EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Afwan da kad’an, na shiga busy ne wayar ma sai in yini ban d’auke ta ba hidima tayi yawa ????.

Mrs Salees Mu’az ????

EL–HABEEB ????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 14.

Gajiya Aleeyu yayi da zaman ya zame ya kwanta kan leather chair d’in dake falon yana lumshe idanunshi, so yake yayi barci amma kukan Seeyamah ya hanashi badan karya rasa aikinshi ba daya d’auki yarinyar nan ya maida ita gidan marayun daya d’auko ta, shi dai ba zaice yallab’ai yayi kidnapping d’in nan saboda kud’i ba to dan me yayi kenan? shine amsar da har yanzu ya kasa samu kuma bashida wanda zai tambaya tunda daga shi sai yallab’ai suka san abinda yake faruwa ba’a kuma buk’atar wani ya shigo ciki.
Da wad’annan tunane tunanen barci yayi nasarar sace shi cikin rashin jin dad’i.

Hankali kwance Habeeb yasha barcinshi, koda ya dawo daga masjeed ma sallahr asubah wani barcin ya k'ara komawa sai k'arfe tara da y'an mintuna sannan ya tashi, bathroom ya shiga yayi wanka, cikin k'ananun kaya ya shirya k'irar kamfanin D&G  black trouser jeans da red shirt mai gajerun hannuwa wanda hakan ya bawa cikakkun fararen damatsen shi damar fitowa, bak'in takalmi yasa k'afa ciki ya d'aura Rolex watch black a tsintsiyar hannunshi sai red p.cap daya zaro inda suke tule a ma'ajiyarsu duk da bawai ya cika mu'amala da ita bane yakan dad'e kafin ya sata (Ba irin d'an gidan Mom sayyeed da Aunt jamila ba Abdallah Madugu wadda ta zame masa kamar ibadah ????).

