EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

★______★

A daidai wannan lokacin da aka haska hoton Seeyamah a NTA ana cigiyar ta, Heedayah da Zainab ma suna zaune a falo da yaran Aunt Ramlah kasancewar suna duba books d’insu na school ne yasa basu maida hankali wajen canza tasha ba dan indai suna zaune a falon basuda tashar kallo sai Arewa 24 ko MBC Bollywood, Zainab ce ta fara ganin hoton Seeyamah daya mamaye fuskar talabijin d’in a mazaunin wadda ake cigiyar ta ta b’ata kwanaki biyu da suka wuce. A matuk’ar razane ta zaro ido tana k’ara bin fuskar Seeyamah da ido kafin ta girgiza kafad’ar Heedayah wadda kanta ke sunkuye tayi nisa cikin duba littafin hannunta, d’agowa tayi ta kalli Zainab tace
“Menene wai?”. Hannu Zainab tasa ta nuna mata TV tabi hannun Zainab d’in da kallo, Ido ta k’walalo kamar zasu fad’o k’asa tsabar yadda ta fito dasu.

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

Jama’a kuyiwa Habeeb uzuri baku tunanin ta sanadiyyar d’auke Seeyamah dayayi komai zai bayyana? duk inda na lek’a anata yadawa Habeeb Gashua magana ???? easy guys mubi komai a sannu har zuwa lokacin da zamu gano bakin zaren, Gashua a cigaba da kidmashin Mom sayyeed da Aunt jamila na bayanka ????????????????.
Godiya mai tarin yawa a gareku reader’s alkhairin ALLAH yakai muku a duk inda kuke jazakumullah khair ????????????.

No 19.

  Batasan lokacin data saki littafin hannunta ba cikeda tsantsar mamaki da al'ajabi basuda bambanci a komai na halitta hatta dimple d'in da Seeyamah take dashi itama Heedayahn tana dashi a fuskarta wannan lamari akwai d'aure kai da rikitarwa ta sani cewa akwai mutane dayawa masu kama da junansu ako ina amma wannan dai kamar tasu ta b'aci ta yadda idan d'aya ya b'ata za'a iya kama d'ayan ace shine he's totally confused ta rikice da ganin wannan baiwar ALLAH da ake haskawa.

