EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

A ranar da dare bayan yagama da duk wasu abubuwa daya saba gabatarwa kafin ya kwanta kamar yin wanka gabatar da sallah raka'a biyu da addu'oe shan coffee brush da sauran ƴan abubuwan daya saba yi kafin ya kwanta, yau ɗin ma bayan duk hakan ta kasance ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya barci, ya rufe ido bayan gama karanto addu'ar saurin buɗewa yayi saboda gano Heedayah dayayi kuma ba abinda yake gani irin bakinta lokacin datake faɗa masa nunar rana, tsaki yaja ya buɗe idanunshi ya ƙara juyawa ɗaya gefen tareda ƙara rufe ido still dai ƙaramin bakin nata ya ƙara gani wanda yasha lipstick yaketa shining yayin datake ta juyashi tana magana.

“Yaa Ilahee”. yace ƙasa ƙasa yana dafe goshinshi gaba ɗaya haushin kanshi ya kamashi me yake damunshi haka ne? ALLAH idan ya kama yarinyar nan sai taji ba daɗi baisan ma wane kalar hukunci zaiyi mata ba kawai dan tsabar mugunta tazo zata hanashi barci hakan na nufin duk mafarkin dayake a can baya ita ce kenan?.
Ƙananun tsaki ya dinga ja yana juye juye da cije lips da ƙyar yasamu barci ya kwashe shi a wannan rana batare daya daina ganin Heedayahn cikin idanunshi ba.

★★★__★★★
Washegari bayan ya taso daga office kai tsaye inda ake ginin ɗaya kamfanin nasu ya wuce yaga yadda ginin yake tafiya yayi nisa ma sosai abinka da akwai kuɗi zubasu kawai ake.
Daga nan babban shagon da Muhammad yake mallakin Alhaji Sulaiman ya nufa, sosai yaran shagon suka dinga girmama shi sai miƙa gaisuwa suke saboda sun san ko waye sun san kuma kusancin dayake dashi da mai wajen, hannu kawai ya ɗaga musu duk yawansu ya nemi da ayi masa iso wajen manager.
Bayan gaisawa da sukayi Habeeb ya nemi Muhammad daya bashi address ɗin gidan matar shi a Katsina zaije yayi wani bincike a can ya tattauna kuma da iyayen matar tashi, Uncle Muhammad yaso musa masa amma tsabar yadda ya cika masa ido da kwarjinin dayayi masa a idanunshi yasa take ya rattaba masa kwatancen gidan shima zuwa yanzu ya fara tunanin anya bata hanyar Mr Habeeb Gashua ɗin za’a gano asalin iyayen su Heedayah ba? wannan ai abin farin ciki ne a gurin Heedayahn dasu kansu su Baban dan haka baiji ko ɗar ba yana sa ran insha ALLAH ta sanadin Habeeb ɗin a gano real parents ɗinsu Heedayahn.
“Thank you so much”. Abinda yace kenan ya tashi yabar office ɗin Uncle Muhammad ya bishi da kallo shifa har yanzu tunani yake meyasa Mr Habeeb ɗin yasa kanshi cikin wannan lamarin?.

Safiyar talata.
Bayan yayi shirin fita office ya shiga gaida Ummi kuma yayi breakfast kamar yadda ya saba, bayan yayi breakfast ɗin yana shirin fita Ummi tace ya tafi da Neehlah ya sauketa a school kasancewar har zuwa yanzu driver’n nasu bai dawoba Monday ma saboda batada lecture ne shiyasa bataje ba, ficewa yayi yana faɗin ta fito yana jiranta kar ta ɓata masa lokaci.
Dama tunda Neehlah taji Ummi tace shine zai yi drooping ɗinta ta shirya da wuri gudun samun matsala dan Yah Habeeb ba uzuri zaiyi mata ba….

Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????
09139964697

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

No 35.
Last page.

