BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Ina kallon Mimi ta futo salo-salo ta shiga dakinmu kallo na bita dashi ina tab’e bakina nace”Kin had’u da aiki babba a rayuwar ki, Ya Aminu ne naga ya shigo cikin gidan da sauri hannunshi rike da wayar Mimi ya nufi dakinmu, babu wayar ya futo, da alama shi yake kiranta. Zuciyata naji babu dad’i naji ina son inji wace hira suke dashi, daurewa kawai nayi na cigaba da wankina, ina jiyo muryar Mimi k’asa-kasa tana magana…… Kwafa! Kawai nayi cikin zuciyata nace”wannan guy shigowar shi cikin al’amari mu ba k’aramin hatsari bane domin zai iya wargatsa mana zumuncin mu.” Sai da na gama tsaf! Sannan na shiga dakinmu ina k’okarin cire kayan jikina Mimi ta kalleni baki na rawa tace.” Asma’u kin San meye.”? Kai tsaye nace”sai kin fada.”
A hankali tace”Wai Amjadu ne zai zo bayan sallahr Isha’i zai kawo mana tsarabar mu.” Ba tare da na kalleta ba nace”zai kawo miki tsaraba dai.” Har da ke ai.” Girgiza kai nayi nace” ni kam bana son komai nashi, ban sani ba ko sai kunyi aure sannan zan daina jin haushin sa.” Tace”Waye ya fada miki zan aure shi.” Cike da mamaki nake kallonta na kasa cewa komai ma, na cigaba da saka kayansma tace” bazan Iya hada miji dake ba Asma’u, gwara in hak’ura in bar miki shi.” Muryar ta na rawa ta k’arashe maganar.
Sai ta bani tausayi mutuka nace”Mimi zaki iya hakuri da ruhin ki Ashe? Zuciyar ki tana mutukar kaunar mutumin nan, idan kikayi haka to zaki jefa kanki a halaka, wallahi in har don ni zakiyi haka, to bari kiji wallahi zan iya sadauakar miki da komai na rayuwata domin ki samu farin ciki, ballanta d’a namiji ki kwantar da hankalin ki, ni ba bakuwar zafi bace, Sam Amjadu baya gabana, a yanzu na bar miki shi zan cigaba da yi miki fatan alkairi har karshen rayuwar ki.”

Kuka tq fashe dashi hade da rungume ni sosai take kuka nima sai na tsinci kaina da share hawaye tace”Asma’u kin San Allah sai dai in mutu da sonshi mutukar kika ce baza ki aure shi nima na hak’ura gwara soyayyar shi ta zama ajalina.”

Yanda take fad’ar maganar tana shashshekar kuka hade da wani irin Abu yasa hankalina yayi mugun tashi Mimi kuka take wiwi tana dukan k’irjinta hade da fadin”Me yasa zuciyata zakiyi min haka.? Meyasa kullum kike azabtar dani akan son mutumin nan, Asmau da nasan inda zanje in jefar da zuciya ta da najefar na huta da masifa” tana wani irin kuka ta k’arashe maganar.
Hankali a tashe nace”Mimi meye haka? Mai yayi zafi? Kina so ki kashe kanki ne? Kike dukan kirjinki.” Cikin kuka tace” Asma’u gwara in mutu akan i n rayu a duniyar nan, kwata-kwata zuciyata ba tayi min adalci ba, Asma’u na san ke Amjadu yake so amma saboda sharrin zuciya kullum sai take fada min karya ne, ni yake so, kinga kuwa wannan zuciyar bata da amfani a gare ni, Tunda tana kokarin sanya min abunda bazan samu ba.” Cike da tausayin ta nace” Mimi yaya zaki ce baza ki samu ba, kinga na farko dai mutumin nan ya fad’i kirkin ki da kyawun halin ki kyawun zuciyar ki, ko wannan ma amsa ce ta ki gane cewar yana sonki, ki saka a ranki baki da Miji sai Amjadu insha Allahu zan iya bakin kokarina gurin ganin tabbatuwar auran Ku.” Hawaye ne kawai yake zubo mata na sanya gefan zanina INA share mata, da kyar na samu tayi shiru dadin da naji ma Umma ba taji ba yara sun cika gidan suna siyyaya.


