EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Afwan idan nasamu dama gobe zakuga update idan akaji shiru kuma sai zuwa jibi insha ALLAH idan muna da rai da lafiya, ku cigaba da bina wasan yanzu aka fara ????????karku manta da comments and share.

Masu buk’atar a tallata musu hajarsu zasu iya nemana ta wannan number
09139964697.

Jummah Kareem ????

Maryam Ibraheem
Mrs Salees Mu’az ????

Sister’s duk wacce batayi anfani da sabulun mg’s ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg’s sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg’s domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg’s bi’iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg’s batare da kunbukaci wani Mai b????nd wnn new soap din????ne,???? bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic????for the soap reviews????
Soap price:3k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08062991549

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai 11k

Munaturawa Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team????karkubari abaku lbr????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

No 20.

Aunt Ramlah tana komawa bedroom d’inta ta iske tarin miss call na jama’a y’an uwa da k’awayenta wad’anda suka san Heedayah ciki har dana Hajiya Inna tana cikin dubawa wani kiran Hajiyan ya k’ara shigowa, ta d’aga kiran tana kaiwa kunnenta a rud’e Hajiya ke tambayar ta ina Heedayah idan ta fahimta dai itama Hajiyan taga abinda ya faru a labarai kai wannan abu da mugun d’aure kai yake.
“Hajiya yanzu suka tashi daga falo suka koma bedroom itada Zainab”.
Ajiyar zuciya Hajiya Inna ta saki kafin tace
“Alhmdulillah! sai yanzu hankalina ya kwanta wllhy tun d’azu ina cikin alhini da tarin mamaki naga an haska wata yarinya a talabijin wai an saceta basuda maraba da Heedayah komai iri d’aya shine na kiraki inji kan labarin”.
Zama Aunt Ramlah ta gyara tasan dai ko giyar wake tasha bata isa ta bayyana sirrin dayayi shekara da shekaru a rufe ba ta ina zata fara fad’in Heedayahn ‘YAR TSUNTUWA ce? sirrin da iyayenta ma basu tonashi ba wace ita da zata bankad’a shi? murmush ta d’anyi tace
“Wllhy muma mun gani Hajiya munyi mamaki sosai amma Heedayah lafiyar ta k’alau yanzu suka gama karatu a falo suka tashi”.
“Ikon ALLAH, to masha ALLAH ubangiji ya k’ara kiyayewa itakuma waccan ALLAH ya bayyana ta cikin k’oshin lafiya”.
“Amin Amin”. Aunt Ramlah ta amsa mata, har sukayi sallama Hajiya bata daina jinjina maganar ba ita kanta Aunt Ramlahn har lokacin mamaki bai gama sakinta ba, suna gama waya da Hajiya kiran Maman Ilham wannan k’awar tata wadda ta tab’a aiken Heedayah da Zainab gurinta wadda anan suka had’u da Habeeb ta kirata, itama d’in dai tambayar ta Heedayah tayi amsar dai data bawa Hajiya itama ita ta bata itama tana ta mamaki.
A wannan dare Alhaji Mansur Jik’amshi, Hajiya Saudah da Aunt Ramlah sun sha amsa wayoyin jama’a da dama kowa da irin tambayar dayake rattabo musu har wani lokacin ma su rasa amsar bayarwa.
Jawaheer kam cikin kwanciyar hankali tasha barcinta sam ta manta ma da wata maganar Fauziyyah datayi mata a ganinta idan banda k’arya taya za’a ce anga wata da basuda bambanci da ita ko twins ai kafin kaga masu kama d’aya aikine saidai kowa da kamarshi sai ita za’a wani ce anga irinta shirme kenan.
Ta b’angaren Heedayah ma duk juyin da zatayi cikin barcinta sai fuskar data gani d’azu a TV ta fad’o mata sam batayi wani cikakken barci ba sai wajen asubah shima kuma baiyi wani nisa ba aka kira sallah dolenta ta tashi barci cikeda idanunta sukayi alwalah sukayi sallah kuma ba damar komawa tunda su suke aikin gidan gaba d’aya kafin su tafi school musamman yau da suke da lecture by 7@m.
A gurguje sukayi breakfast sannan suka tafi da Uncle Muhammad zai saukesu a school d’in dayake yau ya fito da wuri da alama akwai inda zaije.
