EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Sai bayan sallah idan Allah ya nuna mana da rai da lafiya hop za’aci nama a hankali ????.

Mrs Salees Mu’az ????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION*????
(Home of expert & perfect writer’s)

Alhmdulillah! I’m back ina yiwa kowa fatan alkhairi tareda fatan anyi sallah lafiya ubangiji ya amshi ibadunmu Amin. I’m so sorry na rashin update babban uzuri ne ya rik’eni zamu cigaba da yardar ALLAH sai a dinga hak’uri da yanayin yadda posting zai dinga zuwa harkar mai iyali sai a hankali, duk lokacin dai dana samu time zanyi bakin k’ok’arina wajen yin typing.
Nagode! 1luv my dearest fans jazakumullahu khair.????

No 17.

Yana nan zaune yana faman tufka da warwara a cikin zuciyarshi har zuwa lokacin da Aleeyu ya dawo gidan hannunshi rik’e da wata leda mai tambarin sunan wani pharmacy wanda ledar kawai zaka kalla ya tabbatar maka da babban pharmacy ne.
“Sir ga drugs d’in an siyo”. yaji maganar Aleeyu cikin kanshi wanda ya katse masa tunanin dayake sai sak’e sak’e yake cikin ranshi tausayin yarinyar yanaso ya rinjayesa saidai bazai bari tafaru bazata bar gidan nan ba har saita fad’a masa alak’arshi da ita data sawa rayuwar shi ido kuma take zuwa masa cikin barcinshi.
Kamar bazai d’ago ba dan yafi mintuna biyar bai d’ago kai ya kalli Aleeyun ba wanda yake tsaye yana jiran umarnin ogan nashi, tsaye ya mik’e key d’in motarshi kawai ya karb’a ya wuce yana fad’in
“Kaje ka bata tasha”.
“Ok Sir”. Aleeyu yace yana nufar hanyar bedroom d’in.
“Ka tabbatar taci abinci before tasha maganin”. Habeeb ya fad’a yana ficewa daga falon yaja k’ofar.
Shi yaso ya shiga yabata maganin da kanshi amma saiyaji ya kasa bashida wannan k’warin gwiwar haka nan kukanta ke masa ciwo cikin ranshi kuma yasan tana can tana aikin yinshi dan haka kawai ya zab’i fita daga gidan gaba d’aya.
Ba k’aramin fama Aleeyu yasha da Seeyamah ba kafin yasamu taci abincin tasha maganin dan saidaya ciro wayarshi yace zai kira Habeeb dama yace idan tayi masa gardama ya kirashi sai sannan ta d’an tsakuri abincin tana kuka tasha maganin takoma ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya irin wadda tasha kuka ta k’oshi yaushe zata yarda ya kira mata wannan mutumin bala’in tsoron shi takeji tun daga lokacin dayasa aka d’auko ta ta cireshi daga cikin jerin masu tausayi da imani.
Shima Aleeyun ajiyar zuciyan yasaki tareda girgiza kai sannan ya fita daga bedroom d’in yaja k’ofar.

____
Y’an sanda sun fara bincike kan b’atan yarinyar da gidan marayu suka kai musu report amma har lokacin basu samu abinda sukeso ba saidai sun tsananta bincike da fatan samun nasara.
Wani daga cikin shugabannin gidan marayun ne ya kawo shawarar ya kamata sukai cigiya kafafen sadarwa ko ALLAH zaisa a dace, hakan kuwa akayi sunkai gidajen radio da talabijin nan ma suka bada hotonta a gidajen talabijin d’in da suka kai cigiyar.

Duk yadda Mujaheed ya dinga tambayar Habeeb ina yaje ya fita cikin gaggawa haka yak'i kulashi k'arshe ma zagi ya auna masa yace ya k'yaleshi kar ya dameshi Mujaheed yayi k'wafa ya fita ya rufo k'ofar da k'arfi shima yana zaginshi da kallo kawai ya bishi tsaki yaja yayi baya yayi relaxing sosai kan kujerar idanunshi a lumshe yana jujjuyawa.

