EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Afwan da kad’an ????.

Mrs Salees Mu’az ????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 16.

 Aleeyu yana kan hanyar shi ta komawa kiran Habeeb ya shigo wayar shi bayan yayi picking yace masa yasamu boutique ya siya mata kayan sawa. Aiki ja wato har kayan sawa ma za'a siya mata kenan ba ranar sakinta? Aleeyu ya fad'a cikin ranshi yana yin reverse yakoma baya inda ya d'an gota wani babban boutique clothing store yayi parking ya shiga ya fara jidar mata kaya duk dogayen riguna ne ya d'ibar mata da skirt and blouse wad'anda basa matse jiki yaje ya biya kud'in ya shiga mota ya k'ara komawa baya inda gidan yake dan kai mata kayan (Aiki ya sameka Aleeyu Lol).

Sosai hankalin Aleeyu ya tashi lokacin daya isa yaga halin da Seeyamah take ciki, har lokacin tana kwance akan dardumar tana rawar sanyi bata ma san da shigarshi d’akin ba, ba shiri ya ciro wayarshi a aljihu yayi dialing number Habeeb.
Lokacin suna zaune a office d’inshi shida Mujaheed yana gwada masa tsarin wasu gine gine na companies a cikin labtop d’inshi yana zab’ar irin design d’in dayake so kasancewar suna shirin fara gina wani company daya shafi necklace, earrings, bangles and rings kuma zasu dinga fitar da design wa sauran kamfanunuwan da suke yin harkar.
Har wayar ta katse baiyi picking ba wani kiran ya k’ara shigowa, k’aramin tsaki yaja dan duk hankalinshi ya tafi ga gine ginen yanaso ya tantance wanda zaifi k’ayatarwa idan aka gina, hannu yakai ya d’auko wayar dake ajiye bisa table d’in kusa da tashi system d’in ya duba mai kiran yaga Aleeyu ne, picked up yayi yayi yakai kunnenshi batare dayace komi ba jin an d’aga yasa Aleeyu yace
“Yallab’ai yarinyar nan fa batada lafiya nazo na sameta kwance tana ta rawar d’ari da alamu tana jin jiki gaskiya”.
Haka nan yaji gabanshi ya d’an fad’i ya dake tareda fad’in
“Tun yaushe?”.
“Yanzu dai dana dawo kawo mata kayan dakace a siyo mata na sameta a haka”. Aleeyu ya amsa masa.
So yake ya cewa Aleeyun ya samu Dr ya dubata ayi mata duk abinda ya dace amma saiyaji ya kasa fad’ar hakan yaji yanaso ya ganta yaga halin datake ciki dan haka ya tsinci kanshi da fad’in
“Okay I’m coming”.
Yana sauke wayar daga kunnenshi yaga Mujaheed ya k’ura masa ido yana kallonshi, yasha mur sosai yana bankawa Mujaheed d’in harara yace
“Kallon na meye?”.
Tsaki Mujaheed yaja yace
“Uban me zan kalla a jikinka kai ba mace ba?”.
Gira ya d’age yace
“Shiyasa ai naga ka tsura min ido saikace wani maye”.
“Mayu dai ba maye ba”. Mujaheed yace yana hararar shi, bai k’ara magana ba sai mik’ewa tsaye dayayi ya d’auki wayoyinshi yasa d’aya a aljihun wandonshi d’ayar kuma ya rike a hannunshi yana k’ok’arin ture kujerar dayake kai baya.
“Ban gane bafa wai ina zakaje ne haka?”.
“Inda ake zuwa”. amsar daya bashi kenan yana k’arasawa wajen shelf dan ajiye wasu files daya d’auka kan table d’in.
“Kutt amma ka rainamin hankali ma wallahi ina zaman zamana a office ina aikina ka tasoni kace lallai lallai inzo in nuna maka tsarin gine ginen zaka zab’a shine kuma zaka tashi lokaci d’aya kace fita zakayi bak’in halin kama baisa kayi budurwa ba bare inyi tunanin itace tayi maka wannan kiran urgently haka”.
Tsaki kawai Habeeb yayi, Mujaheed yace
“To yanzu maganar da muke fa?”.
“Please MJ ka k’yaleni haka mana banason hayaniya by 8pm ka sameni a gida mu k’arasa okay?”.
“Ai ba bawa ka aje ba da zan bika har gida”. cewar Mujaheed yana rufe system d’in gabanshi, k’ofar fita Habeeb ya nufa yana fad’in
“Ok check your account shi zaiyi maka bayani”.
Da sauri Mujaheed ya mik’e yana fad’in
“Ah haba Dude kar muyi haka dakai mana ka rik’emin salary ai akwai matsala mugu duk wani salon mugunta ka sanshi, wai gidan uwar wa zakaje ne?”.
Bai tanka masa ba ya fice yana cewa idan ya gama tsayuwar ya rufo masa office d’in.
“Mtwss ALLAH ya shirya ka mutum saikace aljani”. yayi maganar yana d’aukar system d’in ya fita ya rufe office d’in lokacin har Habeeb ya shiga lifter, shikuma ta elevator yabi zuwa 2nd floor inda nashi office d’in yake.

