EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Mrs Salees Mu’az ????

EL–HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 15.

Da mamaki sosai shimfid’e a fuskarshi yake kallonta, koda yake ba abin mamaki bane dan tace ta sanshi dan da ace bata sanshi ba bazata dinga bibiyar sa duk inda yaje ba da batayi masa wasa da hankali ba.
Seeyamah kam sai bayan data gyad’a masa kai sannan ta gano irin katob’arar datayi na cewa ta sanshi harga ALLAH tsabar kwarjini da cikar haibar shi ne da yadda yayi mugun cika mata ido dad’in dad’awa kuma da bala’in tsoron shi daya mamayeta lokaci d’aya shine ya haddasa mata hakan gashi ta janyowa kanta.
Shiru d’akin ya d’auka sai sautin kukan Seeyamah dake fita k’asa k’asa cikin fad’uwar gaba.
Knocking door akayi, da k’yar Habeeb ya bud’e baki yace
“Yes coming”.
Bud’e k’ofar akayi Aleeyu ya shiga hannunshi rik’e da wata leda mai tambarin wani restaurant sai daya rissina sannan ya mik’a masa ledar had’i da car key d’in hannunshi, key d’in kawai ya d’auka yayi masa alamu da ido ya ajiye ledar a k’asa, ajiyewar yayi kamar yadda ya umarce shi sannan ya fice tareda jan k’ofar. Har yanzu bai daina mamakin abinda yasa Boss d’in nasu ya d’auko yarinyar ba especially data kasance marainiya idan ba’a tausaya mata ba ai ba’a cutar da ita ba.
“Who I’m?”.
Taji sautin muryar shi a dake wanda yasa hantar cikinta kad’awa, shiru batayi magana ba to kota bud’e baki batasan me zatace masa ba. bata sanshi ba, bata tab’a ganin ko mai kama dashi ba, abu d’aya tasani a kanshi yana yawan taimakawa gidan marayun su koda yaushe akance musu akwai wani bawan ALLAH dayake taimaka musu bayan haka batasan komai a kanshi ba.
Iskar daya cika bakinshi da ita ya fesar ranshi yana k’ara b’aci da rainin hankalin da yarinyar take masa bayaso ya fito mata a asalin Habeeb Gashua d’inshi shiyasa yake d’an bida ita a hankali kafin ya fito mata a true color d’inshi. (Ka d’auki abin da zafi Habeeb ????).
“Who I’m?”. yace yana lumshe ido da alamun b’acin rai cikin muryar tashi wanda yasa tsinkewar gabanta ya k’ara tsananta.
“I said waye ni?”. ya fad’a cikin wata hargitsattsiyar murya wadda saida d’akin ya amsa tareda tashi a fusace yayi ball da stoll d’in dayake zaune, a razane tayi baya tana k’arawa kukanta volume lokaci d’aya tana rufe bakinta da hijabinta jikinta sai rawa yake tamkar mai jin sanyi.
Hannu yakai kan sumarshi ya shiga yamutsa ta idanunshi a lumshe ya rik’e k’ugunshi da hannu d’aya yana sauke numfashi.
Takowa yayi har gabanta yaja trouser d’inshi sama sannan ya tsuguna daf da ita har numfashin su na had’uwa waje d’aya.
“I’m asking u”. yace cikin cool voice kamar bashi ya gama hayagaga ba yanzu idanunshi a kanta. Yawun tsoro ta had’iya kafin cikin kuka da rarraba maganar tace
“Bal…..ba…….balarabe ne kai, ALLAH shi kad’ai nasani a kanka sai taimakon da kake yiwa gidan marayun mu”.
Juyar da kai yayi yana lumshe ido gamida cije lips d’inshi, amma yarinyar nan ta mugun raina masa hankali duk wannan tada jijiyar wuyan dayake saboda yanaso yaji actually abinda yasa take canza kamanni take kuma binshi duk inda tasan zaije shine zata bud’e baki tace wai balarabe ne?.
Juyowa yayi yana jan tsaki yace
“Hakan yana nufin zaki cigaba da zama a nan gidan kenan har zuwa lokacin da zaki gaji ki bayyana min gaskiya understand?”.
“Dan ALLAH kayi hak’uri ka maidani inda ka d’aukoni wllhy bansan komai a kanka ba daya wuce wannan please help me”.
Idanunta ya k’urawa nashi hazal eyes d’in yanason gano gaskiyar abinda ta fad’a, itama kallon nashi take da idanunta da sukayi jawur saboda kukan datasha ko iya wannan hawayen data zubar sai ALLAH yayi mata sakayya akansu.
Kai kawai ya girgiza yana datse bakinshi kamar zaice wani abu saikuma ya fasa ya janyo ledar da Aleeyu ya kawo ya bud’e ya tura mata gabanta.
“Eat”. ya furta hakan kamar mai ciwon baki, kai ta girgiza masa wasu hawayen na gangarowa kumatun ta, fuskar sa ya k’ara tamkewa sosai yace
“Bana gane body language open ur mouth”.
Cikin rawar murya tace
“I’m full”.
Wani mugun kallo ya watsa mata hakan yasa ba shiri ta janyo ledar gabanta ta bud’e takeaway d’in dake sama sakwara ce da miyar ganye da akayi mixing da egusi taji naman rago sai k’amshin spices take. Yadda ya tasata a gaba ne yasa ta fara ci a hankali, kallon yadda take gutsurar sakwarar yake tamkar jariri za’a bawa saboda k’ank’antar ta, bai daiyi magana ba ya tashi tsaye ya isa inda ya ajiye wayoyinshi ya d’auki d’aya ya fara danne danne a ciki.
Kad’an ta yayyafita ta ture gefe, tana shirin tashi taje ta wanke hannunta yadawo wajen saita fasa tashin tayi k’asa da kanta cikin fad’uwar gaba, hannu yasa ya d’auke takeaway d’in da sakwarar ke ciki yana kallon yadda ta fiffincine ta ya d’auko d’ayan dake k’asa ya bud’e ya tura mata gabanta, abinda ke ciki tabi da kallo potatoes with eggs sai miyar hanta a gefe. So take tayi masa musu amma ta kasa saboda yadda yabi ya tamke fuskar ba alamun rahma samanta dole tasa hannu ta fara ci duk da kawai dai turawa take batare da tanajin dad’in shiba sam bakinta ba wani d’and’ano, shima d’in kamar wancan kad’an taci ta tureshi cikin ranta tana addu’ar ALLAH yasa kar yace saita k’ara ci saikuma aka ci sa’a bai tanka ba, toilet taje ta wanke hannunta a sink ta fito bata sameshi a d’akin ba harya fice, gefen gado ta samu ta zauna ta matse jikinta cikin hijabinta wani kukan nason k’wace mata.
Tare da Aleeyu suka tafi kamfanin bayan ya tabbatar an kulle ko ina ta yadda ba zata samu hanyar fita ba.

