EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Mrs Salees Mu’az ????

EL–HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 12.

 Saida suka fara biyawa ta gidansu Mujaheed suka saukeshi sannan suka wuce.

 Zaune yake kan kujera bayan yagama shan coffee'n nashi na k'aidah, daga shi sai farin boxer ya hard'e k'afafunshi dare ne sosai dan k'arfe biyu ma ta kusa ya gaza samun barci sam sau biyu yana kwanciya barcin yana gagarar shi dan haka ya tashi ya shiga bathroom ya d'auro alwalah yazo ya gabatar da nafilah raka'a hud'u yayi addu'oen shi ya had'o coffee ya zauna kan kujera ya shiga sha duk da irin turirin dayake fitarwa haka yasha yana k'ona masa baki sai kace dole, bayan ya gama sha kuma yayi zaune yana sak'a da warwara kan abinda ya dace yayi duk da dai tun cikin mota ya gama yanke hukunci kan abinda zai aikata saidai yana ganin kamar ba daidai bane abinda shirin yin amma a halin yanzu dai bashida wata dabara data wuce yayi hakan idan ma mutum d'aya ce zai sani koma dai meye zai sani.

Da wannan shawarar ya kwanta bayan addu’oen dayayi har barci yayi galabar d’auke shi.
Wata sabuwa.
Kamar yadda ta saba zuwa masa cikin barcinshi yau d’inma tazo bayan barci ya d’auke shi kuma a yau yayi nasarar ganin fuskar ta, duk da a cikin barci ne ya ganta amma yayi matuk’ar razana fuskar daya gani ta matuk’ar girgizashi dan ba wata bace illa wannan yarinyar fuskarta yagani muraran tana jifanshi da wani irin shu’umin murmushi wani kallo take masa wanda ya kasa fassara shi. Wata irin zabura yayi ya tashi zaune yana ambatar sunan ubangiji yana sauke wani irin numfarfashi tamkar wanda yake filin tsere yayin da zuciyarshi take wani irin zillo tamkar zata fito waje tsabar yadda take bugawa sai gumi ne yake tsattsafo masa ta ko ina.
Zaune yayi a tsakiyar gadon ya kasa koda motsa d’an yatsanshi ne, dama wannan yarinyar ce datayi shekaru tana azabtar dashi cikin barcinshi ta hanashi sukuni da jin dad’in barci kamar yadda kowa yake ji.
Idanunshi ya rufe yana k’ara hasko fuskar tata wani haushin ta yakeji, lips d’inshi ya cije tamkar zai hudashi ya sauka daga kan gadon ya shiga zagaye bedroom d’in
Tofah!!! wata sabuwa inji y’an caca shin a cikin su ukun wacece yake mafarki da ita tsahon wannan lokaci? Heedayah? Seeyamah ce? kokuma waccan wadda har yanzu ba aji sunanta ba??? gareku reader’s.

