EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Gareku reader’s, Heedayah ce kokuma wata ce daban??? A kafta.

Maryam Ibraheem Aleeyu
(Ummee).
Mrs Salees Mu’az ????

EL–HABEEB ????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 9.

Har suka k’arasa gidan bai bud’e ido ba, koda sukayi parking Aleeyu yaga bashida haramar fita daga motar yadda yake a hakan nan kuma tsoron yimasa magana yake sai dayaga zaman nashi yak’i k’arewa sannan a hankali yace
“Oga mun k’araso fa”.
Batare daya bud’e ido ba yayi masa alama da hannunshi ya tafi kawai fita yayi ya rufe motar yabar wajen yana fatan koma dai meye ALLAH ya sauk’ak’awa maigidan nasu damuwarshi.
Sai bayan wani lokaci sannan ya fita ya shiga cikin gidan duk da baiso shigar ba saboda yadda yanayin shi yake amma kuma ya riga ya saba yana dawowa saiya dangana da inda Ummi take. A hargitse ya shigarwa Ummi ko sannu da zuwan da Neehlah take masa baiji ba baima ganta ba sam, tsareshi Ummi tayi da tambayar lafiya kuwa me yake damunshi? lafiya k’alau yace mata kawai yanayin aikine ya gaji ne sosai ba yadda batayi dashi ba akan ya fad’a mata idan wani abun ne yace ba komai dan haka tace ya tashi yaje yayi wanka ya huta tashin yayi ya fita ta bishi da kallo can k’asan ranta bata yarda da abinda yace mata ba.

Ranar ko abinci kasa ci yayi dama kuma ba ma’abocin cin nashi bane sai coffee daya dinga d’urawa cikinshi da zafinshi da komai, wanka yayi ya d’aura alwalah yayi sallah raka’a biyu kamar yadda ya saba kullum kafin ya kwanta sai yayi. jallabiyyahr dayayi sallahr da ita ya cire yasa pyjamas milk color masu kauri cikin nutsuwa ya karanto addu’ar kwanciya barci ya kwanta, yana kwanciya kuwa tunanin yarinyar ya addabeshi daya rufe ido da niyyar yin barci saiya hangosu itada wannan saurayin lokacin da suke dariya.
Da k’yar yasamu barci ya d’auke shi da tunanin ta lokacin da barcinshi yayi nisa kuma yarinyar data saba zuwa masa cikin barcinshi tazo abu biyu ya had’e masa, wani irin barci yayi a ranar marar dad’i shiyasa akan kunnenshi akayi kiran sallahr asubah na farko tashi yayi yana jin jikinshi duk ba k’wari wanka yayi yasa jallabiyyah ya fesa turaruka sannan ya wuce masjeed.
Bayan dawowar shi bai koma barci ba sai Alqur’ani mai tsarki daya d’auka yafara rairo karatunshi cikin daddad’ar murya dakuma k’ira’ar shi irin ta Mohammad Alkhusary mai dad’in gaske.
Barcin dabai komaba kenan dan lokacin daya gama karatun gari yayi haske sosai dan haka yayi wani wankan yafara shirin office.


Tun daga ganin yarinyar dayake tsammanin Heedayah ce yake hange hangen inda zai ganta a kullum idan ya fita ya tsiri zuwa gidan Hajiya akai akai sab’anin da dayake d’iban kwanaki kafin yaje ko ALLAH zaisa ya ganta amma bai k’ara ganinta ba kuma bawai zuwan ne batayi ba saidai sab’ani da suke samu wani lokacin data fita zai shigo kokuma idan shi yagaji da zaman ya fita itakuma tazo duk yabi yahana kansa sukuni shi kanshi a karan kanshi idan aka ritsashi akace saboda me yake nemanta bai saniba baisan me zaice ba kuma ya kasa tambayar Hajiya labarin yarinyar.


