EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

No 18.

Rufe system d’in Mujaheed yayi bayan sun kammala ya ajiyeta kusa data Habeeb, zamanshi ya gyara ya d’auki remote d’in TV da tun d’azu takeyi a tashar larabawa ana labarai channels ya shiga canzawa yana fad’in
“Mudai ba larabcin nan mukeji ba bari mukai inda mukafi wayo”.
Habeeb da bayan gama tattaunawar tasu ya d’auki waya ya cigaba da danne danne ya d’ago ya kalli Mujaheed yana b’ata rai yace
“Wai meyake damunka ne MJ akan me zaka canzamin channels?”.
“To kallon kake? tunda na shigo d’akin nan banga ka d’aga kai ka kalli TVn nan ba”.
“Dole saina kalla zanji abinda ake fad’a? ba kunne ne yake jiba”. Habeeb ya fad’a yana antayawa Mujaheed harara. Baki kawai Mujaheed ya tab’e ya cigaba da neman channels d’in dayake so kan N.T.A. ya tsaya daidai lokacin da zasu fara news ya ajiye remote d’in yana fad’in
“Yawwa bari muga abinda duniyar ke ciki”. tsaki kawai Habeeb yayi ya maida kanshi kan wayar dake hannunshi shikuma Mujaheed kacokam ya maida hankalinshi kan TVn, bayan mai gabatarwa ya gabatar da kanshi da kuma kanun labaran sannan aka tsunduma cikin gundarin labaran.
Labari na farko da mai labaran ya fara karantowa shine na b’atan Seeyamah bayan wasu y’an maganganu dayayi hoton Seeyamah ya mamaye fuskar talabijin d’in a matsayinta na wadda ake nema, tana sanye da k’aton hijabi kamar yadda ya saba mai hannu light blue fuskarta d’auke da k’ayataccen murmushi wanda har beauty point d’inta saida suka lotsa wanda take dashi a gefen kumatun ta na dama
“Innalillahi”. Mujaheed ya fad’a cikin razana yana zaro ido ganin yarinyar nan ta gidan marayun da suka tab’a zuwa da Gashua wadda har yace saita bar gidan garkuwa akayi da ita kenan?.
“Gashua kaga wani abin mamaki”. Mujaheed yace cikin fad’uwar gaba yana dafa kafad’ar Habeeb wanda gaba d’aya hankalinshi yake kan wayarshi da alamu wani abu mai muhimmanci yake yi a ciki. A hankali ya d’ago kai idanunshi suka fad’a kan Seeyamah da har zuwa lokacin ba’a d’auke hotonta daga TVn ba, ba zaice gabanshi bai fad’i ba amma dayake namijin duniya ne saiya maze ya shanye fad’uwar gaban nashi ya kalli Mujaheed yana neman k’arin bayani daga wajenshi.
“Wlhy wai b’ata tayi ba’a ganta ba har gidan marayun aka shiga aka d’auketa nasan ka ganeta ko? kai jama’a duniya ina zaki damu ne? marainiyar ALLAH bata jiba bata ganiba anje anyi garkuwa da ita Yaa ALLAH”. ya k’arasa maganar cikin tsananin jimami yana dafe goshinshi sosai labarin b’atan Seeyamahn ya dakeshi saiya tuno lokacin daya tambayeta sunanta ta fad’a masa da irin murna da farin cikin daya hanga daga cikin idanunta lokacin dayace ta tashi ya maida ita gidan marayun yau gashi anje har cikin gidan inda take tunanin nan ne garkuwar ta bango abin jinginar ta an saceta.
Sam Habeeb kasa d’auke idanunshi yayi daga kan allon talabijin d’in idanunshi k’ur akan Seeyamah duk yadda yaso janye idanunshi ya kasa har zuwa lokacin da aka d’auke hoton mai gabatarwar ya cigaba da labaran shi, a hankali yayi k’asa da kanshi ya cigaba da danne dannen dayake a zahiri wanda a bad’ini kawai shige shige yake a cikin wayar batare dayasan ina yake shiga yake fita ba tunanin kacokam ya tafi can wani waje daban.
