BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Shiko Anthony ya dauka irin mutanan sa Wanda suka sanyo shi a gaba wato abokan a dawar sa, sai ya dafa kafad’ar sa yana rarrashin sa da kalamai masu sanyi.
Gyad’a kansa kurrum yake yana tunanin irin hukuncin da zai dauka kan yarinyar da shi kanshi guy…wani irin rad’ad’i da zugi zuciyarsa take masa in da yake jin kamar ya Dora hannu aka yayi ta kurma ihu ko ya samu sassauci,, cikin maza don rashin nutsuwa ko wane namiji yazo ya jata kamar tinkiya ta bishi tana murguda masa mazaunai hade da gantsaro masa nonuwa duk Rabin nonuwan ta a waje da ta d’aga hannu hammata a waje
Ya ilahi!! abunda ya fada kenan da mugun k’arfi, Anthony ya mike da sauri gami da bude kofar dakin ya futa.
Minti biyu ya dawo hannusa rike da wata bak’alar kwalba wani Abu mai kyali a saman ta, bude wa yayi da sauri ya mik’a masa, cikin harshen turanci yake fadin “karb’i ka sha wannan zaka ji sassauci a zuciyar ka.” Giya ce Anthony yake mik’a masa a zuciyarsa yace.” Asma’u bata Isa ta sashi ya fara shan giyaba ko da zuciyarsa zata yi bundiga sai da ya mutu da bakin cikin ta. Kauda kansa yayi yak’i karb’a, Anthony ya aje kwalbar giyar da sauri ya Ciro kwalin sigari hade da leghtar ya kunna guda ya mik’a masa, aikuwa da sauri ya karb’a ya fara bata huta, duk guda zuk’a biyu yake mata ya shanye, tas!! Ya shanye kwali guda Anthony ya mike da sauri ya futa domin dauka masa wata, shi zufa kawai yake lokaci guda yaji wani irin sanyi-sanyi a jikinshi alamun zazzab’i ya kama shi. Kwanciya yayi rigingine kan bed din yana sak’e-sak’e cikin zuciyarsa
Kwata-kwataKwata-kwata ma ni mantawa nayi da naga Rambo cikin jama’a na koma muka cigaba da sabgar mu, har lokacin da taro ya watse.
Ana kiran sallahr Magariba muka shiga gida, nida Mimi Yaya Aminu da Umma na tsaye da alama magana suke, kafin in an kara naji duka ko ta ina!! Ihu! Na kurma ina fadin “Yaya Aminu me nayi maka kake dukana.” Fad’i yake “Asma’u gwara in kashe kan inga abun kunyar da kike k’okarin jawo mana banje gurin party Ku ba, amma ina da labarin dukanin abunda ya faru so kike ki futa zakka a jikinmu Asma’u Ashe ‘yar iska ce ke ban sani ba,.”!!! Ya k’arashe maganar cikin tsananin b’acin rai!
Umma naga tayi shigewar ta daki ranta a bace babu abunda tace kan irin dukan da yake min, kuka na fashe dashi INA fadin” wallahi Allah ba zai barka ba sai ya saka mi… Wani irin mari ya galla min tare da fadin” a gidan uwarki sai ya hau dukana da kafafunsa ina karewa tare da fashe wa da kuka.
Mimi na tsaye tana kallonmu daman abunda take guda kenan shiyasa tun farko ta hanani, ganin yanda yaya Aminu yake dukana ne yasa Mimi shahada taje ta rungume ni sosai itama tana kuka tana tayani bashi hakuri, amma saboda rashin imani na Aminu ko kallonmu baiyi ba ya dinga duka yana fadin “Ai dama bakinku daya, wato ke mai tausayi ko? Asma’u zata Kai ki ta baro.!!! Sai da yayi mana lilis sannan ya kyalemu.
Da Jan jiki muka shiga dakinmu ko wacce tana shararar hawaye Mimi tace” Tun farko abunda na hango kenan, amma da yake kedin me taurin kan tsiyace kika ji, kika dinga shiga cikin maza saboda rashin kamun kai, wallahi Kiyi wa kanki fad…. Katse ta nayi a fusace.! Nace”Mimi kiyi min shiru ki k’yaleni inji da guda d’aya mana.””” Itama a fusace! Tace”bazan k’yale ki ba Wallahi ai dama gaskiya ce bakya so sai kije kiyi tayi.” Mik’ewa tayi ranta a bace ta fara cire kayan jikinta.