Bai ankara ba yaji har har anfara kiran sallahr asubah lallai ba k’aramin lokaci yaja cikin duniyar tunani ba gashi har an kira assalatu, bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya d’aura alwalah ya fito ya zura jallabiyyah ya fita masallaci. Bayan dawowar shi ya kwanta saboda idanunshi da suke masa zafi saboda rashin barci gashi duk sunyi ja sun d’add’aga, bai dad’e da kwanciya ba kuwa wani irin barci mara dad’i ya kwashe shi shi kad’ai yasan yadda yakeji a cikin zuciyarshi.
Washegari da wani zazzafan zazzab’i ya tashi ga wani masifaffen ciwon kai daya addabeshi duk yadda yaso ya tashi yayi shirin office kasawa yayi dan haka ya cigaba da kwanciya cikin tattausan blanket d’in daya lullub’a a ciki sam kuma baiyi hausar kiran Ummi ya fad’a mata ba.
Ganin shiru shiru bai shigo gidan kamar yadda ya saba ba yasa Ummi taji hankalinta yak’i kwanciya tasan indai lafiya to yanzu ya shirya ya fito har sun gaisa ya tafi office, tasan halin babanta sarai yanzu haka wani abun ne ya d’auki waya ya kirata shine abin ya gagara ya gwammace yayi ta kwanciya a d’aki batasan wani irin hali gareshi haka ba zurfin cikinshi yayi yawa.
Wasu y’an mintunan ta k’ara ko zai shigo amma shiru dan haka ta tashi da kanta ta fita zuwa side d’in nashi dan Neehlah tana school bare ta aikata ta gano mata shi.
Tayi sa’a tana tura k’ofar falon ta bud’e dan lokacin daya dawo sallahr asubah baisa key ba turata kawai yayi, shiru falon sai k’arar air conditioner dake ta aiki da k’amshin shi na musamman da gaba d’aya side d’in nashi yake d’auka.
Kai tsaye bedroom d’in ta nufa ta tura k’ofar ta shiga, tun daga k’udundunewar dataga yayi tasan ba lafiya ba ga kuma A.C daya k’ureta gaba d’aya bedroom d’in ya d’auki wani uban sanyi mai ratsa jiki, saidata kashe air conditioner d’in sannan ta nufi gadon ta tsaya tareda d’an janye blanket d’in fuskarshi ta bayyana yayi saurin bud’e idanunshi ya zubasu kan Ummi dake tsaye wadda saida gabanta ya fad’i saboda ganin yadda idanunshi suka canza launi gaba d’aya gashi sun kumbura, cikin harshen larabci take tambayar shi me yake faruwa?. mayar mata da amsa yayi da yaren datayi masa magana ya fad’a mata abinda yake damunshi d’an k’aramin tsaki taja tace
“Abbuna kanada matsala wllhy yanzu saboda ALLAH kana cikin irin wannan halin amma ka gaza kirana a waya ka sanar dani? yanzu akan lafiyar taka ma sai kayiwa mutane zurfin cikin?.
“I’m sorry Ummi”. yace cikin rawar murya mai data shagwab’a, kai kawai ta d’an girgiza ta samu gefen gadon ta zauna ta fara laluben number a wayarta Dr Huzaifah shine asalin family doctor d’insu dayake dubasu tun bayan dawowar su Nigeria tun ma da ran Abbu, shi ta kira ta sanar dashi Abbanta ba lafiya yayi hanzarin zuwa ya dubashi ya amsa mata da gashi nan zuwa yanzu.
Tashi Ummi tayi ta fita bayan ta k’ara ja masa blanket d’in har kanshi, tea ta had’o masa mai kauri wanda yaji had’e had’e irin nasu na Arab bata had’o masa da wani abun ba dan tasan kota had’o dashi ba ci zaiyi ba tea d’inma tasan sai tayi fama dashi haka yake kamar k’aramin yaro idan bashida lafiya.
Aikuwa kamar yadda Ummin ta ayyana da k’yar yasha ruwan shayin bayan dogon faman datasha dashi duk ya wani shasshake mata duk abinda yake kuma duk abin nan dayake tunanin nan yana manne da zuciyarshi so yake kawai ya tashi yasan abinyi (Gashua jarabar duniya bakada lafiyan ma ????).
Kusan a tare Dr Huzaifah da Mujaheed sukazo gidan dan Dr Huzaifah yana shigowa ko rufe gate d’in maigadi baiyiba motar Mujaheed ta kunno kai, anan farfajiyar gidan suka had’u suka gaisa sannan suka nufi side d’in Habeeb wanda ke cikin compound d’in.
Baki suka had’a wajen yin sallama Ummi ta amsa musu suka shiga suka gaisa da Ummi Mujaheed yace
“Ashe Gashua ba lafiya Ummi?”.
“Wllhy Mujaheed, zazzab’i ne da ciwon kai suke damunshi”.