Gaba d’aya yinin ranar bai hasala wani abin kirki ba duk da yadda yaso yayi aikin kuwa, kasa hak’uri yayi saidaya kira Aleeyu yaji ya jikin nata ya tabbatar masa da taji sauk’i yanzu ma ya shiga ya dubata sai a lokacin hankalin shi ya d’an kwanta yasamu nutsuwa.
Haka yinin ranar yazo ya wuce bazaice ga wani muhimmin aiki d’aya dayayi a office ba a ranar, da wuri ma yabar kamfanin yatafi gida batare daya nemi Mujaheed ba duk dayaso su k’ark’are aikin dasuka fara d’azu saboda yanaso yayi magana da wad’anda yabawa kwangilar aikin ginin kamfanin da za’a fara dole zai nemi Mujaheed d’in ko zuwa dare ne su k’arasa.
Yaso biyawa ta lamid’o crescent yaga halin da yarinyar take ciki saikuma ya fasa kai tsaye ya wuce gida.

★★★__★★★
Bayan magreebah.
Kwance yake akan doguwar kujera dake falon nashi yana sanye da farin wando 3quater mai aljihuna gaba da bayan wandon sai k’aramar riga ta shan iska ash color, wani sassayan k’amshi ne yake tashi tako ina a jikinshi da kuma falon wanda aka k’ure A.C hakan yasa falon ya d’auki uban sanyi kamar k’ank’ara kuma ba abinda ya dameshi ga kayan jikinshi bawasu na kirki ba. tamfatsetsiyar wayarshi ce a hannunshi yana latse latse ya hard’e k’afafunshi daga kwancen dayake, number Mujaheed ya lalubo ya danna masa kira jinsa shiru har yanzu baizo ba saidai yana kira akace masa line busy alamun waya yake tsaki yayi ya kashe ya k’ara dialing still dai akace masa akan waya yake wani tsakin ya k’ara ja ya yanke kiran yana tunanin ko da uban wa yake waya? Saida aka d’an d’ebi wasu y’an mintuna sannan ya k’ara trying number cikin sa’a ta shiga bata dad’e tana ringing ba Mujaheed yayi picking bakinshi d’auke da sallama ko amsa sallamar baiyiba yace
“Da uwar wa kake waya ne wai tun d’azu?”.
“Ah ban ganeba an fad’a maka kowa ma irinka ne idan akaji kana waya kan business ne bawata y’ar soyayya da nishad’in nan irin na zamani da y’an mata”.
“Mtwss! An fad’a maka kowa ma bashida aikin yi irinka? dallah malam kazo ina jiranka karka b’atamin lokaci”. Bai jira abinda Mujaheed yake fad’a ba yayi hang up yana fad’in
“Useless man kawai wazai b’ata lokacin shi wajen yin wata soyayya salon yara su rainaka ai shi ko soyayyar zaiyi bazaiyi da k’aramar yarinya ba sai wadda ta amsa sunanta na mace ta mallaki hankalin kanta I thought ma sa’ar shi koma wadda ta girmeshi zai aura hankalinshi kwance amma auren k’aramar yarinya ba abinda yake janyowa illah raini da zubar da girma shikuma duk abinda zai zubar masa da girmanshi baya shiri dashi.
Bayan sun gama waya da Mujaheed ya kira Aleeyu ya k’ara jin lafiyar Seeyamah, saidaya k’ara jan kunnenshi kan ya k’ara kula da ita sosai kuma kar yayi saken dazata gudu sannan ya kashe wayar yana tuna kukanta na d’azu da yadda take kiranshi da balarabe sai yanzu abin ya bashi dariya amma dayake ba gwanin yinta bane murmushin gefen baki kawai ya saki yana cije lips d’inshi na k’asa.
Bayan wani d’an lokaci Mujaheed ya iso gidan wajen Ummi ya fara shiga dan su gaisa, suna zaune a k’ayataccen falon nasu wanda ke tashin k’amshin turarukan wuta na asalin larabawa suna kallon tashar Aljazeerah Ummi da Neehlah, yana shiga idanunshi suka sauka kan Neehlah datake zaune kan kujerar dake facing d’in k’ofar falon suka had’a ido dashi wani k’ayataccen murmushi suka sakarwa junansu ya matuk’ar yimata kyau cikin bak’in wandon jeans da farar riga long sleeve da bak’in agogon fata dake d’aure a tsintsiyar hannunshi, kamar yadda shima tayi masa kyau ainun cikin shigarta material ne bak’i da adon golden na fulawoyi a jikinshi riga da siket kasancewar ta fara yasa yayi bala’in haskata ido ya kashe mata tayi saurin sadda kanta k’asa tana murmushi gamida addu’ar ALLAH yasa Ummi bata ganshi ba Mujaheed bashi data ido wlhy, Kai tsaye wajen Ummi ya nufa ya zauna k’asan k’afafunta yana gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar shi mutanen gida ya amsa mata da
