EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Har akayi parking a cikin harabar k’aton companyn wanda yayi mugun had’uwa yaji glasses tako ina ko cikinshi ba’a gani bai bud’e ido ba saida aka bud’e k’ofar motar sannan ya bud’e idonshi da suka d’anyi ja k’afafunshi yafara zurowa kafin gangar jikinshi ta biyo baya saida ya daidaita tsayuwarshi sannan ya shiga takawa cikin sauri da kazar kazar irin na mai wadatacciyar lafiya da ubangiji ya hore masa ita sauran suka rufa masa baya.
Tunda ya shiga cikin companyn ma’aikata keta faman mik’o gaisuwa da hannu kawai yake amsawa batare dayace komi ba wanda sun riga da sun saba da yanayin amsa gaisuwar tashi dan haka ba wanda ya damu suka cigaba da ayyukan gabansu.

Maryam Ibraheem Aleeyu
(Ummee)

Mrs Salees Mu’az ????

EL–HABEEB????

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

©️Oum Hanan.

No 2.

Daga inda zai hau lifter ta kaishi 2nd floor inda office d’inshi yake suka rabu dasu bayan sun bashi briefcase d’inshi.
K’aton office ne mai girman gaske wanda aka k’awatashi da duk wasu nau’ikan kayan k’awa da akeyin ado dasu a office k’amshi kawai yake zubawa da k’yalli tako ina saboda gyaran dayasha, wani d’an k’aramin katako ne wanda shima akayi masa wani irin fenti mai kyau aka k’awatashi da tambarin sunanshi ajiki wato
HABEEB IBRAHEEM AHMAD GASHUA daga k’asan sunan nashi aka rubuta matsayin shi a kamfanin wato GENERAL MANAGER.
Had’add’iyar office chair d’inshi wadda take har yanzu a ledarta kamar yaune aka ajiyeta ya nufa ya zauna bayan yayi bismillah wanda ya zame masa k’aidah kullum sai yayi kafin ya zauna k’asa ya d’anyi da kanshi ya dafe goshinshi da hannu d’aya d’ayan kuma ya shiga d’an bubbuga table d’in da pen d’in daya d’auka bayan zamanshi kujerar ta shiga jujjuyawa dashi tarin ayyuka ne a gabanshi saboda shirye shiryen bud’e wani sabon company da babban kamfanin nasu zaiyi na sarrafa fata shiyasa a y’an kwanakin bashida tsugun koyaushe yana busy hakan nema ya k’ara rage masa tunanin yarinyar shi ta mafarki sai yau kuma da abin yadawo sabo fil.
Knocking akayi daga bakin k’ofar
“Yes coming”. yace a hankali tamkar mai ciwon baki cikin daddad’an sound d’inshi da ubangiji ya azurta shi da ita batare daya bud’e idonshi ba koya daina jujjuyawa kan kujerar ba, wani kyakkyawan saurayi ne dogo ya matse cikin suit light blue da tarin files files a hannunshi ya shiga office d’in
“Mazajeeeee”. wannan saurayin ya fad’a yana zube tulin file’s d’in bisa table tareda jan kujera ya zauna fuskarshi d’auke da fara’a, cak ya tsaya da juyawar dayake yaja siririn tsaki tareda bud’e idanunshi ya sakarwa wannan saurayin harara a hankali kamar mai tsoron yin magana yace
“Matsalata dakai kenan hauka MJ ya zaka shigomin office ba sallama saikace ba musulmi ba”.
“Oh shiiit wllhy na sha’afa ne”. Mujaheed yace yana d’an dukan goshinshi, idanunshi ya k’ara mayarwa ya rufe batare dayace komi ba murmushi MJ yayi yana kama kunnuwanshi da duka hannayenshi yace
