BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Pictures da Mimi ta turo masa yake dubawa, du Rabin su ita da Asma’u ne sai wannan budurwar da ya tab’a ganinsu tare wato Munnu, kayansu iri d’aya haka ma Dinkin su iri daya to wai me yasa d’inki a jikin Asma’u yafi nuna tsaraci. Shi kadai yake WANNAN tunanin, wata zuciyar tace masa ai duk tafi su ciki ta ko wane fanni.. Fuskarta yake kallo kamar zai lashe ta, har kara zomming din pic din yayi dai-dai ita yana kare mata kallo, ajiyar zuciya ya sauke tare da fadin”Zaki gane Baki D’s wayo yarinya, wani pic din ya bude ,sai da wayar ta kusa fad’uwa daga hannunsa, ganin guy nan shi da ita suna kallon juna kamar masu kallon love. Ji yayi duk duniyar tayi masa zafi, ya kalli Anthony da jan ido cikin turanci yace.” Gobe zan wuce najeria Tunda komai ya kammala anan.”
Anthony ya gyad’a kansa gami da cigaba da aikinsa
Mik’ewa yayi da sassarafa ya shige bedroom din, kan wata duguwar kujera ya zube hade da dafe kanshi, yana cije lips din sa tunani kawai yake wane irin hukunci ya kamata yayi wa yarinyar nan.
[11/4, 5:47 PM: *
Kwanan bakin ciki da damuwa yayi a ranar, washe gari kuwa da wuri ya gama sallamar duk Wanda ya dace, ya bar amanar komai a hannun Anthony ya nufi k’asar sa ta gado wato Najeria.
Sha biyu dai-dai jirgin su ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu kano, su Rambo na gefa suna ganin saukowar sa suka k’araso da sauri Rambo ya karb’i wayoyinsa shi kuma doh-doh ya karb’i ‘yar jakar sa. Suka nufi mota.
Satar kallon fuskar sa suke ganin fuskar ogan nasu kamar Wanda aka aikowa masa da mutuwar iyayensa, Tunda ya shiga motar babu Wanda ya kula a cikinsu har suka isa gida. Get Man yana ta d’aga masa hannu tare da fatan alkairi ko kallonsa bai yi ba Doh-doh na gyara parking ya bude motar ya futo ba tare da ya jira rambo ya bude masa ba.
Kai tsaye ciki ya nufa suka rufa masa baya, nan parlor suka aje masa wayoyin shi hade da jakar shi, suka futa da sauri.
Yana shiga bedroom dinshi ya fada toilet Wanka yayi ya futo ko mai bai shafa ba, parlor ya futo masifa na cin sa, zama yayi hade da kiran Rambo a waya domin yaji meye labarin guy nan yana ganin ta kanshi zai fara.
4/November/2019
[11/5, 11:28 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
Mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.
41
Rambo ya shigo cike da Ladabi yace. ” Sir g… Gurin zama ya nuna masa Rambo ya zauna jikinsa a sanyaye saboda yanayin da ya ga ogan nasu ya bashi tsoro. Cikin dakakkiyar murya yace.” Wannan guy ya bar garin nan ko kuwa.”? Rambo yace.” E to jiya da na ga gilmarsu a mota shida abokina sun wuce can Titin rimin gata, ina kyauta ta zaton can masaukin sa, yake.” Mik’ewa tsaye yayi hade da goya hannunsa a baya, ya kalli Rbow da jajayen idonsa yace.” Kaje kazo min dashi, nan.” Rambo ya mik’e jiki na rawa ya futa daga d’akin. Shi kuma ya cigaba da kaiwa da kawo wa cikin parlor
Rambo da doh-doh sun jima a tsaye suna tattauna maganar kafin Rambo ya shiga mota ya tafi, yanda suka tsara shine baza su biyewa Ogansu ba, zasu yi masa dabara ne kawai saboda suna ganin a yanda yake kan dokin zuciya zai iya kashe guy nan kamar yanda ya fad’a.
Amjad yafi a wa guda a tsaye a parlor sai kace wani soja, bedroom dinshi ya nufa wayar shi ya dauko ya dawo parlor ya zauna numbar Mimi ya kira yaji wayar a kashe, ranshi a bace ya aje wayar yana tunanin ta yarda zaiyi ya gansu. Minti ashirin a tsakani ya k’ara kiran wayar kamar da wasa aka dauki wayar, Muryar Namiji yaji yana sallama.Amsawa yayi Tare da gyara zaman sa, Ya Aminu a nashi b’angaran ya gane muryar Amjadu da sauri ya gaishe shi, ya amsa babu yabo babu fallasa, yace.” Yallab’ai Ashe dai yaran nan da gaske suke yi.” Amjadu yace.” Menene ? Aminu yayi masa bayanin yadda suka tada hankalinsu ganin wayar a hannunsu. Murmushi yayi yace.” Nine na bata domin mu dunga gaisawa, Ya Aminu yace.” Allah ya saka da alkairi gaskiya akwai alamun tambaya anan Yallab’ai idan banyi rashin kunya ina so in San cikinsu wacece tayi dace da samun gwarzo miji irin ka.”