Ta cikin mirror Uncle Muhammad yake k’ara k’arewa Heedayah kallo har sai data tsargu, so yake yaga meye bambancin su da yarinyar jiya amma ya kasa ganowa dole ya maida hankalinshi kan driving d’in dayake tunda shidai bazai iya fad’ar abu d’aya wanda Heedayah take dashi waccan yarinyar bata dashi ba, zuwa yanzu ya k’ara tabbatarwa lallai Heedayah twins ne wani abu ya rabasu to meye abinda ya rabasu d’in? itace tambayar da kowa bai saniba.
Gaba d’aya Heedayah saidata tsargu tayi dana sanin zuwan nata school d’inma saboda yadda ake faman kallonta tamkar wadda tayi wani abin kunya duk tasan hakan kuma yanada alak’a da abinda kowa yagani jiya idan baka gani a TV ba zaka gani a waya, farko ma cewa tayi gida zata tafi Zainab ta hanata kuma ba wanda ya tunkareta yayi mata magana saidai nunata da ake tayi da hannu duk inda suka wuce ana binta da kallo maza da mata gaba d’aya abin ya isheta tamkar ta tsala ihu duk saita dabarbance tafiyar ma taso gagararta hannunta Zainab ta kama suka shige Hall d’in da zasu gabatar da lecture su ta ranar anan d’inma dai bata tsira ba dan wasu ma kasa hak’uri sukayi saida sukayi mata magana ta rasa amsar da zata basu, harda masu cewa wai yaushe aka ganta? surutai dai iri iri anata maida magana har zuwa lokacin da Dr Naseer Sufi ya shigo Hall d’in hakan yasa akayi shiru kowa ya nemi wajen zama ya shiga gabatar da abinda ya kawoshi.
Sai 8:30a@ sannan aka gama, Dr Naseer Sufi yana shirin fita daga Hall d’in class rep d’insu ya d’aga hannu da fad’in
“Sir”. tsayawa yayi ya juyo yana kallon mai maganar, tashi class rep d’in yayi ya isa inda yake k’asa k’asa ya d’anyi masa magana kafin ya nuno desk d’in da Heedayah take zaune itada Zainab gabanta fad’uwa kawai yake ta sunkuyar da kanta k’asa amma Dr Naseer Sufi yace ta d’ago kanta dole haka ta d’ago tana kallonshi, ido ya k’ura mata sosai yana kad’a kai kafin kuma ya fice daga Hall d’in gaba d’aya wasu daga cikin student’s suka rufa masa baya.
Tuni idanunta suka ciko da k’walla ta kalli Zainab tana fad’in
“Na shiga uku Zainab dana sani banzo school d’in nan ba yau kiga fa yadda ake faman nuna ni ana magana ta ga Dr Sufi ya ganni yanzu ya fita yana girgiza kai me hakan ke nufi?”.
“Please calm down mana Heedayah meye abin d’aga hankali a ciki wai? tambaya cefa kawai da amsa kece wance? a’a bani bace finish kuma mutane ma da suke ta wannan shirmen inace an rubuta sunan yarinyar da ake nema Seeyamah ce ko Sawwamah na manta duk wannan shegen Nura Ahmad (class rep) d’inne yaja ai”.
Heedayah ta bud’e baki zatayi magana kenan akazo aka kirata wai ana nemanta a office d’in VC, ido ta zaro tana kallon Zainab, Zainab bata bari tayi magana ba ta tashi ta kama hannunta suka fita daga Hall d’in.
Sai data rakata har wajen office d’in VC sannan ta tsaya tace ta shiga ita kad’ai.
Da sallama ta shiga office d’in, tunda ta shigo yake kallonta yanaso yaga bambancin su da yarinyar jiya daya gani a labarai amma shidai baiga wani abu d’aya dazaice ya bambanta su ba. Guri ya nuna mata ta zauna ta sunkuyar da kanta k’asa cikin fad’uwar gaba, sai daya kalleta sosai kafin yace
“Whats ur name?”.
Cikin d’ar-d’ar ta amsa da
“I’m Heedayah Abubakar”.
“What’s ur address?”.
“Rijiyar zaki”.
Tambayoyi ya shiga yimata kala kala a tak’aice dai a wannan rana saida Uncle Muhammad yazo school d’in ya tabbatar musu da ba yarinyar da ake cigiya bace wannan asalinta ma ba y’ar Kano bace daga Katsina take, dan da farko ma har police sukaso su saka a cikin maganar wai za’a maida ita gidan marayun da k’yar suka yarda da Uncle Muhammad daya dinga rantsuwa, Heedayah kam har kuka saida tayi musamman dataji sun sako maganar y’an sanda da kuma cewar za’a maida ita gidan marayu. Tare ma suka tafi da Uncle Muhammad d’in batare da sun gama lecture d’insu ba duk ta tsorace har abin yakoma bawa Zainab dariya.
Ta b’angaren Jawaheer ma hakan ce ta kasance a inda take karatu dan dai kawai ita ba mutunci dataga mutum yana mata kallon k’urilla zata tsaya ta zabga masa rashin mutunci ta k’ara gaba dan haka aka dinga shakkar kallon nata ma dan ba wanda baisan JAWAHEER MANSOOR JIK’AMSHI ba a school d’in.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button