EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Afwan da kaɗan????????.

Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

No 28.

Duk abinda ake sam Neehlah batada masaniya kwananta biyu bata gidan tana gidan Aunt Mashhoodah data damu Ummi da waya tana roƙon ta Neehlah taje ta mata ko kwana biyu ne sai a yau ne ranar da Seeyamah tadawo gidan itama daf da magreebah driver’n Aunt Mashhoodahn yadawo da ita, lokacin Ummi da Seeyamah na zaune a falo Ummi na ɗan bata tarihinsu a taƙaice tareda nuna mata ta saki jikinta duk abinda takeso tayi magana.
“Oyoyo Umminah nadawo”. muryar Neehlah ta karaɗe falon tun kafin shigowar ta, murmushi kawai Ummi tayi tareda girgiza kai itama Seeyamahn murmushin tayi tasamu labarin ta yanzun nan a wajen Ummi, tsaye tayi tana bin Seeyamah da kallo bayan ta shigo falon tana tunanin abinda ya kawo Jawaheer Mansoor Jiƙamshi gidansu to wajen Ummi tazo ko kuwa dai wajenta tazo? to amma itafa ba shiri suke ba hasalima magana ta fatar baki bata taɓa haɗasu ba saboda Jawaheer muguwar ƴar rainin wayo ce sam basa shiri…..”ƙaraso mana”. Ummi ta katse mata tunanin datake, kusa da Ummi ta ƙarasa ta zauna har lokacin bata daina tunanin abinda ya kawo Jawaheer gidansu ba.
“Ummi Aunt Mashhoodah tace tana gaisheki”.
“Ina amsawa ya kika barosu da yaran?”.
“Lafiya ƙalau wllhy, Noor mafa harda kukanta wai saita biyoni kuma matsalar akwai school gobe amma tace weekend driver zai kawota ta kwana biyu”.
“ALLAH ya kaimu, bakiga baƙuwa bane Neehlah?”. cewar Ummi tana kallon Seeyamah data sadda kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta murmushi ɗauke a fuskarta.
“Na ganta Ummi a ina kika samota?”. A taƙaice Ummi ta bawa Neehlah labarin abinda ya faru duk da dai bata faɗa mata cewa Habeeb ne yasa aka kama ta ba, sosai Neehlah tayi mamaki jin ba wadda take zato bace wata ce daban jin tayi shiru yasa Ummi tace
“Ya kikayi shiru ne?”.
Sai data ƙara kallon Seeyamah sosai taga dai basuda bambanci da Jawaheer sannan tace
“Ummi abin ne akwai ban mamaki a school ɗinmu fa akwai wata irinsu ɗaya da wannan wllhy ba abinda ya rabasu komai fa Ummi I’m confused wllhy”.
“Ikon ALLAH dama haka lamarin ubangiji yake ai wasu ma ba ƴan gari ɗaya bane sai kiga kamannin su yazo ɗaya”. Kai kawai Neehlah take gyaɗawa tana ƙara karantar yanayin Seeyamahn wadda har yanzu batayi magana ba.
“Ga ƴar uwa nan nakawo miki yadda kike da damar yin komai a cikin gidan nan itama tana da wannan damar kar in sake inji wani abu ya ɓullo daga wajenki yanzu amana take a wajen mu”.
“Insha ALLAH Ummi”. Neehlah ta faɗa tana tashi ta koma kusa da Seeyamah ta zauna tana murmushi.
“Kema Seeyamah ga Neehlah nan kamar yadda na faɗa miki itace ƙarama duk abinda tayi miki ba daidai ba ki sameni ki faɗa min ALLAH ya haɗa kanku yayi muku albarka”.
Da Amin suka amsa gaba ɗayansu Neehlah ta miƙawa Seeyamah hannu suka gaisa kowacce da murmushi saman fuskarta jin an fara kiran sallah yasa Ummi ta miƙe tsaye tana faɗin
“Oya aje ayi sallah tayi amfani da wannan bedroom ɗin na kusa da naki kaya ma tafara using naki tunda naga kusan size ɗinku ɗaya kafin ayi mata siyayyar nata”. sosai Neehlah ta shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka tace
“Haba Ummi inama laifin kice muyi using bedroom ɗaya dama fa ya min girma”. murmushi Ummi tayi tace
“Ba matsala ta zauna a naki bedroom ɗin shikenan?”. cikeda murna Neehlah ta rungume Seeyamah tana dariyar farin ciki harga ALLAH dama zaman gidan nan yana mugun ci mata tuwo a ƙwarya tana shan zaman kaɗaici ba laifi gidan kawu Sulaiman ne dama gurin zuwanta kuma shi ƴaƴan shi duk maza ne matan basuda yawa kuma duk sunyi aure tun ma acan Yoben shiyasa har bataso weekend yayi gara idan da school ɗin tana ɗebe mata kewa.
