d’aurin aure

Amjad Jahid Khalid Ma’aruf suka futo cikin shiga iri daya shadda CE fara tas dinki babbar Riga da ‘yar ciki fad’ar tsadar shaddar bata lokaci ne, takalman su iri daya hulunsu irin daya agogonsu iri daya komai iri daya sukayi amfani dashi kamar yanda suka yi ranar d’aurin auran Amjad da Mimi mota suka shiga guda Khalid ne take draving har suka isa gurin d’aurin auran dake cike makil da jama’a take wani maroki ya saki wata shegiyar gangarsa ya fara wasa Amjad da fadin”Ango Na Asma’u sarauniyar mata gwarozo a cikin maza! Sai Amjadu! Hak’ika Wannan yarinya tayi dace da miji na nunawa sa’a fari mai farar aniya yaro mai halin manya gugan k’arfe sha kwarafniya gaba salamin baya salamun.!!!!!!!!! Jama’ar dake gurin suka dinga mamaki yaya ga ango kuma maroka na wasa abokin ango wai meye yake faruwa ne.”! Shi kuwa Amjad Sam! Bai Kawo komai cikin ransa ba, kawai dai yafi tunanin ko don yanayin sunansu daya sa Jahid din yasa marok’an suka kasa ganewa wanene angon a cikinsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button