EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

M&S????

EL–HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

Jama’a kubi Habeeb Gashua da addu’a yana neman zaucewa???????? Humayrah taki ta sameki fa sweetyn ki ya sukurkuce ya kamata yaga likitan k’wak’walwa ????.

No 11.

K’ara rik’oshi Mujaheed yayi yana fad’in
“Please Gashua ka tsaya muyi magana ta fahimta mana me kakeyi haka ne?”. fisge jikinshi yayi daga rik’on da Mujaheed yayi masa idanunshi sun kad’a sunyi jawur jijiyoyin kanshi duk sun tashi, ganin abin dai babba ne yasa sauran manyan gurin suka nufo inda suke suna tambayar shi lafiya meyake faruwa rai had’e yake kallonsu yace
“Dole ku kori yarinyar nan idan ba hakaba duk sai nasa an d’aureku”. kowa na wajen mamaki ne ya rufeshi akan me zaice sai an kori yarinya daga ganinta.
Mujaheed daya fara fusata cikin d’aga murya yace
“Wai yaushe ka zama mara imani ne Gashua? idan baka tausaya mata a matsayinta na marainiya ba ai bai kamata ace ka cusguna mata ba”.
“Malam ya isheka haka, kayi shiru da bakinka tunda bakasan abinda yake faruwa ba”. Sosai yarinyar take kuka duk gaban hijabinta ya jik’e da ruwan hawaye tunanin ta d’aya ta yaya ya santa har yake fad’ar wasu maganganu akanta wanda bata tab’a sanin su ba tafi tsammanin dai wata ce suke kamanni da ita ya d’auka waccan d’in ce.
Duk yadda suka so su nunawa Habeeb yadda al’amarin yake sam ya kasa fahimta ya zage sai bala’i yake wanda wasu dayawa daga cikin mutanen wajen ba fahimtar abinda yake fad’a suke ba sun tsinci kalmar dai dole a koreta ita sukafi ganewa cikin maganganun dayake.
Sarai sun san waye HABEEB IBRAHEEM GASHUA sun kuma san waye mahaifinshi duk da baya raye lallai idan har basuyi abinda ya umarce su suyi ba zasu iya jazawa kansu dan haka suka amsa masa da to zasuyi abinda yace d’in.
Kuka yarinyar take sosai wasu y’anmata kamar ta suna tayata kukan tunani take idan har tabar gidan marayun nan ina zata dosa? wata sani gaba d’aya a duniyar nan banda y’an gidan marayun wad’anda ta bud’i ido ta ganta tare dasu ashe mugu ne mutumin nan basu saniba in har yayi sanadiyyar barinta gidan nan bazata yafe masa ba dan ya d’auki alhakinta bataji ba bata ganiba.
Batayi zato ba taji ya kama hannunta k’iiii da uban sauri ya shiga janta har zuwa bakin gate d’in gidan ya tura ta ya maida gate d’in ya rufe, gaba d’aya ido y’an wajen suka zuba masa an rasa mai yin magana ko ya dakatar dashi dama kuma Mujaheed ne mai k’arfin halin yin hakan shikuma ya tsunduma duniyar tunanin anya kan Habeeb d’in bai kwance ba kuwa? to idan ba kwancewar kai ba ya daga ganin yarinya a gidan marayu sai kora ina tausayi da imanin shi suka tafi da har ya aikata wannan aikin?.
Wata kujera ya samu ya zauna yayi k’asa da kanshi tareda rufe idanunshi gam kanshi na wani irin juyawa tsabar tension dayayi masa yawa ya rasa ta inama zai b’ullowa lamarin da gaske ne yarinyar nan FUSKA UKU gareta sai taje ta gama tantirancin ta a waje sannan ta dawo gidan marayu to meye amfanin zamanta a gidan marayun yana so yasan wacece ita me kuma ya kaita gidan Hajiya?
Wani daga cikin manyan gidan marayun Mujaheed yasamu yayi magana dashi ta fahimta da nuna masa kar su damu insha ALLAHU zata dawo dama a kwanakin nan sun rasa gane kanshi su kwantar da hankalin su, daga nan ya sallamesu suka watse cikeda alhini musamman k’awayen nan nata su biyu da har lokacin kuka suke.
Bayan kowa ya watse Mujaheed da Aleeyu suka k’araso inda Habeeb ke zaune har yanzun bai d’ago kanshi ba, kusa dashi Mujaheed ya zauna yana fad’in
“Lamarin ka yafara bani tsoro Gashua ya daga taimako kuma zaka b’ige da wannan aiki? dan ALLAH ka fad’amin damuwarka ko akwai shawarar da zan iya baka ko zata iya zama mafita a gareka”.
