EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Mrs Salees Mu’az ????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 34.
Second to the last page.

Bata koma ta zauna ɗin ba kamar yadda ya umarce ta ɗin tayi tsaye tana tura baki da gunguni wanda baisan abinda take faɗa ba.

“I said sit down”. yace cikin ɗan ɗaga murya yana buɗe mata ido dan yaga alamun yarinyar magana ɗaya batayi mata.
“Ni wllhy bazan zauna ba kawai sai kaita min wasu tambayoyi da ban gane kansu ba”. tayi maganar kamar zatayi kuka tana harararshi ta ƙasan ido, kai kawai yake jinjinawa yana kallonta itakam taƙi yarda ma sam ta kalleshi.
“ALLAH idan kika bari na tashi zanyi miki abinda bakiyi zato ba so kwanciyar hankalin ki koma ki zauna mu karasa maganar da muke batare da wani yaji kanmu ba kar kiga a cikin gidan ku kike wannan bashi zai hana in hukuntaki ba”.
Kamar zata saki kuka ta koma ta zauna bakin nan kamar zai taɓo Gashua dake zaune tsabar yadda ta turoshi gaba yau dai tana ganin ikon ALLAH azo har inda take a nuna mata fin ƙarfi da iko ALLAH mutumin nan ba ƙaramin ɗan rainin hankali bane gaban kujerar ya matso sosai yace
“Kina kallon TV?”. Haushi yasa tace a’a
“Why?”. ya ƙara jefo mata wata tambayar
“Ra’ayi na ne hakan”. ta faɗi hakan cikeda rashin kunya, tsaye ya miƙe yana kaɗa kai ya nufo inda take zaune duk da gabanta ya faɗi amma bata nuna alamun haka ba harya ƙaraso gabanta yana zuwa ya ɗora ƙafa ɗaya kusa da ita ya ranƙwafa kanta murya ba alamun wasa yace
“Zaki faɗa min gaskiya kokuwa saina baki mamaki yanzun nan?”.
“Nifa gaskiya na faɗa maka”. tace kamar zatayi kuka harga ALLAH ta fara gajiya da halin mutumin nan.
“Wai ina wasa dake ne? bazaki faɗa min gaskiya ba”. Ganin yadda ya ƙarasa maganar cikin tsawa yasa ta ɗan tsorata ta ɗaga masa kai.
“Good! kinga yarinyar da aka haska wadda ta ɓata ake nemanta?”. Nan ma kai ta gyaɗa masa hakan yasa yace
“Kamar ku ɗaya ba abinda ya bambanta ku me hakan ke nufi?”.
“Nima ban saniba”. ta bashi amsa kai tsaye.
“Kin santa ne?”.
“A’a ni ban taɓa ganinta bama”. Kai kawai yake kaɗawa yana cije lips kafin ya tashi daga ranƙwafar dayayi a kanta ya zura hannayenshi duka cikin aljihun wandonshi ya fara zazzagayawa cikin falon ta bishi da harara kamar idanunta zasu faɗo tsabar haushin shi datake ji, ba tare daya juyo ya kalleta ba yace
“Zaki iya tafiya amma kina iya gani nadawo koda yaushe idan buƙatar hakan ta taso”. Dama kamar jira take jinta take tamkar akan ƙaya, saurin miƙewa tayi ta nufi ƙofar fita har lokacin bai juyo ya kalleta ba, sai data tabbatar data fita sannan ta tsaya daga bakin ƙofar tace
“Karka sake ka dawo gidan nan wllhy inba haka ba saina baka mamaki kaima kamar yadda kace zaka bani Mr. Nunar rana”. tana faɗa tabar wajen da hanzari tana ƴar dariya tasan dai tagama kunna shi tunda ta faɗa masa wannan sunan yo inba nunar ranar ba me za’a kirashi? ragowar shawara kawai.
Lips ɗinshi ya cije tamkar zai hudashi ya runtse ido yana tunanin wane irin raini ne yakeso ya shiga tsakaninsu da yarinyar ne? yaushe ma sukayi zaman da har zata rainashi haka? lallai ya kamata ya goge rainin dake tsakaninsu tun kafin ya ƙara yawa ta wace hanya kenan zaiyi hakan? ƙwafa ya saki ya fito batare di takan abinda ta ajiye masa ba tun ɗazu ya fice daga gidan, motarshi ya shiga ya figeta da wani irin mugun speed ya fice daga layin sam bai iya bin mota a hankali ba a duk lokacin dayake driving.
A falo ta samu Aunt Ramlah, zama tayi kusa da ita tana jan tsaki duk yagama ɓata mata rai wannan gayen.
“Lafiyar ki kuwa Heedayah meya faru kike tsaki?”. Aunt Ramlah ta tambaye ta.
“Nida wannan jikan Hajiyan mana ɗan rainin wayo yazo sai wasu tambayoyi yake min marasa kai ko ina ruwanshi dani”.
“Wane irin tambayoyi yayi miki?”.