Wani Dr'n daban yasamu ba Dr Huzaifah ba tunda shi na gida ne bayaso kuma kowa yasani har zuwa lokacin dazai sallame ta.

Aleeyu na zaune kan sofa Habeeb da Dr Ameer suka shiga bedroom d’in, har lokacin tana kwance a k’asan saidai ta daina rawar sanyin da alamu tasamu barci ne.
Bai zauna a bedroom d’in ba saiya koma falo ya zauna bayan ya k’ara jaddadawa Dr Ameer ya tabbatar yayi mata duk abinda ya dace.
Yana nan zaune a falon yana aikin danne danne a waya Aleeyu ya fito daga bedroom d’in bai d’aga kai ya kalleshi ba ya cigaba da abinda yake, gefenshi Aleeyu ya tsaya ya d’an rissina yace
“Yallab’ai sai kazo fa daga kusa tun d’azu Dr yakeso yayi mata allura tak’i yarda shine yace a kirawo ka”.
Bai tankawa Aleeyun ba haka kuma bai daina latsa wayar ba ganin haka Aleeyu yakoma bedroom d’in yasan bazaiyi maganar ba.
Sai bayan shud’ewar wasu y’an mintuna sannan ya tashi ya nufi bedroom d’in bayan ya k’ara tamke fuskarshi yadda bazata kawo masa wargi ba.
Sab’anin da datake kwance a k’asa yanzu akan gado ya hangeta a zaune hawaye kawai ke ziraro mata ta mak’ure waje d’aya jikinta sai rawa yake.
“Yawwa Mr Habeeb gara da kazo ai tun fitarka nake fama da ita wallahi taki yarda ayi mata injection”. Dr Ameer ya fad’a bayan shigar Habeeb d’akin.
Tana ganinshi ta k’ara matsawa can jikin fuskar gadon tana k’ara curewa waje d’aya haka ma rawar da jikinta yake ta k’aru saboda ganin shi datayi.
A hankali cikin takunshi na k’asaita da zallar mazantaka ya nufi wajen gadon ya had’e gabas da yamma tamkar baisan wani abu dariya ba ya nutsar da idanunshi cikin nata wanda hakan ya k’ara mata mutuwar jiki.
“An gaya miki wasa mukazo yine anan? allura kawai kinzo kina b’atawa mutane lokaci gyara ayi miki ko in b’ata miki rai yanzun nan”.
Duk da tsoron shi datake bala’in ji hakan bai hanata fara yimasa magiya ba da fad’in ita batason allura a k’yaleta kawai dan ALLAH”.
Idanunshi ya d’an lumshe kad’an yana cije baki ya nemi gefen gadon ya zauna ya kalli Dr Ameer yace
“Yi aikin ka”.
“Dan ALLAH balarabe kayi hak’uri”. tayi maganar cikin kuka tana kallon Habeeb daya d’ora d’aya kan d’aya yana girgizasu, da sauri Aleeyu ya juyar da kanshi yana matse dariyar data taho masa jin sunan da Seeyamah ta kira Boss dashi, shima Dr Ameer d’in sai daya d’an dara kafin ya matsa daf da Seeyamahn ya rank’wafa yana fad’in ta janye hijabin ta nad’e hannun rigar ta.
“Dan ALLAH kayi masa magana balarabe kar yayi min allura banaso wllhy”. ta k’ara fad’a cikin wani kukan, a fusace ya juya ya kalleta yace