____
A safiyar ranar orphanage house suka wayi gari da tashin hankalin b’atan Seeyamah lungu da sak’o na gidan ba inda ba’a duba ba, ba ita ba alamunta ba k’aramin tashin hankali jama’ar gidan suka shiga ba, manya da yara musamman k’awayenta da suka shak’u sosai Ikram da Aminah sai kuka suke sauran na kwantar musu da hankali duk da suma d’in dai hankalin nasu a tashe yake. Abin ya mugun d’aure musu kai, ganin suna k’ara b’ata lokaci yasa mutum biyu suka wakilci sauran sukaje suka kai report police station da hoton ta, anan D.P.O d’in ya tabbatar musu da insha ALLAH zasuyi iya bakin k’ok’arinsu wajen ganin sun nemota.
Da rana ma waya Habeeb yayiwa Aleeyu yace yayi launch yakai mata, nan da nan kuwa ya cika umarnin shi yayi takeaway na fried rice with chicken da lemon aya ya had’a da fresh milk ya nufi gidan.

Tun daga falo yake jin shasshek'ar kukanta, wani tausayin ta ya k'ara kamashi wato har yanzu bata daina kukan ba.

Key yasa ya bud’e bedroom d’in ya shiga bakinshi d’auke da sallama, kan darduma ya sameta ta d’aga hannayenta sama tana kuka gamida rok’on ALLAH ya fitar da ita daga wannan wajen.
Lumshe ido yayi cikeda tausayin yarinyar ya k’arasa ya ajiye ledar a kusa da ita, kallonshi tayi cikin kuka tace
“Bawan ALLAH kaji tsoron ALLAH ka maidani inda ka d’aukoni ka duba maraicina da tashin hankalin da zakusa bayin ALLAHn da basuji ba basu ganiba ka taimakeni ka fitar dani daga nan wllhy bansan akan me oganku yake tuhuma ta ba help me please”.
Sosai jikin Aleeyu yayi sanyi wata zuciyar na fad’a masa ya fitar da ita kawai yayin da wata zuciyar take masa kashedi da jan kunne na rasa aikinshi da zaiyi wanda da shine yake taimakawa iyayenshi da basuda k’arfi.
“I’m so sorry”. abinda yace kenan ya juya ya fita dan idan ya tsaya zuciyarshi zata iya karyewa ya aikata abinda bai shirya yinshi ba.
Wani kukan ta k’ara fashewa dashi bayan fitarshi, kanta sai wani irin sarawa yake saboda kuka bata ko dubi inda ya ajiye ledar ba saboda ba damuwar ta bace tasan abinci ne dai kuma ba iya cinshi zatayi ba.
Kafin kace me zazzafan zazzab’i ya rufeta ruf batayi yunk’urin hawa gadon ba nan saman pray mat d’in ta kwanta ta k’udundune cikin hijabinta tana rawar sanyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button