Gaban makeken mirror d’inshi ya k’arasa wanda ke cikeda uban turaruka masu tsada da asalin kyau, body spray ya fara shafawa sannan yabi jikinshi da kalolin turaruka kusan kala uku masu mugun k’amshi da kama jiki uwa uba kuma sanya nutsuwa da kwanciyar hankali ga duk wanda ya shak’a. Bak’in glass ya d’auka saidai bai sashi a idonshi ba ya mak’alashi a gaban rigar ya fice bayan ya kwashi wayoyinshi.
Kai tsaye side d’in su Ummi ya nufa dan gaisheta yana k’ofar shiga falon kira ya shigo d’aya daga cikin wayoyin nashi, duba mai kiran yayi yaga Mujaheed ne picking yayi yakai kunnenshi cikin amon muryar shi mai dad’in saurara yayi sallama Mujaheed ya amsa yana fad’in
“Mazajeee ya jikin naka?”.
Baiyi magana ba sai daya k’arasa shiga cikin falon ya tsaya gaban makekiyar TVn dake lik’e jikin bango yace
“Alhmdulillah”.
“Masha ALLAH, ALLAH ya k’ara sauk’i zaka shigo kamfani ne yau?”.
“Insha ALLAH, but zanyi wani uzuri kafin in k’araso”.
“Okay no prob, saika shigo d’in”. Mujaheed yace tare da hang up d’in kiran.
Yana sauke wayar daga kunnenshi Ummi ta shigo falon da sallama taci gayunta cikin bak’ar doguwar riga k’irar Dubai abayah wadda gaba d’aya gaban rigar akayi mata kwalliya da k’ananun stones masu mugun k’yalli hakan yasa suke ta faman walwali suna d’aukar ido ta yane kanta da gyalen rigar wanda ya k’ara fito mata da asalinta na cikakkiyar balarabiya, k’amshi kawai take zubawa mai dad’i tayi kyau abinta idan ka ganta bazakace tana da cikakken saurayi kamar Habeeb ba.
Kan kujera ta zauna tana murmushi, ya k’arasa inda take ya tsuguna har k’asa yana gaisheta cikin yaren larabci, cikin sakin fuska ta amsa tana tambayar shi jikinshi ya amsa mata da yaji sauk’i, daga nan dinning area suka nufa sukayi breakfast duk da dai Habeeb sama sama yayi nashi dan hankalin nashi kuma ya koma kan yarinyar gidan marayu wadda baisan sunanta ba, ganin Ummi ne ma yasa har ya tsaya yin break d’in yasan idan yace baya ci fad’a ne zai sha shi kuma ta ritsashi dole saiyaci d’in shiyasa yaci kad’an ya tashi duk da haka saida Ummi tayi masa k’orafin baici dayawa ba sumbata kawai ya sakar mata a kumatun ta ya fice yana fad’in yayi latti ne.
Da kallo ta bishi harya fice daga falon yana k’ok’arin toshe idanunshi da black shade d’in dake mak’ale a gaban rigar shi, girgiza kai kawai tayi tana murmushi kullum da uzurin dazai kawo mata idan yaga tana k’ok’arin tilasta masa yaci abinci dayawa daga yace yana sauri saiyace zai gana dawasu bak’i a ranar ko yace akwai important issues da zaije ya gabatar sai yasan yadda dai ya zille mata ya fita ta rasa irinshi cin abincin ma kamar yana masa wahala ne.
Ganin yasa d’aya daga cikin security’s d’in dake tsaye jikin motar Habeeb ya bud’e masa k’ofar motar, saidai ganin yayi tsaye yasa ya bishi da kallo da alamu yau zasusha fama dashi ganin black shades d’in daya manna. Hannu kawai Habeeb ya tara masa batare dayayi magana ba, kallon rashin fahimta yabi Habeeb dashi da tunanin me zai bashi?.
“Give me my key”. yace k’asa k’asa yana d’an hararar shi ganin saida yasa shi magana batare dayayi niyyar yiba, da sauri ya mik’a masa key d’in.
“Kowa ya tafi bana buk’atar kowa yau”. yace yana k’ok’arin bud’e driver seat ya shiga ya tada motar ya fice daga gidan suka bishi da kallo.
Kai tsaye unguwar lamid’o crescent ya nufa inda gidan yake, unguwar sam ba yawaitar mutane sai motoci da suke d’an yawan wucewa kasancewar safiya ce kowa na tafiya wajen aiki.
Parking yayi a k’ofar gidan bai shiga da motar ba, ya kira Aleeyu yace ya fad’a masa yana waje, nan da nan Aleeyu ya fito ya bud’e masa suka shiga ciki tare Aleeyu na mik’a gaisuwar shi da hannu kawai ya amsa masa ya wuce ciki, suna shiga falon yaja tunga ya tsaya yana kallon Aleeyu da alama so yake ya tambaye shi wani bedroom d’in take amma ya bud’e baki yayi maganar ne aiki Aleeyu ya saba ganin haka daga gareshi dad’ewar da sukayi tare yasa ya fara lak’antar shi.
“Left bedroom”. Aleeyu yace yana kallon Habeeb, baice komai ba ya wuce ya nufi corridor’n dazai sadashi da side d’inshi na hagu inda bedroom d’in yake, kafin yabar cikin falon ya tsaya ganin haka Aleeyu ya k’araso ya tsaya a bayanshi, hannu yasa cikin aljihun jeans d’inshi ya ciro rafar kud’i
y’an five hundred ya cillawa Aleeyu yace
“Kaje kayi breakfast itama ka samo mata abinda zataci”. daga haka yayi gaba Aleeyu kuma ya fita daga falon yaja k’ofar.