Neehlah na shiga motar ya figeta da uban gudu kamar yadda ya saba dama already maigadi ya riga ya buɗe masa gate, ko tari Neehlah batayi ba tunda suka tafi ba abinda ke tashi cikin motar sai sautin karatun Alqur’ani mai girma dake tashi kaɗan kaɗan cikin ƙira’ar Khusary wadda yake biyo farkon suratul Ma’idah.
A bakin gate ɗin makarantar su Neehlah SKY LINE UNIVERSITY dake cikin birnin Kano yayi parking bai shiga ciki ba. A ɗan tsorace Neehlah ta ɗan saci kallon shi alamun neman ƙarin bayani.
“Get out”. yace ba tare daya juyo ya kalleta ba, kamar zatayi kuka tace
“Yah Hab……”I said get out from my car”. ya katse ta cikin ɗaga murya ba shiri ta buɗe murfin motar ta fita yayi reverse ya cilla motar kan titi yabar wajen tana tsaye tana kallonshi yau kuma haka ALLAH yayi da ita ji yadda ya watsar da ita anan kamar kayan wanki ta saba kullum driver ya kaita har cikin makarantar ya sauketa cikin girmamawa da mutunta wa ita wllhy ma matar dazai aura take tausayawa ta shiga uku gaskiya ba fata dai take mata ba koma wacece shi iya masa sai ALLAHn daya halicce shi ina rayuwa zata yiwu a haka?
Baki ta taɓe ta nufi gate ɗin tana gyara side bag ɗinta ta shiga cikin school ɗin.
Tun daga wajen ajiye motoci na cikin kamfanin ake ta faman miƙa masa gaisuwa kamar yadda ya saba ɗaga musu hannu yauma hakan yayi ya shige cikin kamfanin cikin zafin nama da wadatacciyar lafiya da ubangiji ya hore masa yana shiga kowa ya nutsu waɗanda suke tsaye suka zazzauna kowa ya maida hankali kan aikin dayake, kalaman barka da zuwa ne kawai ke tashi lokacin daya shiga sun riga sun saba da yanayin amsa gaisuwar tashi dan haka ba wanda ya damu kowa ya cigaba da aikin gabansa.
Lifter ya hau zuwa 1st floor inda office ɗinshi yake ya buɗe ya shiga, a gyare tsaf ko ina ƙal-ƙal tamkar ba’a amfani dashi sai tashin ƙamshi mai daɗi yake, brief case ɗin ya ajiye kan babban table ɗin dake office ɗin sannan ya zauna kan kujerar yana zama yayi baya ya kwantar da kanshi kan kujerar yana sauke numfashi lokaci ɗaya yana rufe idanunshi tareda jujjuyawa kan kujerar.
Buɗe ƙofar da akayi baisa ya buɗe idanunshi ba dan yasan ko waye mutum ɗaya ne yake da damar yin hakan a duk faɗin kamfanin wato Mujaheed.
Motsin da bakinshi yayi ne kawai ya tabbatarwa da Mujaheed ya amsa amsa sallamar dayayi idan da sabo ya saba shikam wane hali ne na Gashua bai sani ba?.
“Welcome Mr. Habeeb Gashua”. Mujaheed ya faɗa yana zama kan ɗaya daga cikin kujeru biyun dake kallon wadda Gashuan yake zaune tare da zube wasu tarin pepper’s akan table ɗin, ɗagowa yayi yana buɗe idanunshi ya kalli Mujaheed kamar bazai yi magana ba saikuma yace
“Mr. Mujaheed Yusuf meya hanaka shigowa Company jiya?”. cikin tsare gida yayi maganar yana janyo computer ya buɗe ya fara danne danne a ciki.
“I’m sick”. Mujaheed ya bashi amsa.
“Why did you call me?”. yace har lokacin bai daina latse latse a laptop ɗin ba, shegen wato yau dai ƴan rashin mutuncin ne a kanshi Mujaheed ya ayyana hakan cikin ranshi kafin yace
“Wai Gashua me yake dam…….”Look MJ I’m still your Boss karka kawomin maganar banza mana”. Yace a zafafe yana kauda laptop ɗin gabanshi gefe.
“Toooh yau kuma da haka kazo? dan ubanka nabi Boss ɗin da gudu ba wando kai meyasa bakada uzuri ne a rayuwar ka Gashua? ni dalla malam kayi min signing a takardun nan in tafi inada aikin yi a gabana”. ya ƙarasa maganar yana harararshi, shima hararar ya jefa masa kafin ya janyo takardun yayi sign, Mujaheed ya miƙe ya ɗauke su ya fita yana maganganu wanda bayajin abinda yake faɗa amma ya tabbatar iskanci yake masa ƙwafa yayi a fili yace
“Ubanka zanci very soon wllhy”. System ɗin ya janyo ya cigaba da aikinsa a ciki.

Neehlah ba ƙaramin ruɗu da tarin al’ajabi ta shiga ba lokacin da Jawaheer Mansoor Jiƙamshi ta shigo cikin school ɗin exactly ba abinda ya rabasu a komai da Seeyamah har yanayin maganar su kuwa bambancin kawai ita Seeyamah cikin sanyin murya take maganar ta wanda hakan ya kasance kamar halittar ta ne hakan, saɓanin Jawaheer dake magana gatsal gatsal ba alamun rissinawa anya babu wata alaƙa kuwa tsakanin Seeyamah da Jawaheer ɗin? tunanin data dinga yi kenan har zuwa lokacin da suka shiga lecture.

