EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Afwan babu yawa ????.
Kwana biyu za’a jini shiru sakamakon biki dazamu fara gobe in ALLAH ya kaimu saikuma bayan biki insha ALLAH.
Nagode.

EL–HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

Alhmdulillah munyi biki lafiya antashi lpy nagode sosai da addu’oen ku dafatan ALLAH yaba ango da amarya zaman lafiya dauwamamme ya kad’e dukkan fitina a cikin aurensu dama sauran wad’anda suka angwance muna musu fatan alkhairi.

No 10.

Kwanaki sun cigaba da tafiya yayin da har yanzu dai bata canza zani ba game da irin mafarkin da Habeeb Gashua yake, kuma har yanzu dai bai k’ara had’uwa da wannan yarinyar ba wadda kullum tunanin ta yake caza masa k’wak’walwar kanshi yasha komawa ShopRite d’in ko ALLAH zaisa ya ganta amma ko mai kama da ita bai tab’a gani ba. Aleeyu yana mamakin abinda yake dawo dasu Mall d’in tunda tare suke zuwa kuma basa shiga saidai yasashi yayi parking a waje yana kallon masu shige da fice duk da dai bai fad’a masa ba yasan wani abun yake nema kuma da alamu abinda ya tab’a gani kwanaki har ya bishi a mota shiyake dawo dashi gurin koma dai meye ALLAH ya kawowa maigidan nashi mafita gaba d’aya ya wani sukurkuce ya hana kanshi sukuni.
Yau kam shi kad’ai ma yadawo Mall d’in bayan sun koma gida daga office ya k’ara yin wanka ya fito duk suka taso danyi masa rakiya kamar yadda suka saba ya dakatar dasu har Aleeyun ma dasuke fita tare yau dakatar dashi yayi yace baya buk’atar rakiyar kowa dan haka aka bud’e masa mota ya shiga yabar gidan.
Ya dad’e zaune cikin mota yana raba idanu kan mutane masu shiga da fita amma dai har yanzu zancen d’aya ne babu ita babu alamar ta, idanunshi ya lumshe tareda luma hannunshi cikin sumar kanshi ya shiga yamutsa ta lokaci d’aya yana fesar da wata zazzafar iska daga bakinshi wanda hakan yabawa daddad’an k’amshin mouth freshner d’in dayayi amfani dashi fitowa mai k’amshin banana, da sauri ya bud’e idonshi kamar wanda akace yayi hakan ya k’urawa wata Range Rover fara datayi parking ido haka nan ya tsinci kanshi da son ganin mai fitowa daga cikin motar, koda motar tayi parking ma saida aka dad’e ba’a fito ba hakan kuma baisa ya d’auke idanunshi daga kai ba gabanshi na wata irin fad’uwa daya rasa dalilin yinshi.
Luckily idanunshi suka hasko masa hoton wannan yarinyar ta fito daga motar, yau shigar atamfa ce tayi saidai an ciwa atamfar mutunci wajen d’inki saboda yadda duk ta fito da tsarin halittar jikinta gashi bawani mayafin kirki d’an siriri ne ta rataya shi a kafad’arta, lips d’inshi ya cije cikeda b’acin rai ganin irin banzar shigar datayi, kai tsaye ta wuce cikin Mall d’in cikin wani irin taku na yanga da jan hankali tana k’ara gyara side bag d’inta dake rataye, bayanta yabi da kallo cikin jin haushin yadda take bayyana surar jikinta kowa na kallo jiyake tamkar ya janyota ya koya mata hankali.