“Lafiyar su k’alau sunce a gaisheta”. ya ida maganar yana satar kallon Neehlah wadda itama daidai lokacin ta d’ago kanta ya kasheta da wani irin kallo dayasa duk ta daburce cikin y’ar rawar murya wadda ta had’u da siririyar muryar ta tace
“Yah Mujaheed ina yini”.
“Lafiya k’alau k’anwata ya kike?”. Yace yana murmushi bayan ya d’ago kai yana kallonta.
“Alhmdulillah”. Kawai tace ta tashi tabar falon kafin Ummi ta ramfo su duk da hankalin Ummin ma dai yana kan TV, da idanunshi ya rakata da kallo har ta shige ya daina ganinta ajiyar zuciya ya saki ya mik’e tsaye yayiwa Ummi sallama ya fita.
Yana dosa kai falon Habeeb wani uban sanyi yayi masa maraba sallama yayi ya shiga har lokacin Habeeb na kwance saidai sab’anin d’azu da wayace a hannunshi yanzu wata y’ar madaidaiciyar laptop ce apple daya d’orata kan cinyarshi yana sarrafa ta, ciki ciki ya amsa sallamar Mujaheed batare daya juyo ya kalleshi ba.
Jakar hannunshi ya ajiye wadda shima system d’inshi take ciki ya d’auki remote control na air conditioner d’in ya rageta sosai ya daidaita sanyin yadda baiyi yawa ba kuma baiyi kad’an ba, sai a lokacin Habeeb ya juyo ya kalleshi cikin had’e rai yace
“Malam meye haka wai?”.
“Kamar ya?”. Mujaheed yace yana zama kujerar dake fuskantar wadda Habeeb d’in yake kwance, zaune ya tashi yana b’ata rai yace
“Ya daga zuwanka zaka canzamin tsarin yadda nakeson d’akina ya kasance”.
“Kowa ma mahaukaci ne irinka? in banda hauka taya zaka dinga bankawa kanka sanyi haka ko tsoron pneumonia bakayi saboda tsabar bakada hankali wautar d’an fari na d’awainiya dakai”.
Wata uwar harara Habeeb ya jefawa Mujaheed yace
“Banason iskanci, d’akinka ko nawa, inada right d’in inyi duk abinda nakeso a ciki ba matsalarka bace”.
Baki Mujaheed ya tab’e yana d’age kafad’a yace
“To kabari inbar d’akin idan ma cikin k’ank’ara zaka shiga Gashua k’arewar sanyi kanada damar yin haka amma yanzu kam saidai kayi hak’uri”.
Kai Habeeb ya kad’a yana sakin k’wafa ya daidaita zaman system d’in ya cigaba da dannawa batare daya k’ara kallon sashen da Mujaheed yake ba.
“Naga alamun baka lallab’a lafiyar ka ko?”. yaji Mujaheed ya k’ara fad’a, banza yayi masa bai tanka shiba, baki Mujaheed ya k’ara tab’ewa ya janyo jakar dayazo da ita ya ciro tashi system d’in ya tashi ya koma kusa da Habeeb d’in ya zauna ya d’auke system d’in dake kan cinyar Habeeb ya d’orata kan wani center table na glass daga gefenshi ya juyo yana fad’in
“Malam ka maida hankalinka kan aikin daya kawoni inyi in tafi tsabar jaraba irin taka daren ma bazaka hak’ura ba kana min bak’in cikin huawar da zanyi kayi hak’urin goben shine bazaka iyaba”. Habeeb yanajin Mujaheed yanata faman mita k’ala baice masa ba idan ya biye ta Mujaheed sai sun zama kamar zararru shiyasa wani lokacin yake masa banza yayi yagama.
Dolenshi ya maida hankalinshi kan abinda zasuyi d’in tunda shiya matsawa Mujaheed d’in saiyazo gaba d’ayansu suka maida hankali Mujaheed ya cigaba da nuna masa tataccen speech kawai ke tashi a wajen har zuwa lokacin da suka kammala suka tsaida mgn.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button