EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL–HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 13.

Har drip d’in da Dr yasawa Habeeb ya k’are Mujaheed ya cire masa bai sani ba yanata barci, sharp sharp ya fita yaje wani babban pharmacy ya siyo magungunan yadawo yasamu har lokacin bai farka ba. Sai abincin daya gani da lemuka da alamu Ummi ce ta kawosu.
Sai daf da Azhar sannan Habeeb ya tashi ba laifi ya d’an ji dama dama sosai a jikinshi zazzab’in kuma tuni ya sauka sai ciwon kan da har lokacin bai gama sakinshi ba.
“Gashua ya jikin naka?”. Mujaheed ya fad’a yana kallonshi bayan tashin shi
“Alhmdulillah”. yace yana k’ok’arin mik’ewa tsaye ya nufi hanyar bathroom dan yin wanka Mujaheed ya bishi da kallo kafin ya maida kanshi kan wayar da dama ita yake dannawa, ya d’an d’auki lokaci kafin ya fito sanye da bathrobe black color da k’aramin towel a kanshi yana goge sumar shi kai tsaye clothes d’inshi ya nufa ya bud’e wani side wanda kayan shan iska ne kawai na zaman gida ya d’auko wasu riga da wando red color da adon fari a jiki ya koma toilet d’in ya shirya ya fito, gaban mirror ya tsaya ya taje sumar kanshi ya shafa mata mai ya fesa turaruka sannan ya shimfid’a pray mat ya tada sallah.
Yana zaune akan dardumar bayan ya idar da sallahr Mujaheed ya kalleshi yace
“Ni zan wuce Gashua, accountant yafara kirana kasan munada lissafi dashi yau d’in nan amma tunda ga yadda ta kasance sai mu d’aga lissafin”.
Kai ya girgiza cikin sanyin murya irin ta marar lafiya yace
“No, zaku iya yi ba dole sai ina wajen ba tunda gaka hakan ma yayi”.
“Okay bari inje ga abinci nan ga kuma drugs d’in nan kan bedside ALLAH ya k’ara afwah”. Bai jira amsawar Habeeb ba ya fice dan yasan mawuyacin abune ya amsa d’in.
Kallon inda kayan abincin suke yayi an shiryasu cikin babban tray yunwa yakeji sosai kuma bayajin zai iya ci bai sha’awar komi a yanzun ga bakinshi dayake masa wani iri ba dad’i, lumshe ido yayi yana k’ara tuna abinda ke faruwa dashi cikin y’an kwanakin nan kamar wanda akeso a haukata koma dai meye yazo k’arshe insha ALLAH dan zai d’auki matakin dayake ganin yafi masa, saita fad’a masa dalilin dayasa take masa wannan iskancin na canje canjen yanayi datake.
Tashi yayi ya fita falon shi ya shiga k’aton kitchen d’in dake cikin falon wanda yaji uban kayayyakin electric, black coffee ya had’a ya koma kan kujera ya zauna ya shiga sha da zafinshi kamar yadda ya saba, sam bai bi takan magungunan da Mujaheed yace ya siyo ba bare yayi tunanin shan su.