Fita yayi shima daga motar yabi bayanta yana d’ora P. Cap d’in daya fito da ita a hannunshi a kanshi, koda ya shiga ciki baiga alamunta ba sam, tsaye yayi ya tura hannayenshi duka a aljihun wandon jeans d’in dake jikinshi yana wuwwurga idanunshi ko zai hangota. Can gurin turaruka ya hangota a tsaye tana dubawa, cikeda karsashi ya nufi wajen yana zuwa kusa da ita yaja birki ya tsaya dan baisan abinda zaice mata ba, jin alamun mutum a kusa da ita yasa ta d’an juyo sam batayi tsammanin ita yake bi ba dan haka tayi gaba tana k’ara duddubawa shima yabi bayanta, ganin dai da gasken ita yake bi yasa ta tsaya ta juyo idanunsu suka had’u waje d’aya yayin da bugun zuciyarshi ya k’aru itakuma nata yafara daga lokacin.
“Malam lafiya kuwa? me kake nema ne a wajena da kake ta bina tun d’azu?”. Cikin tsiwa da rashin kunya tayi maganar tana masa wani irin kallo duk da yadda gabanta yake fad’uwa wanda kallon cikin idanun Habeeb ya haddasa mata.
Sosai ya had’e rai ya k’ara matsawa daf da ita murya ba alamun wasa yace
“Meya fito dake da irin wannan shigar? meye yasa bakya kishin kanki ne?”.
Sakato tayi tana kallonshi cikeda mamakin abinda yace ikon ALLAH sai kallo bata tab’a ganin mutum ba yazo kuma ya tsareta yana tuhumarta to me yake nufi?
“Bakya jine?”. yace a zafafe yana bud’e mata idanu, wata uwar harara ta sakar masa tace
“Kai dallah malam ya isheka haka ya zakazo kana tuhuma ta batare dana san kai d’in wanene ba daga jin maganar ka ma hausa bata isheka ba alamu sun nuna kai ba d’an k’asar nan bane dan haka ka gaggauta komawa k’asar ku ka nemo yarinyar dakake nema”. ta k’are maganar da jan wani mugun tsaki tareda sakar masa harara tayi wucewarta tana cigaba da taunar chewing gum d’in dake bakinta.
Tsaye yayi ya kasa katab’us shi bai juya ya fita ba haka kuma bai bita ba ya shiga duniyar tunani. Gaskiya shima kanshi yafara tunanin wadda yagani a gidan Hajiya daban sannan wannan ma daban idan ya canka daidai su d’in twins tunda gashi nan ba abinda ya rabasu da waccan d’in to amma meyasa yaga waccan cikin shigar kamala da mutunci wannan kuma gani biyun dayayi mata duk ba shigar arzik’i ce a jikinta ba.
“Bambancin ra’ayi”. wani sashen na zuciyarshi ya amsa masa, kai anya kuwa? kodai ita d’in ce take so tayi masa wasa da hankali tayi masa BASAJA shiyasa ta nuna ba ita bace.
“Oh my God”. ya fad’a cikin tsananin damuwa yana lumshe shanyayyun idanunshi da suka canza kala, baisan iya adadin mintunan daya d’auka tsaye a wajen ba yayi zurfi cikin tunani daga bisani ya fito daga cikin Mall d’in koda yakai dubanshi inda motar data ajiyeta take ba komai alamun har sun tafi kenan.
Cikin mutuwar jiki ya k’arasa inda motarshi take ya shiga yabar wajen da gudu ranshi a b’ace.