Ni ko zama nayi ina duba jikina inda Ya Aminu ya FASA min wani gurin ma har fatar ta kwailaye gefan bakina ya fashe hannu na NASA na shafo jinin , a fili nace ” Allah ya Isa Wallahi bazan tab’a YAFE wa, duk abunda nayi ai ba akaina farau ba, ballanta na ma banyi komai ba tunda dai ba kamani a kayi gidan karuwai ba ina zina ko ina cacah,tsabar mugunta da rashin tsoron Allah yayi mutum yawo aikin banza da wofi”!! Da k’arfi na karasa maganar domin ya Aminu yaji na dauka yana gidan, Umma ce ta d’aga labulen dakin tace” Yayi miki kyau! Asma’u wuyan ki ya Isa yanka kiyi ba dai-dai ba kice baza’ayi miki fada ba, lallai kin cika, kuma kin kai munzali Yanzu kin kara tabbatar min da cewar aure kike so bari gobe tayi da kaina zai wanke kafafuna naje gidan Kawun Ku Yunusa muyi magana gwara in aurar dake tun kafin ki jawo min abun kunya.”
Da sauri na mike na Isa gurin hade da rike mata kakafu ina kuka tare da bata hakuri ina fadin”Umma wai me akace muku nayi a gurun party nan ne, Umma ki lura dani wallahi bazan tab’a zubar da mutumci na ba da kima ta ta ‘ya mace, Umma ki yafe min kina kallon yanda Ya Aminu yake duka na kamar zai kashe ni.” Umma ta fuzge k’afafunta ta futa daga dakin ba tare da tace komai ba
Bakin kofar na zauna ina kuka Mimi tazo ta tsaya a kaina tare da fadin “Bani waya ta,aikin kawai kin karar min da chaji a banza da hotunan ki, kin San ba wuta ake kawo wa ba”Wani irin kallo nayi mata ina gyad’a kai cike da takaici nace” Ki duba wayar ki cikin jakata gata can a tsakar gida. ” tsallake ni tayi ta futa, daga dakin.
Chaji taje ta kai domin bai zama lallai su kawo mana wuta ba,
Ranar ko abuncin dare hanci ba, haka na kwana da cikina tsabar bakin ciki ya hanani bacci sai juyi nake.
Kamar yanda ta kwana tana juyi to shima haka ya kwana yana murk’ususu zuciyarsa Sam! Babu dad’i ga uban zazzab’i da ya kwana dashi, ko da asubah ma a daddafe yayi sallah Yana jira gari ya waye musu a can , time din ko wace k’asa daban yake
K’arfe Biyar na asubah mun tashi Ya Aminu ne ya tsaya a kanmu har sai da yaga ko wacce ta mike tsaye sannan ya nufi massalaci, motsin Umma Naji a tsakar gida tana alwala da sauri na koma na zauna, domin bana son na futa mu had’u. Mimi ta futa ta barni,, ko minti biyu ba ayi ba kira ya shigo wayar Mimi, daga inda nake in hangowa Heart beat sunan da nagi kenan, cikin zafin zuciya na dauki wayar na kashe! A fili nace”Aikin banza da wofi asubar fari za’a damu mutane. ” wani kiran ne ya kara shigowa na kashe da sauri,, A’a wani kiran ya kara shigowa na kashe, sai da ya kira sau bakwai ina kashewa, yana kiran na takwas din ne kawai na kashe wayar gaba d’aya.
Nashi b’angaran sakato yayi da wayar a hannu lokacin da ya kira suka fad’a masa cewar an kashe wayar ma gaba d’aya, tunani ya shiga yi anya Mimi zata kashe masa waya kuwa? Why!!! Me yake faruwa ne.? Jefar da wayar yayi kan bed ya yunk’ura ya tashi zaune kwalin sigari ya dauko ya bata wuta ya fara fesawa cikinsa hayak’i da sanyi safiyar na, da sauri kuma ya dauko wayar tare da nemo numbar rambow bugu guda tayi ya dauka baki na rawa yace.”good morning sir.” Bai amsa ba yace.” Meye labari ina fatan ka yi aikin da na sanya ka.”? Rambow yace.” Yes sir Ashe ma ba d’an gari bane yazo bak’unta ne dan barno ne wato mai duguri.” Da babbar murya yace.”kaje Sanar dashi cewar inji ya bar garin nan kafin in k’araso idan ba haka ba sai da uwarsa ta haifi wani Wallahi. “!!!! Rambo ya tsorata jin furucin oban gidan nasa, ta yaya zai iya zuwa ya fad’awa mutumi haka, amma duk Dan a zauna lafiya yace.” Insha Allahu zani yanzu.” Kashe wayar yayi yana huci!!!