9:45pm.
K’aramar farfajiya ce wadda aka k’awata ta furanni masu k’amshi sai rumfa irin ta bunu d’in nan teburi ne guda d’aya kacal sai kujeru guda hud’u da sukayi masa k’awanya an wadata ko ina da hasken fitilu masu kyau da d’aukar hankali wannan duk a cikin sashen Habeeb yake nan yake d’an zama jefi jefi yana shan iska duk da bawai zaman gidan ya cika yiba kafin ya zauna d’in ma aiki ne.
A yau dai a daidai kuma wannan lokacin yana zaune a ciki yana jiran zuwan Aleeyu wanda sukayi waya dashi yana son ganinshi. K’arar ringtone d’in wayarshi ne yasa ya bud’e idanunshi da suke rufe, hannu yakai ya d’auko wayar dake ajiye bisa table d’in yayi picking yakai kunnenshi sam banji abinda yace ba saboda yadda yayi maganar tashi murya a shak’e kamar mai ciwon mak’ogwaro.
Shud’ewar wasu y’an mintunan da basu wuce biyu zuwa uku ba Aleeyu ya shigo cikin farfajiyar ya k’araso inda Habeeb yake, sallama yayi ya shiga ciki.
“Yallab’ai barka da hutawa”. yace yana d’an rissinawa alamun girmamawa, sallamar kawai ya amsa yayi masa nuni da d’aya daga cikin kujerun wajen cikin mak’alalliyar murya yace
“Sit”.
Kujera Aleeyu yaja ya zauna ya sunkuyar da kai yana jiran yaji abinda maigidan nasu zai fad’a, Habeeb bai k’ara magana ba yayi shiru tareda rufe idanunshi sai faman girgiza k’afa yake, shidai Aleeyu yana zaune yana jiran Habeeb ya gama shan k’amshin nashi yaji kiran dayake masa, muryar Habeeb yaji yace
“Ina tunanin zaka gane yarinyar nan da muka gani a orphanage house wadda nace sai tabar gidan?”.
“Yes sir, zan ganeta”.
Baki Habeeb ya d’an cije lokaci d’aya yana lumshe ido sannan ya bud’esu akan Aleeyu dayake jiran k’arin bayani.
“Inaso ka sace min ita”. yayi maganar yana k’ara had’e rai sosai, a razane Aleeyu ya zaro ido yana kallon Habeeb wanda hankalinshi kwance baza kace ma shi yayi magana makamanciyar wannan ba (jama’a kowa yayi ta kanshi Habeeb Gashua ya zama d’an kidnappers ????????????).
Wani mugun kallo Habeeb ya jefawa Aleeyu hakan yasa ya danne tsoratar dayayi ya shiga shafa kai da fad’in
“Sorry sir”.
K’aramin tsaki Habeeb yaja yace
“Idan ka d’auko ta ka kaita can k’aramin gidana na lamid’o crescent ka tabbatar babu abinda ya sameta ko kwarsane (k’warzane) kunsan mutumin no hausa ????) banaso ya sameta do you hearing me?”. ya k’arasa maganar yana d’an kama gefen kunnenshi tareda yiwa Aleeyu kallon gargad’i, Kai kawai Aleeyu yake gyad’awa da tunanin yaushe maigidan nasu ya koma haka? kidnapped fa kenan duk da baisan dalilin shi na b’oye yarinyar ba, maganar Habeeb ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi
“Zaka iya tafiya, kar kowa yasan da wannan maganar bare har yasan ka d’auko wata yarinya yin hakan zai iya ja maka matsala understand?”.
“Yes sir, yaushe za’ayi hakan kenan?”. cewar Aleeyu.
“A yau da daren nan”. yace kai tsaye yana mik’ewa tsaye tareda zura hannu a aljihun wandonshi ya zaro wani key ya mik’awa Aleeyu, rissinawa yayi ya karb’a key d’in duk da yadda gabanshi yake ta fad’uwa saboda irin aikin da yallab’ai yasa shi.
“Good luck”. Habeeb yace murya a dashe tareda fita daga cikin rumfar Aleeyu ya take masa baya.
“Ka kula”. Habeeb ya k’ara fad’a lokacin da Aleeyu yake k’ok’arin fita daga side d’in nashi.
“Insha ALLAH”. Aleeyu ya amsa masa.
Rufe side d’in nashi yayi ya koma ciki, wanka yayi ya d’aura alwalah cikin nutsuwa yayi raka’ah biyu yayi addu’oen shi sannan ya kwanta yana karanto addu’ar kwanciya barci. Abin mamaki kuma sam
a wannan daren baiyi mafarkin yarinyar ba kamar yadda ya saba abin ya d’aure masa kai da tunanin me hakan kuma ke nufi???.

°•°•°•°•°•°
A wannan daren Aleeyu yayi nasarar k’wamuso Seeyamah yarinyar gidan marayu bayan ya k’ulle mata baki ta yadda koda tayi ihu ma babu wanda zaiji ALLAH ya bashi sa’a kuma sam bai samu matsala ba har ya fice da ita ya sata a mota yabar wajen da mugun gudu.
Tun a daren ya kira Habeeb ya sanar dashi aiki ya kammala, yaji dad’i sosai ya k’ara jaddada masa ya kula da ita zuwa da safe zai shigo unguwar daga nan sukayi sallama.

Plat house ne gidan da Aleeyu yakai Seeyamah had’add’e ne sosai yaji kayan k’awa tako ina masu kyau da tsada, kuka sosai Seeyamah take na fitar hankali tareda yiwa Aleeyu magiyar ya taimake ta maida ita inda ya d’aukota karya cutar da ita, baiyi magana ba bare ya tanka mata yasa ta cikin wani bedroom ya rufo ya koma falo ya zauna yanajin duk ba dad’i ga tausayin yarinyar daya cika masa rai bai san dalilin d’auko yarinyar ba wato bai hak’ura kenan dama, jiyake tamkar ya d’auketa ya maida ita inda ya d’aukota lokacin da shasshek’ar kukanta ke ratsowa cikin falon dayake.
A takure take a k’asan royal bed d’in dake d’akin ta matse kanta cikin gwiwoyinta tana kuka mai cin rai waye wannan mutumin daya d’aukota? meye had’inshi da ita? wane laifi tayi masa? tambayoyin datake ta maimaita su cikin zuciyarta ta kasa samun amsar su, kasancewar ya rufe fuskar shi da face mask shiyasa batasan waye ba kuma koda ta ganshi d’in ba lallai ta ganeshi ba tunda ranar da sukaje gidan marayun bata ganshi ba koma dai waye tana addu’ar ALLAH ubangiji ya kub’utar da ita daga sharrin shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button