“Wai bakaji abinda nace bane Gashua ka maida kanka ka cigaba da abinda kake?”. Mujaheed ya fad’a cikin jin haushi yana kallon Habeeb.
“Me kakeso ince MJ? ko zuwa zanyi in nemota da kaina?”.
“Bakaji na fad’i haka ba amma dai at least ko addu’a ce kayi ta ALLAH ya bayyana ta tunda ba’a san a wani irin hannu take ba anya kanada imani kuwa Gashua?”.
Wani banzan kallo Habeeb ya jefi Mujaheed dashi kafin yace
“Ina nake dashi? ai imani sai sheikh Mujaheed”. yayi maganar cikeda gatse.
“Ai naga alama kam inba hakaba ai duk wani musulmi mai imani idan yagani zai tausaya har ma yabita da addu’a”.
Tsaki kawai Habeeb yaja ya zame ya kwanta yana cigaba da duba wayarshi.
“ALLAH ya shiryeka ya canza maka halinka”. Mujaheed ya fad’a shima yana d’auko wayar shi wadda ya ajiye kan center table tun bayan shigowarshi falon, ko kallonshi Habeeb baiyiba bare ya tanka masa.
Yanar gizo Mujaheed ya shiga nan ya fara cin karo da hoton Seeyamah a Facebook da labarin b’atan ta, kai kawai ya girgiza cikeda tausayin yarinyar ko a wani irin hali take ciki yanzu? ALLAHU A’ALAM, ALLAH dai ya tona asirin wad’anda suka d’auketa.
“ALLAH ya bayyanaki cikin k’oshin lafiya Seeyamah”. Ya fad’a a fili cikin alhini, baki Habeeb ya tab’e cikin ranshi yana mamakin irin yadda yaga Mujaheed ya nuna zallar damuwarshi kan b’atan yarinyar da sai yanzu ma yake jin sunanta.
D’aya wayar tashi wadda ke ajiye gefenshi ta fara bada sautin kid’a mai dad’i, kamar bazai d’auka ba saikuma yakai hannu ya d’auka ya duba mai kiran yaga Aleeyu ne batare da shayin komai ba yayi picking ya kara a kunnenshi cikin muryar nan tashi mai cikeda amo da sautin mai dad’in saurara yace
“Ya akayi?”. Sam bai saurari gaisuwar da Aleeyun keyi masa ba, daga b’angaren Aleeyu yace
“Yallab’ai yarinyar nan fa tak’i cin abinci na kad’a na raya amma tak’i kulani kuma dole sai taci abincin sannan tasha maganin ko d’azu da rana ma kad’an ta yafita tace ta k’oshi sai aikin kuka datakeyi tun d’azu”.
K’aramar ajiyar zuciya Habeeb ya saki yana d’an dafe goshinshi da sakin numfashi kamar bazaice komai ba saikuma yace
“Bata wayar”.
Aleeyu dake tsaye akan Seeyamah datake ta kuka tun d’azu ya mik’awa wayar yana fad’in
“Zakuyi magana da yallab’ai”.
Gaba d’aya jikinta rawa ya d’auka saboda tsoro ita sam batayi tunanin kiranshi zaiyi ba sai dataji yafara magana dashi wllhy mugun tsoron mutumin nan take ji, hannu na rawa ta karb’i wayar takai kunnenta saidai ta kasa magana sai shasshek’ar kuka datake k’asa k’asa wanda yasa Habeeb lumshe idanunshi ya k’ara gyara kwanciyar shi kafin cikin cinkushasshiyar murya ya k’ara had’e rai sosai kamar yana gabanta yace
“Ke! kin raina mutane ko?”.
Girgiza kai kawai tayi kamar yana kallonta tana share hawayen idanunta da d’aya hannun, Aleeyu dai yana tsaye yana kallonta.