Kai tsaye yace.” Dukaninsu nake so zan aura lokaci guda idan zaku bani.” Aminu yaji gabansa ya fad’i yace.” Yallab’ai a yi haka kuma.”?
Murmushi yayi yace.” Anyi an gama ni dai a gurina saboda haka ina so ka sanar da manya kafin in turo magaba tana a tsai da magana domin baza a ja lokaci me tsayi ba.”
Yaya Aminu yace.” Insha Allahu Yanda kace haka za’ayi mungode sosai da wannan karamcin.” Sallama sukayi hade da kashe wayar.
Yaya Aminu ya dad’e zaune a gurin da yake kafin ya mike ya shiga gida jikinsa a mutukar sanyaye, ya samu Umma na d’aurin sikari a rumfa zama yayi kusa da ita tare da fadin “Umma kinji gagarimun abunda mutumin nan ya dauko mana kuwa.” Umma tace”Wane mutumin ?
“Amjadu” Aminu ya fada jikinsa babu k’wari, tace “A ina kangan shi kai.”
“Yanzu muka gama waya dashi, Wai yana son ya auri Asma’u da Mimi lokaci guda.” Umma ta saki ledar da take hannunta tana kallon Aminu cike da mamaki tace”Wannan wace irin magana CE.”? Yace.” Wallahi haka yace” Shiru tayi tana nazarin maganar daga bisani tace”Mimi da Asma’u Anya hadin yayi kuwa gaskiya Indai Yana so sai da ya zab’i d’aya a cikinsu.” Aminu yace”Umma mutum me girma kamar wannan ko mata hudu yace.” Zai aura a lokaci guda za’iya ya tsallake gidaje sama da miliyan yazo nan bamu aje ba bamu bawa wani ajiya ba, gaskiya ni bazan iya fada masa haka ba.”
Umma tace “Zaman kishi tsakanin Asma’u da Mimi akwai kwara Mimi sanyi hali Asma’u wayo da rashin kunya gata itace k’arama bana son abunda zai tab’a zumumcin su.” Aminu yace.” Sai dai idan sune suka so haka amma in sun hade Kansu babu wata matsala. Umma tace” Shikkenan zanyi magana dasu.” Ya Aminu ya mike ya futa jikinsa babu kuzari.
Mimi na daki a kwance ni kuma ina bakin rijiya ina wanki Umma ta kwala mana kira, aje sabulan hannuna nayi na amsa hade da cewa “Gani nan zuwa Umma.
Ina zama Mimi ta shigo salo-salo Umma tace.” Kun San abunda yake faruwa kuwa.”? Girgiza kaina nayi, tace” A cikin Ku Wa ya tab’a furtawa Kalmar so.” Nace”Umma waye.” ? Hararata tayi tace”Wanda kuka sani mana.” Kaina sai ya daure kawai domin ban fuskanci abunda take nufi ba.”
Tace”Ke ya baki KUDI hade da yi miki shopping ke kuma ya baki waya, shine nake tambayar wacece a cikin Ku ya taba cewa wance ina son ki,saboda yau ya bujoro mana da bukatar son ya aure Ku duk Ku biyun.”
Das!das! Haka gababa ya dinga fad’uwa, baki na rawa nace”Umma ban…ban fahimce ki ba.” Mimi ta kalla tare da fadin”Ke dai nasan kin fahimce ni ko.”? Mimi ta gyad’a kanta tare da fadin”Na fahimce ki Umma a gaskiya ni dai Kalmar so bata tab’a hadani dashi ba sai da ko ita Asma’u. ” harara na banka mata nace”Ki fad’i gaskiya dai ko kinyi maganar aure dashi amma ni meye shafe ni da har zai ce zai aure mu ni dake, babu wata kyakyawar alaka mybe ma duk abunda yayi min saboda kene, Umma ni kam babu abunda ya shiga tsakanina dashi Mimi yake so.” Na fada raina a bace. “
Umma tace”Yanzu dai ya turo Aminu da sako saboda haka sai kuje Ku sasanta kanku.”
[11/5, 7:40 AM] .: Tab’e bakina nayi na mike hade da barin gurin. Wankina na cigaba da yi ina tunanin al’amarin lallai ma, wai yana so ya aure mu ni da Mimi kiji sai kace Wanda aka ce masa mun rasa majin aure aiko sama da kasa zata hade bazan aure shi ba, Mimi taje ta aure shi, ni gani nake ma kamar da wata manufa ya shirya hakan