 Ummi ce zaune akan royal chair d'in da sukayiwa had'add'en falon k'awanya sai k'amshin turarukan wuta ke tashi na asalin larabawa, gefenta Mujaheed ne zaune a k'asan tattausan carpet d'in dake malale a k'asan falon sai d'aya gefen nata Habeeb ne shima a zaune a k'asa kowanne kanshi a k'asa. Kallonsu Ummi tayi d'aya bayan d'aya kafin ta tsaida kallonta kan Habeeb tace

“Abbuna Mujaheed ya kawomin k’ararka me yake faruwa ne?”.
Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace
“K’ara ta kuma Ummi?”.
“Yes” ta amsa masa, kai ya d’an d’aga ya jefawa Mujaheed wata uwar harara yace
“Me yace nayi Ummi?”.
“Yayi min complain akan yanzu ka daina maida hankalinka gaba d’aya aka aikinka sun rasa gane kanka”.
B’ata rai yayi sosai yace
“Ki daina yarda da maganar yaron nan Ummi munafuki ne so yake kawai ya had’ani dake”. Ido Mujaheed ya zaro tareda dafe bakinshi yana kallon Habeeb wanda yayi mirsisi kamar bashi ya fad’i maganar ba ya juyar ma da kanshi gefe yana faman kumbura baki.
“Babu wani zancen had’i ko munafunci ni kaina shaida ce kuma nasha tambayar ka abinda ke damunka saboda nakasa gane kanka a y’an kwanakin nan meye damuwarka ne Abbana”. tace cikin rarrashi tana shafa kanshi, ido ya d’an lumshe yace
“Ummiiii babu komai fa kawai dai…….”Wllhy k’arya yake Ummi ko last week saidaya janyo mana babbar asara a kamfani ko k’arya nayi?”. Mujaheed ya katse Habeeb yana hararar shi.
“Asara kuma? wace iri?”. Ummi ta tambaya.
Zama Mujaheed ya gyara yace
“Ummi wasu bak’i ne mukayi daga Abuja mun dad’e muna tsumayin zuwansu anata shirye shiryen zuwansu dayake wannan ne first time da zamuyi hark’alla dasu kuma akwai tarin alkhairai da mukesa ranshi ta dalilinsu, a ranar da zamuyi zaman dasu kowa ya hallara a d’akin taro damu dasu anata jiranshi ya fara magana kinsan me yayi Ummi?”. Kai ta girgiza kawai, saida Mujaheed ya harari Habeeb da shima yake hararar shi, cikeda takaicin abinda yayi musu ranar yace
“Wllhy Ummi d’an bawan ALLAHn nan kawai saiya tallafe hab’a ya d’ora d’aya kan d’aya yana kallon kowa d’ai d’ai dayake d’akin taron ko A baice ba, danaga haka nayi masa magana yak’i kulani sannan wani daga cikin ma’aikatanmu shima yayi masa magana yak’i kulashi shine sai d’aya daga cikin bak’in namu wani yayi magana dan sunfara gajiya da zama ga shugaban taro kuma baice komaiba, kamar jira yake wllhy Ummi ya hau kan mutumin nan da bala’i wai zai koya masa aikinshi ne daya dad’e yana yi ya dinga masifa duk ya hargitsa d’akin su kuma sukayi fushi sukayi tafiyarsu muka rasa wannan damar, sai gashi har ana rirrik’eshi wai zaiyi fad’a da mutumin, Ummi bansan meya canza Gashua haka ba mutumin dayake da salihi ko hayaniya baiso amma yanzu Ummi idan ya zage yana bala’i baza kice shi bane ya koyi wani zafin rai da masifa dan mutumin dayayi magana daga ma’aikatar tamu ranar da abin yafaru saidaya bashi suspension wai ya rainashi har yanzu bai dawo dashi ba”. Mujaheed ya k’arasa maganar yana kallon Habeeb da tunda ya fara maganar yake cije baki yana hararar shi baki ya tab’e yana d’an d’age kafad’a alamun ko a jikinshi.
“Haka akayi babana?”. cewar Ummi tana kallonshi, rasa abin cewa yayi sai k’asa dayayi da kanshi yana shafa k’eya.
Cikin b’acin rai Ummi tace
“Kanaso raina ya b’aci ne a kanka?”. Da sauri ya girgiza kai batare daya yi magana ba.
Kai ta kad’a tace