“Aunt Ramlah fito kiga wani abin mamaki please kafin a d’auke”. Zainab ta k’walawa Aunt Ramlah dake kitchen tana had’awa Abban Nu’aym fruit salad zata kai masa bedroom d’inshi saboda bayacin abu mai nauyi da dare, fitowa tayi tana mitar me zata nuna mata take k’wala mata wannan uban kiran ko knife d’in hannunta bata samu ajiyewa ba.
“Aunt Ramlah kalli TV kigani dan ALLAH wata kamar Heedayah wai ta b’ata ana cigiyar ta”. Zainab tace tana nunawa Aunt Ramlahn plasma d’in dake manne a jikin bango, itama d’in dai idon ta zaro na mamaki har wuk’ar hannunta na shirin fad’uwa wannan abu da ban al’ajabi yake.
“ALLAH buwayi gagara misali, kuga fa wani ikon ALLAH wllhy badan ina ganin Heedayah tsaye a gabana ba da ba abinda zai hana ince itace wannan ALLAH mai hikmah”. Aunt Ramlah tayi maganar tana rik’e bakinta.
“Wllhy ko nima Aunt tunda basuda maraba da Heedayahn kiga fa Aunt har wannan dimple d’in iri d’aya”. cewar Zainab tana kai hannu kumatun Heedayah inda nata dimple d’in yake, kallon Heedayah Aunt Ramlah tayi tace
“Heedayah ya kikayi shiru bakice komaiba?”.
Wani nannauyan numfashi Heedayah ta sauke tace
“To ai nikam narasa tacewa Aunt Ramlah ki dubafa babu wani bambanci da za’a iya gane tsakanina da ita komai iri d’aya”.
“Ikon ALLAHn kenan ai Heedayah mai yin yadda yaso kuma a lokacin dayaso ku cigaba da karatun ku nima bari inje in k’arasa aikina”. Aunt Ramlah tace tana komawa kitchen d’in can k’asan ranta kuma tana hasaso abubuwa da dama, sukuma nan suka zauna suna k’ara maida maganar hat yanzu basu bar mamaki ba.
Bayan Aunt Ramlah ta gama had’a fruit salad d’in ta zubashi a wani madaidaicin bowl mai kyau ta d’ora kan tray da spoon ta nufi bedroom d’in maigidan nata har lokacin da tunanin datake a ranta.
A zaune ta sameshi kan sofa sanye da jallabiyyah ruwan k’asa shima kuma news d’in yake kallo, bakinta d’auke da sallama ta shiga ya d’ago kai yana amsa mata wajen shi ta k’arasa ta janyo wani k’aramin stool ta d’ora bowl d’in akai ta zauna kusa dashi daga gefen gado tana fad’in
“Abban Nu’aym kaima labaran kake gani kenan kaga wani abin mamaki da aka hasko yanzu?”.
Kai ya gyad’a yace
“Bakiga yanayi na ba, gaba d’aya mamaki yagama kasheni ALLAH mai yadda yaso yarinya saikace Heedayah”.
“Wllhy kuwa Abban Nu’aym abin akwai d’aure kai a ciki zuwa yanzu nafara tunanin anya Heedayah ba twins bane ba kuwa?”.
“Tabbas kuwa nima nayi wannan tunanin gaskiya ALLAH ne ya barwa kansa sani amma kar wannan yasa kuyi wata magana har tasan halin da ake ciki ki k’yaleta kawai”.
“Insha ALLAH! na sake ma nayi mata magana makamanciyar wannan ai na shiga uku wajen Umma da Baba daidai da rana d’aya basa son abinda zai tada maganar nan har Heedayah ta fahimci wani abu”.
Kai kawai Muhammad yake gyad’awa yana k’ara ganin girma da k’imar surukan nashi ko shi badan wani irin sirri da ubangiji ke kimsawa tsakanin miji da mata ba da har Ramlahn ta fad’a masa da bazai tab’a sanin Heedayah ba k’anwar Ramlahn bace da suka fito ciki da itaba tsabar yadda basa bambanta su da y’ay’an da suka haifa saima fifitata da sukeyi akan yaran nasu da suka haifa da cikinsu, bowl d’in ta d’auka ta mik’a masa ya fara shan fruit salad d’in.

★★★_______★★★

A ranar kuma a daidai wannan lokacin bayan kammala labaran da aka gabatar na hangi wasu miji da mata daka gansu zakaga jikinsu a sanyaye yake har lokacin mamaki da d’imbin al’ajabin abinda suka gani yanzu bai sakesu ba wanda hakan ya nuna har akan fuskokin su.
Mutumin wanda ak’alla yabawa shekaru hamsin baya ya kalli matar tashi wadda a k’iyasin shekarun ta zasuyi arba’in da biyar.
Wani nannauyan numfashi ya sauke kafin yace
“Lallai Hajiya inaji a jikina wani babban al’amari yana doso mu wanda bamu san ko meye ba”.
“Cikin raunin murya tace
“Ni kaina Alhaji inaji a jikina kamar wani abu daya shafi JAWAHEER zai bayyana yanzu dan ALLAH wazai dubi yarinyar da akayi cigiyar ta yanzu yace ba Jawaheer d’inmu bace ba alamu sun nuna ita d’in twins ce irin identical d’in nan inaji a jikina wannan yarinyar da aka haska jinin Jawaheer ce ina tsoron ranar da zamu rabu da Jawaheer Alhaji”. ta k’arasa maganar tana sakin kuka wanda ya dad’e yana cinta tana matuk’ar son Jawaheer kamar ranta kamar yadda shima maigidan nata yake mutuwar k’aunarta, hannu yasa ya rungumota ta gefenshi cikin taushin murya da rarrashi yace
Bazamu tab’a rabuwa da y’armu ba Saudah bana fatan in riski ranar saidai a matsayin mu na iyayena kuma masu k’aunar ta dole abin farin cikine a garemu ace ta had’u da asalin iyayenta na gaskiya karki damu kanki muna tare da Jawaheer har k’arshen rayuwar mu insha ALLAH”. Ya k’arasa maganar yana goge mata hawayen idanunta yana cigaba da fad’a mata tausasan kalamai na kwantar da hankali ta lafe sosai a jikinshi tana tuno abubuwan da suka faru shekaru sha takwas da suka wuce a lokacin da suka tsinci jaririyar sabuwar haihuwa.
Nan gaba zamuji su waye wad’annan bayin ALLAHn Alhaji Mansur Jik’amshi da Hajiya Saudah.