“Afwan abokina kaina bisa wuya salamu alaikum”. zamanshi ya gyara yana amsa sallamar ya mik’awa MJ hannu kamar yadda shima ya mik’o masa alamun suyi musabaha, takardun MJ ya janyo gabanshi da nufin fara yimasa bayani saiyaga yayi relaxing kan kujerar ya d’aga kanshi sama yana kallon roofing office d’in wanda ya wadatu da fitilu masu kyau da tsari, ido kawai MJ ya k’ura masa yana nazarinshi alamu sun nuna abokin nashi kuma d’an uwanshi yana cikin damuwa zamanshi ya k’ara gyarawa yace
“Hey Mr Gashua what’s wrong with u? uhmm akwai matsala ne?”.
“Nothing”. Habeeb Gashua yabashi amsa a yadda yake batare daya d’ago kaiba, kai MJ ya girgiza yana fad’in
“No is possible kanada damuwa Gashua fad’amin menene?”.
“Nace babu komai MJ please ka k’yaleni haka mana”. Wani d’an murmushi MJ yayi alamun bai yarda da maganar daya fad’a ba yace
“Nikuma nace akwai wani abu ba yau nafara ganinka ba Gashua na sanka farin sani duk da dai dama kullum cikin k’unci da takurawa kanka kake amma tarayyarmu dakai da dad’ewar da mukayi da juna yasa a hakan nake iya gane farin cikinka da akasin hakan please tell me what’s problem…….A fusace Habeeb ya d’ago kanshi har yana d’an dukan table d’in gabanshi yace
“Nace maka ba komai ba komai har sau nawa kakeso in maimaita maka ne kurma ne kai ko makaho? zaka dameni ko maye ne kai ban saniba?”. Dariya ma yaba MJ ya d’an dara tare da fad’in
“Maye ne mana amma ban fara cin mutane ba wai kodai duk rashin mace a kusa dakai ne yake kawo hakan?”.
Harara ya dalla masa yaja wani dogon tsaki ya janyo takardun da MJ yazo dasu yana fad’in
“Mahaukaci kawai”. Dariya MJ ya k’yalk’yale da ita hakan ya k’ara fusata Habeeb a hasale yace
“Zaka tsaya kayi min bayanin abinda ya kawoka kokuma dariyar zaka tsaya yi?”. Gimtse dariyar yayi ya tattara nutsuwarshi suka shiga yin abinda ya baroshi daga nashi office d’in. Sun d’an d’auki lokaci a tare sannan MJ ya tashi ya tattara takardun zai koma dasu office d’inshi tsayawa yayi ya kalli Habeeb zai k’ara yimasa wani iya shegen yaga yaci serious ya tamke fuskar nan tam yaci d’aci tamkar wanda bai tab’a yin dariya ba murmushi kawai MJ yayi ya fice daga office d’in batare dayace komi ba kuma bawai dan murtukewar da Habeeb d’in yayi ba sai dan tarin ayyukan dake a gabanshi wanda yakeso ya kammala a yau idan ya tsaya kuma zai b’ata lokacin shi anan.
Numfashi ya sauke tareda lumshe ido bayan fitar MJ yanajin tamkar ya kirashi ya fad’a masa damuwarshi ko zaiji sanyi a zuciyarshi idan ya fitar da abinda ke cikin ranshi bayaso lamarin nan ya shafi aikinshi gashi kuma abin ya fara worsted dannewar dayake yi ada tana neman gagara a yanzu.
Tsayin mintuna kusan ashirin ya d’auka a haka daga bisani ya tashi ya nufi inda coffee machine yake ya zuba a mug yadawo tsakiyar office d’in inda aka k’awatashi da leather chair milk color kalar fentin office d’in da glass table a tsakiyarsu, bisa 2sitter ya zube ya shiga shan coffee’n duk kuwa da irin zafin dayake dashi haka ya dinga sha yana lumshe ido.
A tak’aice dai a wannan yinin ranar ba wani abin kirki daya tsinana a office d’in har lokacin tashi yayi ya tafi gida.