K’arfe shida dai-dai ya futo cikin kyakyawan shiri yau, shigar manyan kaya yayi wata lafiyayyir galila ce a jikinshi skyblue dinkin babbar Riga da ‘yar ciki taji lafiyayyan sirfani na masu hannu da shuni yau mutumin Ku ya sanya hula inda ta kara futo masa da ainihin kyawun sa hade da kwarjinsa, hannunsa daure da agogo shi mai tsada sai zabbuna na azirfa guda uku a ya tsunsa masu wani irin ado hade da stons kana ganinsu kasan zasu ja kudi, takalmi me gidan ya tsa ne a k’afafun shi kamfanin Gucci Dan Asali yayi kyau har ya gaji inda kasan wani ango, Ni ko nace ba dole ba za’a tafi neman aure fuskarsa babu yabo babu fallasa ya futa, bodyguard d’insa suka mike da sauri, hannu kawai ya daga musu ya karb’i key hannun Doh-doh da kanshi ya futo da motar daga inda take mai gadi ya bude masa gate ya futa daga gidan suna daga masa hannu Kai tsaye gidan granny ya nufa, bai shiga gidan ba sai da ya gabatar da sallahr magariba a massalacin dake manne da gidan sannan ya shiga.
Kamilar Dattijuwa na zaune kan dadduma da carbi a hannunta tana lazimi da alama ta idar da sallahr ne, zama yayi a kujera Yana jiran ta kammala, minti goma a tsakani ta shafa addu’ar ta, ta kalle shi bayan ta aje carbi tace”Babban mutum.” Kallonta yayi cike da mamaki! Tace”Yau dole in kira ka da wannan suna
Wannan kwalliyar ta burge ni sosai don har na fara kishin ka tun kafin kaje inda zaka je.” Dariya ya sanya tare da fad’in”Ai kuwa sai da kiyi domin babu abunda zai hanani tafiya Neman aure, auran ma na mata biyu kece ta ukun. Kafin in cika so ta hudun.
Hararsa tayi tare da fadin”Mace biyu ai bata kama ce ka ba kaji da guda daya, ta Isa.” Yace.” Ba kin ce zaki shiga kauyika ki samo min maganin k’arfi ba.”? Zama ta gyara tana kallonsa tace”K’warai kuwa yau a can muka yini nida Iyami ga wani sassak’e can na karb’o maka Wanda za’a dafa shi da jar kanwa ya zama shine ruwan shanka, insha Allahu mai maganin yace zaka koma kamar zaki gurin k’arfi.”
Dariya ya kyalkyale da ita Sam! Ya manta da b’acin ran da yake ciki yace.” Toum kinga sai in fara Neman aurena da hujja.” Mik’ewa tayi tsakanin ta da Allah take fad’in”Ai mutukar zaka diman ci shan maganin matar ka baza tayi takaici ba.” Cikin dariya yace.” To kawo min na fara sha yanzu ya bi jikina nasan dai already kin had’a min.” Tace”Yanzu kuwa a i mikewar da nayi zan dauko maka ne, NASA Iyami ta k’ukkula maka shi a farar Leda kullum ka dinga shan d’aya.” Yace” maza ki kawo min uwargina.” Bedroom dinta ta nufa, tana tafiya tana kara tisa maganar.

Shi kuwa bayan shigewar ta dariya ya kama yana mamaki wai shi Granny zata bawa maganin k’arfi hummm! Yana zaune ta futo dashi cikin Leda viva sabuwa dal, dauru kusan ashirin ya karb’a yana dubawa, dauri daya ya dauko yana sansanawa, cikin haushi da takaici tace”Meye haka kuma zaka haramtashi fa.” Cikin dariya yace.” In na haramanta ma ai ni nawa ne kuma ni zan sha.” Tace” To fasa dauri daya kasha a gabana.” Aikuwa ya fasa hade da zukewa yace.” Idan cikina yayi ciwo kece kin yadda.” Tace”Na yarda wannan maganin bazai saka ciwon ciki ba sai dai ma ya gyara ka.” Yace.” Naji to zauna muyi magana dake.”
Granny ta zauna kusa dashi.
Yace.” Neman aure zanje fa.”
Granny tace.” Alhamdullahi yau Allah ya kawo ni wannan lokacin. “
Gyad’a kansa yayi yace.” Mata biyu zan aura ya kika gani. “
Shiru tayi tana nazari daga bisani tace”Ai Matsalar Ka ce abun ji.” Murmushi yayi yace.” Kar kiji komai duk zan iya dasu.
B’ata fuska tayi tace”to naji amma dai ta biyun Hafsa ce ko.”?
Yace.”Wacece Hafsa kuma.”? Tsaki taja tace”Kamanta kenan kana so ka hadani da Innar ka kenan? Dama suna cewa sai abunda nace dakai kake yi baka zumunci dasu dukiyarka baka Mora musu sai dai su ji a gari.”
Shiru yayi kawai domin shi kanshi ya San baya kyautawa Sam baya ziyartar dangin mahaifiyar sa, sun gani da korafin sun hak’ura dole yanzu ya gyara ko don kada duniya ta zage shi, Granny ya kalla yace.” Yanzu yaya kike so ayi. “? Zama ta gyara tare da fadin” Kaje ka nemi auran Hafsa yarinyar na da kirki kuma tana sonka.” Ya mutsa fuskar sa yayi wannan bukatar ta granny baza ta yi wu ba, yace.” Kiyi hakuri Granny bana so ayi Abu daga baya azo ana da an sani kin fi kowa sanin halina bana rufa-rufa yarinyar bata yi min ba, zan dai yi kokari gurin ganin naje mun gaisa dasu kuma zanyi musu alkairi sosai.”
Ajiyar zuciya ta sauke tare da fadin “Shikkenan to Ubangiji Allah yayi maka zab’i na alkairi “
“Ameen yace yana kallon agogon dake daure a hannunsa.
Mik’ewa yayi yace.” Insha Allahu komai ya dai-dai ta zamu je ki ga kawayen naki ko kuma in ce kishiyoyin naki.” Tace”,Allah ya kaimu yanzu ma ace dasu ina gaishe su.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button