Gaba yayi zuwa bedroom d’in, Seeyamah na zaune gefen gado ta k’udundune cikin hijabinta tun bayan sallahr asubah data idar tana zaune a wajen tasha kuka har ta gode ALLAH, idanunta sunyi matuk’ar yin ja sun kumbura saboda kuka da rashin barci dan koda wasa barci bai d’auke ta ba tunda taga bathroom a ciki ta shiga ta d’aura alwalah tazo ta kabbara sallah, kwana tayi tana sallah tana kai kukanta wajen ubangiji subhanahu wa ta’alah ya fitar da ita daga hannun wannan azzalumin daya d’aukota wanda batasan laifin datayi masa ba, to wane laifi ma zatayi masa? su daba fita suke ba kullum suna gida, sai a lokacin nema ta k’ara k’arewa d’akin kallo madaidaicin gado ne royal sai k’aramar drawer saikuma sofa guda d’aya tak kalar gadon su kad’ai ne a d’akin inka d’auke lallausan carpet d’in da aka malale k’asan dashi.
Jin alamun takun tafiya zuwa bedroom d’in datake yasa gabanta yayi muguwar fad’uwa ta runtse idanunta tana kiran sunayen ubangiji tsarkaka saboda batasan da wacce yazo ba yanzun saboda tunda ya kawota ma magana bata had’asu ba.
Tsaye yayi a bakin k’ofar d’akin ya lumshe ido yana sauke numfashi haka nan ya tsinci kanshi da fad’uwar gaba wanda ya rasa dalilin hakan, Ido ya bud’e yasa key d’in bedroom d’in wanda Aleeyu ya bashi yasa ya bud’e ya bud’e k’ofar ya shiga, daga bakin k’ofar ya tsaya yana k’arewa Seeyamah kallo ta cikin glasses d’inshi wadda take a mugun tsorace kallo d’aya zakayi mata ka tabbatar da hakan daga inda yake tsaye yana iya hango rawar da jikinta yake ta takure waje d’aya cikin babban hijabinta mai hannu pink color.
Tsananin tsoro yasa Seeyamah ta kasa d’agowa ta kalli wanda ya shigo d’in tayi nasarar dai shak’o daddad’an k’amshin jikinshi wanda ya baza ko ina tun shigowarshi gidan.
A hankali ya shiga takawa zuwa wajen wani dogon stool na zama wanda yake kusa da sofa, stool d’in ya jawo zuwa gabanta ya ajiye bai zauna ba sai daya kai wayoyinshi kan wannan drawer ya ajiye sannan ya dawo ya zauna, daga zaunen dayake ya cusa duka hannayenshi a aljihun wandonshi yana kallonta da yadda jikinta ke shaking ta cikin glass d’inshi.
Baice komaiba haka itama bata d’ago kai ta kalleshi ba sai had’add’un takalman shi datake kallo ta k’asan idanunta da suke zubar da ruwan hawaye.
Sai daya fesar da iskar daya cika bakinshi da ita ya sauke k’aramin numfashi sannan ya rank’wafa daf da ita ta yadda har yakejin hucin numfashin ta itama take jin nashi wanda ke had’e da wani sihirtaccen k’amshi so take ta d’ago kai taga waye shi d’in amma ta kasa ganinshi take duk yabi ya cika wajen.
“Look at me”. yace cikin wata irin dakakkiyar murya wadda duk da ba da k’arfi yayi maganar ba amma sai data jita har tsakiyar kanta, bata d’ago ba sai kukanta data cigaba dayi wanda k’asa k’asa ne yanzu kuma yake k’ok’arin fitowa fili. Lumshe ido yayi yana cije lips ganin tak’i yin abinda yace mata.
“I said look at me”. ya fad’a a tsawace wanda hakan yayi matuk’ar razana Seeyamah ta d’ago kanta ba shiri ta kalleshi hawaye na zarya a kumatun ta, kallonshi kawai take batare data gane ko shi d’in waye ba saboda glass d’in dake manne a idonshi.
“Kin gane ni?”. yace cikin tsananin had’e rai da tsare gida. Kai ta girgiza da sauri alamun a’a, shima kan ya jijjiga yana d’an taune lips lokaci d’aya yasa hannu ya zare glass d’in idonshi idanunsu suka shiga cikin na juna wanda hakan ya haddasawa Seeyamah tsananin fad’uwar gaba fiye data d’azu ganin wanda ke zaune a gabanta hakan yana nufin shine yasa aka kawota nan d’in kenan? why? me tayi masa haka?.
Glass d’in ya mak’ala a gaban rigar shi p.cap d’in kuma ya cire ya jefata kan gado yana fad’in
“Yanzu fa?”.
Kai ta kad’a masa alamun eh ta ganeshi. “Good”. ya fad’a yana kad’a kanshi.
Shiru yayi kamar bazai k’ara magana ba kafin yace
“Zanyi miki wasu y’an tambayoyi, idan kika fad’amin gaskiya zan k’yaleki insa a maidake inda aka d’auko ki sab’anin hakan kuma bazai miki dad’i ba zan d’auki babban mataki a kanki wanda bazai miki dad’i ba kin gane?”.
Kai ta d’aga masa tana rufe bakinta da hijabinta.
Sai daya k’ara tamke fuskarshi tamau yaci d’aci sosai sannan ya k’ara sunkuyawa daf da ita yace
“Kinsan waye ni?”. A mugun tsorace take hakan yasa batasan lokacin data d’aga masa kai ba alamun ta sani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button