Flashback.
GASHUA’S FAMILY.
Tun asalin ahalin masu arzik’i ne wanda suka gaje shi tun iyaye da kakanni tun lokacin ma arzik’in na noma da kiwo ne da sauran nau’ikan abubuwa da mutanen da suka dogara dashi ta hanyar cin abincinsu.
Malam Ahmad da inna Karime sune iyayen Ibraheem wanda shiya kasance d’a na uku a gurin iyayenshi akwai maza biyu kafin shi Sulaiman da Adam saikuma mata hud’u dake binshi dukansu dai su bakwai ALLAH ya azurta Malam Ahmad dasu sun tsaya tsayin daka wajen ganin sun basu cikakkiyar kulawa tarbiyya ilmin addini dana zamani sannan mazan duk wanda ya taso zai nuna masa kasuwanci dan haka suka taso masu neman na kansu ga kuma ilmin suna kan nema. Adam da Sulaiman tare sukayi aure lokaci d’aya dan dama tsiransu a haihuwa bawani mai yawa bane, Ibraheem kuwa saidaya dad’e sosai baiyi aure ba yanata bawa biro da takarda hakk’insu da neman kud’i har Malam Ahmad ya gaji dasa masa ido ya magantu ganin bashida alamar yi ko maganar ma bayayi dama kuma shi kad’ai ya rage a gidan sauran k’annen nashi mata duk sunyi aure, wata tafiya da zaiyi Dubai kan harkokin kasuwancin Malam Ahmad yace yana dawowa koya nemi yarinyar dazai aura kokuma shi ya nema masa cikin dangi da abokan arzik’i yace to insha ALLAH yana dawowa zai duba matar aure ashe matar auren ce ke kiranshi acan Dubai d’in dan yana zuwa kwananshi biyu ya had’u da wata yarinya balarabiya mai suna AFEEFAH mazauna k’asar Dubai d’in ALLAH ya d’ora masa masifar sonta lokaci d’aya yasha matuk’ar wahala kafin ma yasamu ganinta dan irin gidan nan ne masu mugun tsaro wancan ganin nata ma dayayi har yaji yana sonta sa’a yaci da kuma ubangiji daya rubuta itace matarshi kuma uwar y’ay’anshi.
Gani d’aya tayi masa itama taji ya kwanta mata sosai cikin ranta duk ya fiye mata samarin larabawan nan dake kai mata hari kasancewar ta kyakkyawar gaske dama ance SO GAMON JINI.
Ta guri d’aya suka samu mishkila a soyayyar tasu wato iyayen Afeefah musamman mahaifinta Habeeb Al-Hussain a ganinsu idan suka bari ya aureta zai tafi da ita k’asarshi ya rabasu da ita gashi dama yara biyu kawai ALLAH ya basu daga ita sai k’aninta Muhseen.
Da k’yar da k’yar aka samu suka amince ya aureta amma sun kafa mashi sharad’in saidai yadawo Dubai d’in da zama gaba d’aya dan bazasu iya nisa da yarinyar su ba kai tsaye ya amince batare da wani dogon tunani ba saboda soyayya data rufe masa ido a lokacin burinshi kawai yaga ya mallaketa a matsayin matarshi, ALLAH ALLAH ya dinga yi ya kammala abinda ya kaishi yabaro k’asar yaje yasamu iyayenshi da maganar yana kammalawa kuwa ko kwana d’aya bai k’ara yi a k’asar ba ya dira 9ja cikeda zumud’in zaijewa da iyayenshi labari mai dad’i na samun matar aure.
Bayan dawowar shi ya sanar dasu abinda ke tafe dashi yasamu matar aure balarabiya, Malam Ahmad bai wani ja da tsayi ba ya amince tareda sawa lamarin albarka amma koda yaji maganar Ibraheem ta k’arshe ta saidai yakoma can da zama gaba d’aya anan fa Malam Ahmad ya tubure yace sam bazai yiwuba bai amince ba idan har zai aureta to kuwa saidai su dawo Nigeria su zauna anan bawata k’asa da zaibi wata y’a mace hankalin Ibraheem ya tashi sosai ga waya da Afeefah ke masa akai akai tana k’ara jaddada masa irin son datake masa taji shiru kuma har yanzu bawani labari dan ALLAH karya gujeta ya taimaka yadawo gareta, hakan ba k’aramin k’ara d’aga hankalin Ibraheem yayi ba ya cigaba da bin Malam Ahmad da magiya da rok’on ya k’yaleshi har mutanen da Malam Ahmad d’in yake ganin mutuncinsu duk ya had’ashi dasu amma fur Malam Ahmad yak’i amincewa k’arshe dai da Ibraheem yaga haka saiya yanke shawarar tafiya batare da yardar mahaifin nashi ba dan haka ya tattara duk wasu muhimman abubuwan shi na harkar kasuwancin dayake yayi hayar wasu mutane daga nan suka tafi Dubai nema masa auren Afeefah.
Ba b’ata lokaci kuwa akayi komai aka gama yayi k’ok’arin yin duk wasu al’adunsu wanda saida jarinshi ya girgiza saboda yadda tsarin neman auren nasu yake akwai kashe kud’i amma dayake SO ya rufe masa ido yasa duk baiji k’yashin yin komaiba kuma ko d’ar baiyiba wajen yinsu saboda ALLAH yayi masa lud’ufi cikin sana’ar shi arzik’inshi kuma a lokacin yafara hab’aka sosai kuma a yadda yakejin zuciyarshi koda bashida komai ma zaisan duk hanyar dazai bi yasamu abinda zai mallaki Afeefah dashi.
Daga can kuma gida Nigeria Malam Ahmad da sauran ahalin gidan suna cikin damuwa da rashin jin dad’in abinda Ibraheem yayi Yaya Sulaiman da Yaya Adam sunso binshi Malam Ahmad ya hanasu yace su k’yaleshi kawai a yanzu koda sunje bazai sauraresu ba saboda giyar soyayya na d’ibanshi kuma bazai yimasa baki ba koya furta wata magana marar dad’i a kanshi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button