Da wuri yabar office ranar, yana kan hanya ma Ummi tayi masa waya yaje ya ɗauko Neehlah daga school ƙiri ƙiri dai Ummi ta maidashi driver’n ƙarfi da yaji dole ya canza akalar tafiyar tashi zuwa school ɗin su Neehlahn.
Tunda ya shiga cikin school ɗin idanun ɗalibai da yawa suka dawo kan motarshi ana jiran aga wanda zai fito daga wannan zuƙeƙiyar motar saidai ko buɗewa ba’a da alamun yi, Neehlah da sai yanzu ta hango motar tayi saurin yin sallama da ƙawarta Haneefah Isma’eel ta nufo wajen motar.
Waya yake lokacin data shiga motar cikin sautin muryar shi mai cike da amo mai haɗe da sanyi cikin tataccen speech yake maganar cikeda ƙwarewa, kamar ance ya kalli gefenshi ya hangeta tana shirin shiga motar ta da niyyar barin school ɗin ido ya ɗan zaro yana ƙare mata kallo da tunanin dama a school ɗin su Neehlah take? magana ake tayi masa daga can ɓangaren wanda suke wayar amma sam bayajin abinda yake faɗa ganin har ta shiga ta tayar da motar tana shirin barin wajen yasa cikin sauri yace
“I will call you back Mr Williams”. Daga haka ya kashe wayar zai cillata front seat yaga Neehlah a zaune sam ya manta ma da ita a motar tsaki yaja yace
“Get out kisamu abin hawa ya maidaki gida yanzu”. Yace yana karkacewa ya zaro kuɗi a aljihunshi na gefe 5k ya wurga mata.
“Get up”. Yace cikin tsawa yana zare mata ido ganin tana shirin yin magana kar ta ƙara ɓata masa lokaci, kamar zatayi kuka ta buɗe murfin motar ta fita ya juya kan motar lokacin Jawaheer ta fita daga gate ɗin makarantar ya rufa mata baya ba tare data lura ma wani yana bin bayanta ba.
Tsaye Neehlah tayi ta bishi da kallo harya fita daga cikin makarantar cikin tsananin jin haushi da takaici kamar ta ƙwala ihu wllhy abinda mutumin nan yake sam baya kyautawa tun farko ma daya sani haka yace ta tafi basai ta shiga ba ya fito da ita yau dai tana ganin rayuwa, kafaɗar ta da aka dafa daga bayanta yasa ta juya dan ganin ko waye taga ƙawarta Haneefah ce take tambayar ta lafiya harta shiga motar ta fito?
“Hmm kedai rabani da halin mutumin can haka fa ɗazu nace miki bakin gate ya zubeni ya ƙara gaba abinsa yanzu kuma yace wai ina fito in nemi abin hawa ALLAH kamar Ummi taji ta gama ne”. ta ƙarasa maganar cikin tura baki kamar zata saki kuka.
Ƴar dariya Haneefah tayi tace
“Ai kedai ki bari kawai Bestie sam irinsu basuda daɗin sha’ani nima muna nan da wani yayanmu Yah Khaleel wllhy shima haka yake da abin haushi haka muke fama amma dai gaskiya bai kai wannan Yah Habeeb ɗin naki ba”.
“ALLAH shirye su to”. Neehlah tace tana taɓe baki, daidai lokacin Haneefah ta hango motar gidansu anzo ɗaukar ta hannun Neehlah ta kamo tana faɗin
“Yauwa ga Isah nan ma yazo ɗauka na kizo muje kawai sai muyi drooping ɗinki zuwa gida”.
“Kai Bestie ba za’ayi haka ba ba hanyar mu ɗaya bafa kije kawai zan fita in samu drop ɗin napep”.
“No please kizo kawai meye abin wahala a ciki”. kafin tasamu zarafin magana Haneefah taja hannunta zuwa gurin motarsu ta sanar da direban zasu fara ajiye ƙawarta a gida kafin su wuce cikin girmamawa ya amsa ya buɗe musu suka shiga ya tada motar suka bar harabar makarantar.
Tiryan tiryan yake bin bayan Jawaheer har zuwa unguwar su saidaya tabbatar yaga gidan data shiga da motar ta sannan yayi reverse ya koma da niyyar zai ƙara dawowa ya ɗora da binciken shi.
Tsoro ya hana Neehlah faɗawa Ummi yadda akayi yau da Yah Habeeb da zai kaita da lokacin dayaje ɗaukota kamar yadda da ta ƙudurta tana dawowa zata faɗa mata tasan dai idan Ummi tayi masa maganar kanta abin zai koma haka nan tana zamanta lafiya bazata jawowa kanta ba dan haka taja bakinta ta tsuke sai Seeyamah kawai data faɗawa ita Seeyamahn ma sai abin ya batada dariya ta hau yin abarta aikuwa Neehlah ta shaƙa kamar zata fashe ta haɗe rai da ƙyar Seeyamah ta shawo kanta ta haƙura daga nan kuma ta shiga bata labarin Jawaheer wadda suke tsananin kama da ita wadda a farkon ganinta ma tayi zaton Jawaheer ɗin ce sam Seeyamah bata ɗauka wai kamannin da Neehlahn take faɗa tanayi da waccan ba wata kama ce ta azo a gani ba bare har tayi wani tunani cikin ranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button