“Nifa Aunt Ramlah sam ban gane ma inda ya dosa ba yana ta wani tambayata wai ya muke dake daga ina nazo me nazo yi nan bla bla bla bla ya isheni da surutu”. dariya Aunt Ramlah tayi cikin zuciyar ta tana ayyana anya kuwa wannan mutumin baisan wani abu akan rayuwar su Heedayah ba kuwa? zuzzurfan tunani ta shiga wanda batasan lokacin ma da Heedayah ta tashi tabar wajen ba.
Kai tsaye gidan Hajiya yayi parking bai ƙarasa nasu gidan ba.
Tana zaune Larai mai aikinta tana shafa mata man zafi a ƙafafunta waɗanda suka ɗan matsa mata cikin ƴan kwanakin nan ya shiga cikin falon da sababbiyar sallamar shi daya saba a ciki, waje ya nema ya zauna Larai na masa sannu da zuwa kai kawai ya ɗaga mata ta rufe kwalbar man zafin dama tagama shafawa ta tashi tabar wajen.
Kallon Hajiya yayi yana gaisheta ta amsa tana tambayar shi lafiyar su Ummi a taƙaice ya amsa mata da lafiyar su ƙalau yaja bakinshi yayi shiru.
“Yadai maigidan daga ina haka?”. cewar Hajiya tana kallonshi murmushi ɗauke a fuskarta, rai ya ƙara haɗewa sosai yace
“Ƙarar yarinyar nan na kawo miki Hajiya kija mata dogon gargaɗi a kaina dan ni ba sa’anta bane”.
“Tooo wace yarinya ce haka?”. Hajiya ta tambaya cikin mamaki.
“Wannan yarinyar mai zuwa wajenki I mean Heedayah ne ko menene?”.
“A’a ikon ALLAH, a ina kuka haɗu da Heedayahn ne kuma me tayi maka?”.
“Ayi mata warning dai Hajiya dan zan iya karya yarinya ba damuwa ta bace”.
“Eh lallai ba shakka tunda ga ubanta ai dole ka karya ta yau naji neman masifa da bala’i saika faɗa min abinda tayi maka da har kake maganar zaka karyata”.
Baice komai ba ya tashi ya fice yabar Hajiya tana ta faman mita kamar zata biyoshi.
Ya shiga mota kenan kafin ya tayar da ita wayarshi ta fara ringing yana dubawa yaga Auwal Azare ne mai kiran, picking yayi ya kara wayar a kunnenshi kafin yayi magana Auwal yace
“Mr. Gashua how far?”.
“Alhmdulillah ya kaje gida?”. ya mayar masa da amsa.
“Masha ALLAH ina maganar mu ta kwana ne Gashua please kayi wani abu mana”.
Sam yama manta da Auwal ɗin yace yana son Neehlah dan haka cikin rashin fahimta yace
“Wace magana kenan?”.
“Habaaa mana mutumina maganar ƙanwarmu mana kasan jiya fa ko cikakken barci banyi ba saboda ita dana rufe idona sai in ganta”. ya ƙarasa maganar da iya gaskiyar shi yana sauke numfashi daga ji maganar daga cikin zuciyar shi take fita, takaici ya hana Habeeb cewa komai sai tsaki kawai dayaja jin yayi shiru yasa Auwal marairaice murya yana faɗin
“Please say something mana Mr Gashua zaka bani ƙanwar ka da gaske na faɗa dayawa batare da sanina ba”.
Wayar kawai Habeeb ya kashe bayan yaja tsaki a fili yace
“Shege babban banza Neehlah har takai macen da zaiyi irin wannan ruɗewar akanta? wani kiran Auwal ɗin ne ya ƙara shigowa a fusace ya ɗaga kiran yana faɗin
“Idan ban zageka ba kace ba sunana Habeeb ba wai mayen inane kai Auwal? akan ƙaramar yarinya kake wannan shirmen dan ubanka ka dawwama baka barci indai a kanta ne karka ƙara sani cikin wannan maganar banza mara aikin yi”.
“Ɗan iska dama ai nasan halin rashin mutuncin ka bazaka goyamin baya ba to ni sai inda ƙarfina ya ƙare a kanta”.
Murmushi yayi yana taɓe baki yace
“Goodluck Dr Auwal Azire”. yana shirin kashe wayar yaji Auwal ɗin yana faɗin
“Sanin danayi maka da Gashua ko magana bata dameka ba amma yanzu ka zaƙe da yawa ka koyi rashin mutunci da faɗa what wrong with you Dude?”.
“Ni kaina bansan yaushe na koma haka ba amma nafi tunanin mutane ne suka canzani”. bai jira Auwal yayi magana ba ya kashe wayar yayi switch off ɗinta ma gaba ɗaya dan yasan mawuyacin abune bai ƙara kira ba shi mamaki ma abin yake bashi yadda Auwal ɗin yabi ya ruɗe akan Neehlah shifa soyayyar ma duka gani yake ɓata lokaci ne bare harya ruɗe haka akan mace.
Motar ya tayar ya nufi gidansu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button