“Thank you Ummi”. tace tana miƙewa tsaye tareda kama hannun Seeyamah suka nufi upstairs inda bedroom ɗin Neehlahn yake Ummi ta bisu da kallo tanajin farin ciki mara misaltuwa yana ratsata haƙiƙa taimakon maraya ba ƙaramin lada gareshi ba aiki ne mai kyau ƙwarai da gaske, itama upstairs ɗin ta hau ta nufi nata bedroom ɗin dan bada farali.
Babban bedroom ne sosai wanda har Seeyamah ta dinga mamakin ace na Neehlah ne kawai ita kaɗai lallai masu kuɗi sunajin daɗinsu, tamkar ɗakin wata matar auren bed, wardrobe, mirror da sauran abubuwan ƙawata ɗaki na masu kuɗi sai ƙamshi yake na turaren wuta.
“Bismillah ga bathroom shiga ki fara yin alwalah”. Neehlah ta faɗa tana nunawa Seeyamah wata ƙofa dake cikin bedroom ɗin, inda ƙofar take ta nufa da niyyar shiga Neehlah ta biyota da sauri tana faɗin
“Oh my God! Seeyamah ki cire babban hijabin nan mana please bakyajin ya dameki ne?”. Bata saurari abinda Seeyamahn zata faɗi ba ta fara ƙoƙarin cire mata shi da kanta bata hanata ba ta tayata cirewa.
“Yauwa koke fa Sisi”. Neehlah tace tana jefa hijabin kan bed, itadai murmushi kawai tayi ta shige toilet ɗin.
Ta daɗe tana ƙarewa bathroom ɗin kallo saboda yadda aka ƙawata shi kamar ba toilet ba (dan ma bakiga na oga ɗan kidnapping ba ????).
Alwalah ta ɗaura ta fito ta tarar har Neehlah ta shimfiɗa mata pray mat murmushi kawai suka sakarwa junansu ba tareda wani yayi magana ba Neehlah ta ɗauko hijabin ta miƙa mata sannan itama ta shiga toilet ɗin Seeyamah ta bita da kallo familyn sun burgeta sunada kirki da sanin darajar ɗan adam amma shi wancan meyasa duk bashida su ko kaɗan bashida mutunci da tausayi bai biyo halin mahaifiyarsa ba gaskiya ganin dai tunanin bazai yimata ba tasa hijab ɗin ta kabbara sallah, itama Neehlah bata daɗe ba ta fito wata dardumar ta shimfiɗa kusa da Seeyamah ta ɗauko hijab a wardrobe ta tada tata sallahr.
Bayan sun idar ma hira suka cigaba dayi duk da dai duk rabin hirar Neehlah ce Seeyamah bata cika magana ba sai murmushi kawai datake tana jin ƙaunar ahalin har a jinin jikinta.
Suna nan zaune sukaji an kira sallahr Esha’e dan haka suka tashi suka gabatar da tasu suka ƙara zaman wata hirar, system ɗinta Neehlah ta jawo tana faɗin
“Bari kiga sister na dana dawo daga gidanta yanzu da kuma Big Bro ɗinmu gaba ɗaya”. kafin ma Seeyamah tayi magana Neehlah ta buɗe system ɗin tasa password ta shiga ɓangaren hotuna inda pic ɗinta ne kawai dana Ummi da Aunt Mashhoodah sai mai gayya mai aiki Habeeb.
“Masha ALLAH Aunt Mashhoodah tafiki kyau gaskiya”. Seeyamah tace tana ƴar dariyar tsokana, tuni Neehlah ta haɗe fuska tana jefawa Seeyamah hararar wasa kamar zatayi kuka tace
“Dama ta ina zaki haɗamu? su fa acan Dubai aka haifesu itada Yah Habeeb nikam 9ja bansan meyasa aka haifeni anan ba”. dariya sosai Seeyamah tayi tace
“Dama mutum yana zaɓar inda za’a haifeshi ne?”.