“I will slap u idan kika k’ara kirana da wani balarabe”. yayi maganar yana maka mata harara kafin kuma ya juyo gaba d’ayanshi ya fuskance ta ya cigaba da fad’in
“Ta bud’e ayi mata ko ranta ya b’aci yanzun”.
Haka nan dole ta yaye hijab d’in ta shiga tattare dogon hannun doguwar rigar dake jikinta gashi ya kafa mata ido ba yadda za’ayi tayi masa musu tana ji tana kallo Dr Ameer yayi mata allurar, y’ar siririyar k’ara tasaki bayan shigar allurar jikinta kafin ta fashe da wani kukan tareda saka kanta tsakiyar gwiwar ta.
Kallonta kawai yake shi gaba d’aya ma he’s totally speechless ganin yadda take wannan uban kukan daga yin allura (d’an rainin wayo shima fa tsoron allurar yake nasan kun tuna lokacin da akayi masa tashi allurar ???? kula ne kawai basuyi ba amma lokacin da Dr Ameer ya tsira mata sai daya runtse idonshi gam yanajin tamkar shi aka tsirawa Lol).
Drugs Dr Ameer ya rubuta mata ya mik’awa Habeeb paper, daga nan yayi musu sallama bayan Habeeb yayi masa sallama mai kyau danshi kanshi baisan nawa ya damk’o ya bashi ba aikuwa ya fita yana ta faman washe baki da fad’in gobe da safe zai dawo za’a k’ara yimata wata allurar hakan dataji yasa ta k’ara sautin kukan ta, a rayuwar ta ta tsani allura tablet ko guda nawa ne zata iya sha amma allura kam basa shiri, bazata manta ba duk lokacin da batada lafiya indai za’a yimata allura tofa ranar kowa sai yaji kanta dan sai an taru kanta.
Paper ya mik’awa Aleeyu dawasu kud’i daya k’ara d’aukowa, karb’a Aleeyu yayi sannan yayi hanyar fita bedroom d’in duk da baiyi magana ba yasan abinda yake nufi ( jigila ta sameka Aleeyu ????).
Shiru d’akin ya k’ara d’auka sai sautin kukan Seeyamah dake tashi kad’an kad’an wanda yafara sawa Habeeb ciwon kai, k’aramin tsaki yaja a karo kusan na hud’u kenan kafin cikin dakakkiyar murya yace
“Shut up ur mouth”.
Da k’yar ta had’iye kukanta cikin ranta tana k’ara jin tsanar mutumin duk inda azzalumi yake to wannan bawan ALLAHn yakai ya daketa kuma ya hanata kuka ALLAH ba azzalumin bayinsa bane saiyayi mata sakayya akan wannan zaluncin da akayi mata batasan hawa ba batasan sauka ba batasan laifin datayi ba amma ya rabota da y’an uwanta ya kawota wani waje daban bazata gaji dakai kukanta wajen sarki ALLAH ba.
Daga k’arshe ma tashi yayi ya fita daga bedroom d’in, nan kan kujera ya zube yana jiran dawowar Aleeyu ya dafe kanshi da hannayenshi duka biyun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button