★★★_★★★
A yau datake ranar alhamis bayan la’asar Habeeb Gashua yakaiwa wani wani orphanage house ziyara wato gidan marayu dake cikin garin Kano, daga shi sai Mujaheed saikuma Aleeyu dake driving d’insu.
Sanye yake cikin shadda light blue d’inkin zamani baisa hula ba sai tarin sumar kanshi datasha gyara take ta zuba k’yalli k’amshi kuwa ba’a maganar shi lafiyayyen k’amshi ne mai sanyi da sanya nutsuwa ke tashi a duk ilahirin jikinshi, ya manna siririn farin glass wanda ya k’ara fito da kyawun shi.
Kasancewar an san da zuwanshi yasa duk wasu masu ruwa da tsaki na gidan marayun sun hallara dayake wannan shine karo na farko dazai fara zuwa da kanshi basu tab’a ganinshi ba sai tarin alkhairan shi dake riskar su ako da yaushe suna matuk’ar jin dad’in yadda yake taimakawa marayu da tallafa musu dan haka sukayi shiri na musamman dan tarbar wannan bawan ALLAHn.
Suna isa aka zagaye motar su, kowa kagani cikin farin ciki da annashuwa fitowar Habeeb daga mota yasa suka k’ara fad’ad’a fara’ar fuskar su suna masa sannu da zuwa shi kanshi bai san lokacin daya d’an saki fuskar tashi ba sab’anin da datake cunkus da ita ya shiga gaggaisawa da mutane.
Gidan marayun suka shiga zazzagayawa kamar yadda ya nema dan ganin abubuwan da suke da buk’ata sun shiga hospital d’insu da school da sauran gurare duk inda yaga sunada buk’atar gyara ya kanyi magana tun a wajen tareda yimusu alk’awarin gyarawa insha ALLAHU sunyi murna k’warai da gaske suka shiga godiya da fatan gamawa da duniya lafiya.
Check ya rubuta musu a lokacin yabasu bayan kuma gyaran da yayi alk’awarin yi musu, lokacin kam kasa magana sukayi suka rasa bakin godiya hak’ik’a wannan bawan ALLAHn ba mai saka masa sai ALLAH, ubangiji yana son a farantawa maraya.
Har bakin motarshi suka rakoshi suna k’ara jaddada godiyarsu da yiwa iyayenshi addu’a wanda yake tsananin jin dad’in hakan yana matuk’ar son yaji ana yiwa iyayenshi addu’a yakan tsinci kanshi cikin farin ciki mara misali, d’aya daga cikin masu kula da marayun ne yace bari a kirawo wasu daga cikin yaran suyi masa godiya sam baiso tsayawa ba suka rok’eshi ya tsaya suma suna son ganinshi. Saida Mujaheed yasa baki sannan ya hak’ura ta tsaya.
Kanshi a k’asa yana danna wayarshi yaji hayaniya da maganganu, duk da haka bai d’ago kaiba har suka k’araso suka fara gaisheshi bai amsa ba sai daya kashe wayar ya maida cikin aljihun gaban rigar shi sannan ya d’ago kai da niyyar amsawa idanunshi suka fad’a cikin na yarinyar nan tana sanye da k’aton hijab har k’asa mai hannu ruwan zuma fuskarta d’auke da mayalwacin murmushi wanda ya k’awata fuskar tata sosai saboda jin dad’in ganin wanda yake tallafa musu a yau d’in shiyasa murmushi ya kasa barin kyakkyawar fuskarta.
Wani irin fad’uwar gaba ne ya ziyarci Habeeb cikeda tsabar kad’uwa yasa hannu ya fige glass d’in idonshi ko shine bai gwada masa daidai ba still dai itace tsaye cikin sauran yaran tana magana da wata a kusa da ita, da wani irin sauri ya shiga ratsawa ta cikin yaran dayake daga can k’arshe take daga yaran har manyan sai aka bishi da kallo cikeda mamaki.
Tsaye yayi a gabanta yana k’ara k’are mata kallo, a kwanakin baya yayi tunanin ko twins ne amma yanzu yafara zargin yarinya d’aya ce take raina masa hankali, tuni idanunshi suka kad’a sukayi jawur, yarinyar kuwa jikinta ne ya d’auki rawa ganin irin mugun kallon dayake jifanta dashi wanda batasan dalilin yi mata shiba baya ta d’an ja kad’an saboda yadda suke daf da juna dashi ya k’ara binta yana fad’in meya kawota gidan marayu kuma? kota fad’a masa kokuma yasa a d’aureta tunda ita munafuka ce, girgiza masa kai kawai take yayin da idanunta suka cika taf da ruwan hawaye so take tayi magana amma ta kasa saboda tsabar tsoron mutumin daya mamayeta lokaci d’aya.
Kowa na wajen idanunshi na kansu an rasa kuma wanda zaije yayi masa magana sai Mujaheed ne ya kutsa kai ya isa inda suke yasa yarinyar mutane a gaba sai wasu zantuka yake mata wanda ta kasa fahimtar su hakama mutanen dake wajen ba wanda yasan ko akan me yake maganar, kafad’arshi ya dafa yace
“Wai Gashua menene haka? me yarinyar nan tayi maka ne koka santa ne?”. Mujaheed yace bayan k’arasawar shi wajen.
Hannu yasa ya cire hannun Mujaheed dake kafad’arshi ya k’ara binta inda ta d’an matsa yace
“K’yaleni da ita kawai MJ,. yarinyar nan munafuka ce tantiriya ce nan da kake ganinta kuma wllhy saita bar gidan nan a yau”. ya k’are maganar yana jifanta da wata muguwar harara, ido Mujaheed ya zaro yace
“Are you mad Mr Gashua?”.
“Eh d’in mahaukaci ne ni Mujaheed”. yace cikin d’aga murya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button