“Inafa amma nidai banso ba wllhy a rasa inda za’a haifi mutum sai Nigeria”. ta ƙarasa maganar tana wani taɓe baki, dariya Seeyamah tayi tana cigaba da duba hotunan tana murmushi tana yin next idanunta suka faɗa kan pic ɗinshi yana tsaye kusa da wani ƙaton tamfatsetsen building daya gaji da haɗuwa sanye yake cikin Italian suit dark blue sai shirt ɗin ciki data kasance white color hannayenshi duka suna sanye cikin aljihun wandonshi ya toshe idanunsa da black shade tamkar wanda baisan ma za’a ɗauki pic ɗin ba dan hankalin shi gaba ɗaya baya kan mai ɗaukar hoton can wani gurin yake kallo daban, daga yadda tsarin wajen yake da irin mutanen dake wajen zai tabbatar maka da ba’a 9ja aka ɗauki hoton ba yayi matuƙar yin kyau duk da fuskarshi ba’a sake take ba haka yanayin tsayuwar tasa ma ta bada citta, haka nan Seeyamah ta tsinci kanta da faɗuwar gaba mai tsanani ido ta ɗan lumshe tayi saurin buɗewa saboda Neehlah dake wajen ita sam Neehlahn ma bata lura da yanayin da Seeyamahn ta shiga ba a lokacin ta fara faɗin
“Big B kenan miskili kafi mahaukaci ban haushi kin ganshi nan shine babban yayanmu”. Kai kawai Seeyamah ta kaɗa batace komai ba ta cigaba da dubawa duk pics ɗinshi ne kala kala a mabanbantan gurare mafi yawa ma duk ba’a Nigeria aka ɗauka ba gaba ɗaya ba wanda aka ɗauka yana dariya kowanne fuska a tamke kuma hakan baya hana yayi kyau baifi guda biyu tagani ba wanda ya ɗanyi murmushi, tana shirin tambayar Neehlah shikam baya dariya ne taji muryar Neehlahn tana faɗin
“Haka fa yake baya dariya shi murmushi ma saita kama yake yinshi kullum ta ALLAH fuska a tamke yana baƙin rai kuma yafiso yadda yake kowa ma ya zauna a haka ko dariya fa akayi a gabanshi saiya kori mutum na rasa irin halinsa Mr ɗacin rai kenan”. ta ida maganar tana dariya, itama Seeyamah ƴar dariyar tayi a ranta take faɗin
Lallai na tabbatar kuwa ko ita ɗin nan da bata daɗe da sanin shi ba bata taɓa ganin dariyar shi ba ya iya dai mugunta yasan ta kanta.
“Kinsan ai kowa da yanayin yadda ALLAH yake halittar sa wasu masu fara’a da sakin fuska wasu kuma akasin haka”.
Baki Neehlah ta taɓe tace
“Nashi fa daban ne Sisi ALLAH Yah Habeeb da wuya kiga haƙorin shi a waje kullum a cunkushe kamar wanda baijin daɗin rayuwa ni wllhy ma na matsu yayi aure yabar min gidan in wataya abina”. Seeyamah zatayi magana kenan aka buɗe ƙofa Ummi ta shigo tana murmushi tace
“Oh Neehlah kina nan kin tsareta da surutun nan naki ko? a fito maza ayi dinner”. haɗa baki sukayi wajen amsa mata ta juya ta fita Neehlah ta rufe system ɗin ta tashi tsaye Seeyamah ma ta miƙe suka fita duk jinta take wani iri daban kamar ba ita ba ba haka ta saba da rayuwar ta ba yau ɗaya ALLAH ya canza mata.
Dinning area suka nufa inda Ummi take zaune, Neehlah tajawa Seeyamah kujera ta zauna sannan ya fara serving ɗinsu.
“Ummi banga Yah Habeeb ba?”. Neehlah tace bayan tagama zubawa kowa ta zauna
“Ƙyaleshi kawai yau baiyi niyyar yin dinner ba”. tana faɗa taja plate ɗin gabanta ta fara cin abincin Neehlah ma bata ƙara magana ba kowa ya maida hankali kan abincin dayake ci.
Da suka gama ma cikin falon suka koma suka zauna suna kallo jefi jefi suna ɗan taɓa hira.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button