Ci kanka Habeeb baice wa Mujaheed ba bai kuma d’ago ya kalleshi ba, yasan bazai kulashi d’in ba dan haka yace ya tashi to su tafi magreebah takawo kai, nan ma banza yayi masa sai dayaga dama dan kanshi bayan dogon lokacin da suka d’auka a wajen sannan ya d’ago kanshi fuskar nan a cunkushe, a razane Mujaheed yayi baya yana zaro ido saboda yadda yaga idanun Habeeb ya canza yayi wani irin ja na ban mamaki Aleeyu ma dake tsaye saida yaji tsoro, bai kula kowa ba ya tashi ya nufi inda motar tasu take duk saurin da Aleeyu ya dinga yi dan ya bud’e masa motar bai samu dama ba yana zuwa ya bud’e ya shiga Mujaheed da Aleeyu suka shiga Aleeyu ya tada motar suka bar farfajiyar gidan.
Tunda suka tafi babu mai magana Mujaheed yasan ko yayi masa magana ba tankashi zaiyi ba a wannan lokacin dan haka yaja bakinshi ya tsuke cikin ranshi tunanin ta yadda zai dawo da yarinyar yake batare da Habeeb ya sani ba.
Sun d’anyi nisa da gidan marayun can gabansu ya hango yarinyar tsugune a gefen titi ta mak’ure waje d’aya da alamu kuka take, sosai tausayin ta ya kamashi gaskiya Habeeb bai kyauta ba wllhy in haka ne meye amfanin taimakon daya yiwa gidan?
“Yi parking Aleeyu”. Mujaheed yace yana kallonshi, parking d’in yayi kuwa kamar yadda ya umarce shi, juyowa yayi ya kalli Habeeb daya kishingid’a idanunshi a rufe yace
“Dubi yarinyar can Gashua abin tausayi shin baka tausayawa maraicinta ne? kokuma baka gudun ubangiji ya kamaka da hakk’inta? ina rok’on ka Gashua dan ALLAH dan alfarma da martabar annabin mu kayi hak’uri inje in maida yarinyar nan gidan can baka tunanin duk halin data fad’a a yanzu kaine sanadi? please and please Gashua”.
Ido ya k’ara runtsewa sosai tsigar jikinshi na tashi saboda girman abinda Mujaheed ya had’ashi dashi, shi wanene da za’a had’ashi da girman ALLAH da ANNABI ya juya baya? ai saidai idan bashi da damar yin abun, kuma akwai tunanin daya d’arsu a ranshi yanzu bayan barowar su gidan marayun wanda idan yarinyar tana can aikin zaifi zuwa masa da sauk’i fiye da ace bata gidan ( A tunanin ku me zai aikata reader’s??? ).
Kai ya kad’awa Mujaheed alamun amincewa batare da kuma ya bud’e idanunshi ba.
“WOW thank you very much abokina ALLAH ya saka maka, bari inje”. Mujaheed ya fad’a cikin tsananin farin ciki ya fice daga motar cikeda zumud’i dan sam baiyi tunanin Habeeb d’in zai amince da sauri haka ba sanin halinshi da yayi na muguwar kafiya da shegen taurin kan tsiya.
Can d’aya side d’in ya tsallaka inda take, ya k’arasa wajenta bakinshi d’auke da sallama, da sauri ta d’ago kai tana kallonshi kukan datake yasa ko sallamar tashi bata amsa ba ta maida kanta k’asa ta cigaba da kukanta mai tab’a zuciya ga duk mai imani, y’an sakanni ya d’auka yana kallonta kafin ya durk’usa a gabanta cikin taushin murya yace
“Kukan ya isa haka, munyi magana dashi zan maidake”. Cikeda farin ciki ta d’ago kai tana kallonshi tasa hannu tana share hawayen idanunta tana murmushin jin dad’i cikin rawar murya tace
“Nagode”.
“Never mind”. ya amsa mata shima fuskarshi d’auke da murmushi da wani irin tausayin yarinyar.
“What’s ur name?”. ya tambaye ta.
“SEEYAMAH
“WOw nice name, Seeyamah”. yace yana k’ara maimaita sunan, tashi sukayi suka jera yana janta da hira har cikin gidan marayun dayake ba nisa sosai sai daya damk’ata a hannunsu sannan ya fito ya dawo wajen motar ya shiga suka tafi.

I’m so sorry ba yawa afwan hidima ce dayawa ????.
Rashin comments dinku yasa gaba d’aya labarin yafara fita a kaina wllhy daga wannan page din bazan k’ara wani ba gaskiya sai naga yanayin comments dinku bawai rashin aikin yine yasa muke rubutun nan ba naga kamar labarin bai muku ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button