EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

★★★★★★★★★
“Amshi wannan idan kun tashi lecture ki biya ki kaiwa Hajiya”. Aunt Ramlah tace tana mik’awa Heedayah wani abu da batasan ko meye ba acikin leda dan duk anyi wrapping d’insu amma dai tasan bazai wuce nakiya da alkakin datayi ba shine za’a kaiwa Hajiyan, hannu biyu tasa ta karb’a tace
“Toh insha ALLAH”. daga nan sukayiwa Aunt Ramlah sallama suka tafi itada Zainab.
Wajen 3pm suka fito daga lecture, sai lokacin ne take ji ashe itama Zainab wai gida zata wuce saboda ta kwana biyu bata jeba sam bataji dad’i ba taso ace tare suka tafi haka sukayi sallama kowacce ta tari tricycle ta fad’i unguwar da za’a kaita.
Hajiya murna kamar me saboda zuwan Heedayah itadai ALLAH ya had’a jininta dana yarinyar, bayan sun gaisa ta bata sak’on Aunt Ramlah godiya ta shiga yi kamar ta ari baki k’warai take jin dad’in yadda yarinyar take kula da ita, tashi Hajiya tayi ta fita da nufin tasa akawo mata abinci.
Tana zaune bayan fitar Hajiya taga kamar gilmawar mutum da fararen kaya wajen ta kalla kafin ta k’ara juyar da kanta inda yake ada saikuma ta k’walalo ido ta k’ara waigawa dan ganin abinda tagani d’in da gaske ne kokuwa, sanye yake cikin farar jallabiyyah fara tas kuma sabuwa dal sai irin hular nan tashi ka fiya naci wadda ya d’ora sai hirami daya d’ora a kafad’arshi kalar fari da pink, mug ne a hannunshi ya fito daga k’ofar kitchen yafara taka steps d’in dazai sadashi da cikin falon cikin wani irin taku na mazantaka yana juya spoon a cikin mug d’in dake ta fidda turirin zafi.
Habeeb Gashua ne wanda idanun Heedayah suka hasko mata shi tuni yawun bakinta yafara k’afewa wani irin bugu da kai kawo zuciyarta keyi tamkar zata fito saboda tsabar tsoro shikenan itakam tata ta k’are dama ashe jiya da aljani tayi fad’a bata saniba dama saida Zainab ta fad’a tace maybe shirun dayayi mata na d’aukar mataki ne gashi kuwa ta tabbata ya biyota har inda take zai cutar da ita, tuni jikinta ya d’auki rawa sosai tafara fad’in innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir raheem da duk wata addu’a data sani ta neman tsari daga shaid’anun aljanu wani irin fitsari na son kufce mata wanda yazo mata a lokacin.
Tun fitowarshi daga kitchen d’in ya ganta kuma kallo d’aya yayi mata ya ganeta itace yarinyar datayi masa rashin kunya jiya, amma duk ba wannan ba abinda ya kawota gidan yakeson sani metazo yi wajen Hajiya? sam bai nuna yaga wata halitta a falon ba ya k’araso ya zauna a 1sitter yayi crossing legs d’inshi kanshi a k’asa yana cigaba da jujjuya tea d’inshi. Rawa bakinta yafara tana nunashi da hannu kafin ta k’walla wata uwar k’ara wadda ta ratsa dodon kunnenshi ya runtse ido gam saboda yadda k’arar ta shigar masa k’wak’walwar kanshi amma duk da haka bai d’ago ya kalleta ba so yake su tafi a matsayin shi aljanin ne kamar yadda yaga tayi zato haka nan ya tashi da sonyin irin shigar har dayazo Hajiya na tsokanarshi wai yatuna k’asar su kenan.
Da sauri Hajiya Inna ta shigo kamar zata kifa dan sauri tana fad’in
”Lafiya kuwa Heedayah meya sameki?”.
Cikin rawar baki da murya take nunashi da fad’in
“Hajiya gamo nayi wllhy, aljani ne ya biyoni nan dan ALLAH kibashi hak’uri bazan k’ara yiwa wasu rashin kunya ba kinji Hajiya dan ALLAH kibashi hak’uri ya tafi na tuba wllhy”. Inda take nunawa Hajiyan tabi da kallo taga Habeeb tamkar baisan me akeyi ba, d’an murmushi Hajiya tayi itama dason yin tsokana tace
“To aini banga komaiba Heedayah”. Sosai Heedayah ta k’ara tsurewa tace
“Hajiya gashi nan fa yana sha miki tea dan ALLAH Hajiya ki rok’eshi yayi hak’uri karya cutar dani”.
Kafin Hajiya tayi magana sai gani tayi, tayi luuu tana shirin fad’owa daga kan kujerar ido Hajiya ta zaro ta nufi wajen da sauri saidai kafin ta k’arasa Habeeb Gashua ya rigata wanda hakan yabani mamaki sosai tunda kanshi a k’asa yake bare har yaga fad’uwar da zatayi shi kanshi yayi mamakin hakan, tallafota yayi ta fad’a hannayenshi gaba d’aya jikinta ya saki alamun suma tayi lallai yarinyar nan ba k’aramar matsoraciya bace wato tsiwar ce kawai da fitsara.
Hajiya na k’arasowa ya sakar mata ita ya juya ya fice batare daya k’ara bi takan shayin ba.
A rud’e Hajiya ta janyo wani ragowar ruwa a cikin glass cups dake kan center table ta shafa mata a fuskarta, ajiyar zuciya takawo ta zabura daga jikin Hajiya tana kallon inda Habeeb yake zaune saidai wayam babu shi ba alamarshi, kuka tasa tana fad’in
“Shikenan Hajiya na shiga uku harya b’ace ban bashi hak’uri ba”.
Hajiya da batasan kan labarin ba tace
“Wai wanene meya had’aku dashi ne?”.
A tsorace tabawa Hajiya labarin abinda ya had’asu kwana biyu da suka wuce, dariya Hajiya tayi tace
“To kinga wannan saiya zamar miki darasi Heedayah ba kowane mutum zaka gani a hanya ba kaci masa mutunci wasu ba mutane bane suke shigowa cikin mutane su saje dasu kuma ko ina ana samun irin haka abu kad’an zakiyi kuma suzo su cutar da rayuwar ki dan haka ki dinga kiyayewa kinji, wannan da kika gani jikana ne nina haifi babanshi amma ALLAH yayi masa rasuwa mahaifiyarshi ce balarabiya shiyasa kika ganshi haka baiyi kama damu ba saiya d’aukota”.
Ajiyar zuciya Heedayah ta sauke tana dafe k’irjinta sai a lokacin taji sanyi cikin ranta wllhy duk zatonta aljanin ne da gaske musamman da Hajiya tace bataga kowa ba amma duk da hakan da a tsorace take dan gani take tamkar zai dawo yaci k’aniyarta a wajen dan da ganinshi da k’yar idan zaiyi mutunci wllhy amma fa she’s very very handsome guy dole ma yayi kyau ai tunda Arab ne.