Had’add’en bedroom ne mai d’auke da madaidaicin gado da k’atuwar wardrobe sai tamfatsetsen mirror wanda aka cika samanshi taf da kayan makeup da turaruka,gaba d’aya kayan d’akin kalar light blue ne da white har curtains da sauran abubuwa da ake k’awata d’aki dasu, an kashe fitilun d’akin sai bedside lamp dake kunne wadda ta bada kalar dark blue.
Kyakkyawar matashiyar budurwa na hanga kwance akan gadon dayasha tattausan bedsheet tayi shirin barci cikin riga da wando masu kauri kalar peach mai haske ta rufe k’afafunta zuwa kan cikinta da blanket mai laushi ba komai a kanta hakan ya bani damar ganin k’ananun kalbar dake kanta wadda ta sauka har kan kafad’unta, rik’e take da had’add’iyar wayarta tana ta faman danne danne tana dariya da alamu tana matuk’ar jin dad’in yanayin datake ciki chatting take da k’awayenta na school cikin nishad’i kiran Fauziyyah ne ya shigo wayar tata a lokacin k’awar tace sosai tare suke school, picking tayi takai kunnenta tareda fad’in
“Hello Babe ya daren?”.
“Banza kina ina muna nan yanzu muka gama ganin abin mamaki a NTA news kinsan Yah Abdul da shegen son labarai TVn d’akin shi kuma tasamu matsala shine fa yazo falo ya kunna a TVn falo”.
“Wani abun kuka gani a news d’in?”. cewar Jawaheer tana k’ara jan blanket d’in sama.
“Hmm bari kawai bestie wallahi wata aka hasko ana cigiya kinsan ALLAH badan d’azun nan muka rabu dake ba dasai ince kece kika to dan dai ita wannan ance kwana biyu da b’atan nata kamar kefa Jawa wllhy ina rantse miki bakuda maraba da ita su kansu y’an gidanmu sunyi mamaki wai anya bake bace kuwa nace musu bake bace gaki a online ma lokacin muna magana”.
Baki Jawaheer ta d’an tab’e cikin yatsina tace
“ALLAH ya bayyana ta amma nasan kawai shegen kwakwazo ne irin naki amma ya za’ayi ace komai namu iri d’aya haba saikace a film ke nifa irina ni kad’ai ce a duniya”.
“Ba zaki gane bane k’awata amma ke kanki da kin gani saikin razana wllhy nidai ban tab’a ganin abin mamaki irin wannan ba amma ba’a mamaki da ikon ALLAH”.
K’aramin tsaki Jawaheer taja tace
“Naji to go and sleep Hajiyata barci nakeji”. bata jira cewar Fauziyyah ba ta katse kiran ta santa da nanata magana yanzu idan ta barta zancen dazata isheta dashi kenan shiyasa tayi maganinta duk da har yanzu bata gama yadda da maganar Fauziyyah ba kawai dai taga wadda suke yanayi da ita shine zata dameta da maganar komai nasu iri d’aya ta yaya hakan zata kasance???.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button