“Ayya ALLAH ya k’ara afwah, ai tunda naje company naga ban ganshi ba nace to ba lafiya dan indai lafiya lafiya wannan Mr business d’in baya makara nayi trying number shi kuma switch off shine nazo ingani saikuma na had’u da Dr shima yazo”.
Y’ar dariya kawai Ummi tayi jin sunan da Mujaheed ya kira Habeeb dashi wai Mr business, tashi tayi tace
“Bari inje Mujaheed tunda gaka ka kula dashi please Dr ayi masa duk abinda ya dace”.
“Insha ALLAH”. Mujaheed da Dr Huzaifah suka had’a baki wajen fad’a, ta fita taja k’ofar.
Tashi yayi zaune yana cije baki saboda kanshi dake masa wani mugun ciwo da k’yar yake bud’e ido, Mujaheed ne yasa masa pillow a bayanshi ya jingina.
“Sannu Gashua how are u feeling now?”. cewar Mujaheed yana zama a bakin gadon.
“Alhmdulillah”.
Yace yana lumshe idanunshi.
“ALLAH ya k’ara lafiya”. Kai kawai ya gyad’a masa shima Dr Huzaifah yayi masa ya jiki tareda tambayar shi abinda yake damunshi
“Zazzab’i ne sai kaina yana min ciwo sosai inajin kamar zai fad’o”. yayi maganar yana dafe kanshi wanda yafi takura masa sosai.
“Oh sorry insha ALLAH zaiyi sauk’i fatan ka sawa cikinka wani abu?”. Dr Huzaifah ya fad’a yana fito da kayan aikinshi daga jaka.
Kai kawai ya kad’a masa batare dayayi magana ba.
Sosai Habeeb ya had’e rai yana wani yamutsa fuska ganin Dr Huzaifah yana had’a injection a rayuwar shi ya tsani allura kuma tun asalinshi haka yake lokacin da yana k’aramin yaro.
Bakin gadon Dr Huzaifah ya k’arasa yana fad’in
“Bismillah Mr. Habeeb Gashua”.
“Ka sani fa bana son wannan abin please ka bani magani kawai Dr”. yayi maganar yana cin d’aci da yatsina fuska.
“A’a kar muyi haka dakai mana d’an balarabe nayiwa Ummi alk’awarin zan baka dukkan kulawar data dace kuma allurar nan itace best solution dan sam zazzab’in ba magani yake jiba”.
“Wai Gashua allurar kake wa wannan goce gocen saikace wata mace? haba karka bada maza mana dan ALLAH”.
Duk da yanayin dayake ciki na jin jiki saidaya dallawa Mujaheed harara kafin ya juyo inda Dr Huzaifah yake tsaye da allura a hannunshi.
“Haka nan dai zaka daure mutumina”. cewar Dr yana y’ar dariya dan mutum ne mai wasa da dariya.
Haka nan yana ciccin magani ya shiga nad’e dogon hannun jallabiyyahr dake jikinshi, Mujaheed sai matse dariyar shi yake yana kallon Habeeb wanda yanayin shi ya nuna kamar wanda zai saki kuka.
Matsawa Dr Huzaifah yayi ya saita inda zaiyi masa allurar a hannunshi, runtse ido yayi gam Dr Huzaifah ya tsira masa a inda ya dace.
“Ahhhhshh”. ya fad’a lokacin da allurar ta shiga jikinshi ya k’ara runtse idonshi yana k’ara damk’e hannun da akayi masa allurar da d’aya hannun kamar zaiyi kuka.
“Ahhh kajimin wani sabon iskanci Dr allurar kakewa haka Gashua?”. Mujaheed yace yana bud’e baki da sakin dariya.
Dariya Dr Huzaifah yayi yace
“Ai kad’an ka gani Mujaheed indai Habeeb ne da allura last rashin lafiyar dayayi da ulcer shi ta tashi danayi masa I think har kuka ma saida yayi time d’in”.
“Ah haba dan ALLAH”. Mujaheed ya fad’a yana zaro ido na shegantaka.
Kai Dr ya jinjina masa yana dariya gami da d’auko drip yana neman inda zai sak’alashi.
Cikin dariya Mujaheed yace
“Kutt amma dai anji kunya wllhy ka bada maza wllhy dan ubanshi saiya fita yayi tayiwa mutane muzurai a waje yana tsorata yaran jama’a amma allura kad’ai tana girgizashi ALLAH ya kyauta maka to”.
Babu wanda ya kula a cikinsu sai zamewa dayayi ya kwanta yana sauke numfashi har lokacin yanayin fuskarshi bata gama daidaita ba. Drip d’in yasa masa sannan ya rubuta magunguna yaba Mujaheed takardar yace a siyo su idan drip d’in ya k’are Mujaheed ya cire masa sannan ya k’ara samun abinci yaci, daga nan yayi musu sallama ya fita Mujaheed yana k’ara yimasa godiya.
Nan Mujaheed ya cigaba da zama da Habeeb duk dama dai barci ne ya d’auke Habeeb d’in Ummi ma ta k’ara shigowa ganin jikin nashi ta sameshi yana barci, fita tayi tana yiwa Mujaheed sannu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button