“To ka maida hankalinka kamar yadda kake a baya banaso in k’ara jin labarin ka k’ara yin wani abu dazai dinga ja muku asara a kamfanin ku saboda amana ce a hannunka, abinda duk yake damunka kuma ubangiji ALLAH yayi maka maganin shi tunda bazaka fito ka fad’amin ba a matsayina na mahaifiyarka”. A marairaice ya d’ago kai zaiyi magana ta dakatar dashi ta hanyar d’aga masa hannu tareda fad’in
“Ya isa haka tashi kuje ALLAH yayi muku albarka”.
Ba musu duk suka tashi suka fice, Habeeb ne a gaba Mujaheed na biye dashi a baya suna fita Habeeb ya nufi side d’inshi da sauri Mujaheed ya mara masa baya ko waigowa baiyi ba bare ya kalleshi yana shiga ya zube kan kujera ya d’age kanshi sama yana kallon roofing falon da adon fitilun da aka k’awatashi dasu.
“Meya shigo dakai nan?”. yace lokacin da Mujaheed ya shigo falon batare daya d’ago kaiba.
“Abinda ka shigo yi kaima?”. Mujaheed ya fad’a hankali kwance yana zama kusa da Habeeb d’in, d’agowa yayi yana fad’in
“Malam get out tun kafin in sauke fushina a kanka”. dariya Mujaheed ya k’yalk’yale da ita yace
“Ka dad’e baka sauke fushin naka ba a kaina Gashua yau bazan bar gidan nan ba saika fad’amin dalilin canzawar ka kodai har yanzu baby dream d’inka ke caza maka brain ne?”. Shirun da Habeeb yayi yasa yagane eh hakan ne da gaske canzawar shi tanada alak’a da yarinyar dake zuwa masa cikin mafarki k’aramin tsaki Mujaheed yaja yace
“Kuma dan ubanka saika dinga zuwa kana sauke mana, wadda zata caza maka k’wak’walwa daban mu kuma daba ruwanmu saikazo kana sauke mana kwandon masifa”.
Kai ya d’ago tareda lumshe idanunshi yana sauke numfashi gamida shafa sumar kanshi abubuwan duk sun had’u sun cakud’e masa ya yini yana tunanin yarinyar gidan Hajiya idan dare yayi kuma ta cikin barci tazo masa sun sashi a tsakiya ba dole aga canji a wajenshi ba?.
Mujaheed duk saiyaji tausayin d’an uwan nashi kuma abokinshi ya kamashi a hakan ma kuma baisan da labarin yarinyar zahiri ba, kafad’arshi ya dafa cikin taushin murya yace
“I’m so sorry Gashua ka cigaba da addu’a bata bar komai ba, ni kaina daba ni nake mafarkin nan ba abin ya fara damuna wlhy I’m sorry My brother”. Kai kawai Habeeb ya jijjiga masa yana had’iyar wani yawu mai d’aci.
“Tashi kaje ka shirya mu fita kasan yauma munada wani zaman da zamuyi saura kuma kaje kayi crossing legs kana kallon mutane d’ai d’ai ubanka zanci wllhy”. ya k’are maganar yana dariya.
“Nida kai zanga mai cin uban wani d’an iska kawai”. Habeeb ya fad’a yana mik’ewa tsaye ya wuce makeken bedroom d’inshi dan yin wanka. Bai dad’e ba ya fito cikin shigar manyan kaya sabuwar shadda ce fara k’al sai yarari take da d’aukar ido ko gwiwar shi rigar bata k’arasa ba tasha wani uban aiki da ash color d’in zare hakan yasa ya murza hula zanna wadda ta hau da zaren da akayi aikin sai takalmi mai mad’auri irin na maza shima ash color sai farin glass daya manna wanda ya k’ara fito da kyawun dayayi agogon dake mak’ale a hannunshi ma na fata ash ne sai wani azababben k’amshi yake fitarwa wanda ya karad’e dukkan falon tun kafin fitowarshi duk da girmanshi kuwa, fitowarshi yasa Mujaheed dake rik’e da waya a hannunshi ya d’ago kai ya kalleshi y’ar dariya yayi yace
“Wow Masha ALLAH so beautiful yanzu wazai ganka yace akwai wadda ke firgita ka cikin barcinka gaskiya koma wacece na jinjina mata”. ya k’arasa maganar yana mik’ewa tsaye tareda salute kamar wani d’an sanda.
“Useless man”. Habeeb yace yana binshi da harara yayi gaba yana d’auko wayarshi a aljihun gaban rigar wadda tafara wani sautin kid’a mai mai dad’in gaske alamun kira ne ya shigo ya fice yana amsa kiran Mujaheed ya bishi yana dariya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button