“Ki kama abinci kici kafin ranki ya b’aci duk ranar da kika bari ya k’ara min complain akan rashin cin abincinki sai ranki ya b’aci banason gardama ki kiyaye”.
“Bakya jine”. yayi maganar a fusace cikin d’an d’aga murya jin tayi masa shiru ya tsani yayi magana ayi biris dashi har saida Mujaheed yabar danna wayar dayake ya kalleshi, cikin dashasshiyar murya ta amsa masa da
“Toh”. Wata tsanar shi na k’ara samun gurbin zama a cikin zuciyarta, k’aramin tsaki yaja ya kashe wayar batare da sun k’ara yin magana da Aleeyu ba wayar ma gaba d’aya saiya kasheta ya cillata gefenshi yana d’agowa suka had’a ido da Mujaheed wanda yake binshi da wani irin kallon tuhuma, basarwa yayi ya d’auke kanshi gefe Mujaheed kasa shiru yayi yace
“Gashua dawa kake waya haka?”.
“Zoka matseni sai in fad’a maka munafuki”. yace yana masa wani irin kallo mai kama da harara.
“Oh my God! nifa ba fad’a na nema ba tambaya ce kawai nayi, ALLAH Gashua kazama masifaffe nidai sanin danayiwa wancan Gashuan ba haka yake ba maganar fatar baki ma bata dameshi ba amma lokaci d’aya ka canza ka zama jarababbe magana kad’an saika hau kan mutum da bala’i why?”.
Banza yayi masa bai tanka shiba, baki Mujaheed ya tab’e ya mik’e tsaye yana fad’in
“Naga alamar idan ban bar gidan nan ba duka zaka kai min”.
“Ai kasan ga mahaukaci ko?”. Habeeb yace yana sakar masa harara gamida cije lips d’inshi, dariya Mujaheed yayi yana zura system d’inshi a jaka ya rataya yana fad’in
“A’a nidai bance ba Mr Habeeb Gashua good night sai mun had’e gobe”. daga haka ya d’auki wayarshi ya nufi k’ofar fita yana cigaba da dariyar shi wadda ta k’ara k’ular da Habeeb sosai ya bishi da kallon takaici yanajin tamkar ya shak’oshi yayi ta dukanshi ganin irin dariyar dayake masa ya maidashi wani shashasha.
Zaune Mujaheed yake a cikin motar shi bayan fitarshi da wace yarinya Gashua yake waya har yake mata bambamin idan bataci abinci ba sai ranta ya b’aci? wacece ita? meye alak’arshi da ita? bayaso ya tabbatar da zargin da zuciyarshi take yimasa akan abokin nashi kuma d’an uwanshi amma dole yasa ido, d’azu kafin yazo office yace yana da uzurin dazaiyi kafin yazo dayazo kuma suna cikin aiki an kirashi a waya yabar komai dayake ya tafi yanzu kuma an kirashi yana magana kan taci abinci duk da baiji maganar wanda suke wayar dashi ba ya tabbatar mace ce duk me hakan yake nufi? ya tuno lokacin da Habeeb d’in yayi ruwa yayi tsaki yace dole sai Seeyamahn tabar gidan marayun datake kodai wani abun ya shirya bayan faruwar lamarin yasan halin abokinshi sarai da kafiyar tsiya da taurin kai koma dai meye zaibi ba’asi da diddigi har saiya gano bakin zaren. Motar ya tayar ya fice daga gidan zuciyarshi cikeda tunanika kala kala.
Habeeb bai samu nutsuwa ba sai daya k’ara kiran Aleeyu ya tambaye shi taci abinci da magungunan kuwa? Aleeyu ya tabbatar masa da taci kuma tasha maganin ta kwanta.
B’oyayyar ajiyar zuciya ya saki lokaci d’aya yana sauke numfashi tareda yamutsa lallausar sumar kanshi, kayan kallon ya kashe ya shige bedroom yayi wanka yasa jallabiyyah blue black ya fesa turaruka sannan ya tada sallah kamar yadda ya saba ko wani dare kafin ya kwanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button