A zatonku Heedayah ce Habeeb Gashua yake mafarki?

EL–HABEEB ????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION ????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 8.

Da k’yar Hajiya tasamu Heedayah ta d’an tsakuri abinci dan har lokacin bata koma normal ba gani take tamkar zai dawo ne bini bini ta kalli k’ofar shigowa falon. Tana gama cin abincin tayi shirin tafiya duk da yadda Hajiyan taso ta k’ara zama tace a’a tafiya zatayi akwai abinda zatayi a gidan idan takoma.
Tana fita ta shiga waige waige a k’ofar gidan ko zataga irin motocin data ganshi ranar dasuka had’u amma ba komai da sauri tabar unguwar,sai yanzu ne abinda tayi d’azu yakeson bata dariya tafiso idan taje gida su dara tareda Zainab.
Lokacin data koma gidan Zainab d’in ma bata dawoba sai bayan data d’an jima da komawa sannan ta koma, aikuwa tana ganinta tajata d’akinsu ta hau bata labarin abinda ya faru a gidan Hajiya, sosai Zainab tahau dariya harda rik’e ciki jin wai har suma saida Heedayahn tayi cikin dariyar take fad’in
“ALLAH ya k’ara, maganinki kenan ai to shi Man d’in meyace?”.
Baki Heedayah ta tab’e tace
“Ko k’ala baice ba nifa nafi zaton ma ko kurma ne dan baiyi kama da masu maganar ba”.
“Toh kodai shine zai maye gurbin marigayi Kabeer?”. Zainab ta fad’a tana kashe mata ido, wani kallo Heedayah tayi mata tace
“Ai mai maye gurbin Yah Kabeer saiya shirya wllhy shikam banga wani alamun jarumta a gurinshi ba sai tsayi daya ajiye kamar daren sallah”.
Dariya Zainab tayi tace
“Jarumta ai ba’a k’irar jiki take ba anan take”. tayi maganar tana nuna saitin zuciyarta da hannunta, d’an tsaki Heedayah taja tace
“Dan ALLAH ya isa haka maganar ta isheni”. kafad’a Zainab ta d’an d’age suka shiga wata hirar daban.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button