Mimi ta shigo a tsanake ta shimfid’a dadduma ta tayar da sallah, futa nayi daga dakin nima domin dauro alwala. Bayan ta idar Da sallahr ne sai ta dauki wayar kawai ta ganta a kashe alhalin a kunne ta bar ta. Kunnawa tayi tana zargin Asma’u cewar ita ce zata kashe mata waya.
Aikuwa ko minti biyar ba ayi ba, kira ya shigo wayar tana dubawa taga Heartbeat wani murmushi ta saki had’e da kwanciya kan katifar tana lumshe ido ta d’aga wayar. Tare Da fad’in”Assalamu alaikum.”
Sama-sama ya amsa murya a kaurare! Yace.” Had’a ni da wannan yarinyar.” Dai-dai lokacin dana shigo dakin kenan ina jin komai tunda a hands free wayar take.. Cikin tsawa yace.” Ko ba kyaji ne.”!! Mimi ta tsorata mutuka, muryar ta na rawa tace”Wace yarinyar.”? Kai tsaye yace.” Asma’u. ” jin ya anbaci sunana yasa na zabga tsaki da k’arfi don yaji, aikuwa yaji lokacin da tayi tsaki! Sai ya mike da sauri jikinsa na wata irin tsuma! Kamar Wanda ya sha tsumin ‘yan bori ya kwatsawa Mimi tsawa tare Da fad’in “Bata wayar naji ta a kusa dake.”!!
Ganin yanda yake kurma wata irin tsawa ne yasa na fasa tada sallahr raina a mutukar b’ace na karb’i wayar da take Mik’o min murya sama-sama nace” ta bani wayar meye.”!! Tsaye ya mik’e da sauri cikin hargagi yace.” Budurwar ‘yan daudu yarinya mai aji da kamun kai!! Budurwa me lasisi a jahar kano, duk naga abunda kikayi jiya, ki sani kamar a gabana komai ya faru! Wallahi-wallahi ki kiyayi haduwar mu dake sai kinyi mugun raina kanki!! Ni zaki zubar wa da mutumci…… Katse shi nayi kafin ya k’arasa maganar tashi nima cikin hayaniya nace” Kai!!!! Malam wai me ka dauki kanka ne? Meye ya shafe ka dani? Meye alakar ka dani da kake wannan ihun! To bari kaji naji dad’i da ka gani ka sani jikina ba irin na ko wane lusarin namiji bane irin ka mai aikata sab’on Allah yanzu nayi maka nisa! Kuma tab’a min jiki da kayi kwanakin baya na barka da Allah ehe!!! Ita ma Mimi addu’a nake mata Allah ya tsare ta daga sharrin k………”ShautUp Your dirty mouth.”! A zafafe! Tsorata nayi amma saboda taurin kai yasa nace” Ank’iyin shiru d’in duk abunda na fad’a gaskiya ne ai Mtssss.” Na buga wani irin tsaki had’e da jefawa Mimi wayar a cinyar ta. Ji nayi yana fad’i” Ok zamu had’u ne zaki San Wanda kike wannan rashin kunya wallahi sai kin maimata min duk abunda kika fad’a kuma, kiyi gaggawar korar wannan mummunar saurayin naki bak’i me kamar alade irin ki, idan ya sake Nazo sai na b’adda shi a duniyar nan.”!!
Mimi tayi sakato da waya a hannu bayan ya kashe nu kuwa tada sallah ta nayi raina a mugun b’ace!
Wani irin tunani take a zuciyar ta, wannan tashin hankali da guy nan yake yi na lafiya ne kuwa? Anya ba son Asma’u yake ba? Take tambayar kanta, in kuwa hakane babu shakka rayuwar ta tana cikin garari domin baza ta iya had’a miji da Asama ba, gashi duk duniyar nan babu namijin da take so kamar sa, tana ganin sai da ta mutu babu aure.